← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 89

Sashe 47

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai wuraren karshen dare sanan ya kyaleta ganin kaman zata mutum mai ya kankame yana pecking ko ina a fuskarta, ajiyar zuciya kawai takeyi ahaka ya dinga bubbuga bayanta har wani irin bacci yay gaba dasu.
Biyar da rabi ya farka fuskar ta ya kalla yanda duk hawaye suka wani bushe, lumshe ido yayi yabude su akanta ahankali ya sakin mata light peck a goshi kafin ya kwantar da ita a gefenshi ahankali, yatashi ya shiga bayi ruwan zafi yahada yazo ya dauketa cikin bacci, sakata yay cikin ruwan hakan yasa tabude ido kadan kafin ta saki wani irin wahalallen kuka kwanto da kanta kan kafadar shi yayi yana dan bubbuga bayanta, saida yagama sanan yabude inda ruwan zai tafi yatafi kafin yasake hada wani ruwan yasaka sabulun kumfa yana dauke da ita, sanan ya shiga da ruwan dauke da ita ya zauna ya daurata akan jikinshi yana goggoga mata kumfan awuyan yana kallon yanda ta runtse ido hawaye na bulbulo wa ta gefe, dan murmushin gefen baki yayi ahankali yasake janyota jikinshi sosai yadaura fuskarta akan wuyanshi tareda daura kanshi akan gefen fuskar nata dake wuyarshi murya chan kasa yace "are you angry?" dan shiru yayi jin yanda hawayen datakeyi yake gangarawa ta wuyanshi yana sauka aruwan kumfan daya tsaya a kafadar su, sake lumshe ido yayi ya cusa dayan hanunshi cikin tulin gashinta daya mugun hargitse murya chan ciki yace "buh is not my fault" shiru yay kafin yay murmushi gefen baki yakara saita bakinshi saitin kunenta yace "open ur eyes ki kalli abinda ya wahalar dake haka, is not me" sake kankame idonta tayi wasu sababin hawayen kaman famfo suna zubowa, lakatan hancin ta yayi da murya chan kasa makoshi yace "lazy gurl" dan murmushi yayi kafin ya mika hannu yadauko soft sponge din dayake wanka dashi yasaka a ruwan sanan yaciro batare daya rabata da jikinshi ba yadaura abayanta yafara wanketa ya wanke bayan tass, sanan ya juyo da ita yay relaxing bayanta ajikinshi yafara wanke ta tundaga cikinta dayazo wajen kirjinta sai kuma ajiye sponge din yadan kalli fuskarta ganin har lokacin idanunta a kulle suke hawaye sai fita suke ta gefe yasa yahau wasa da kayanshi, saida yaga gari yasoma haske yasa yay maza yay nashi wankan yasa tai wankan tsaki shima yayi sanan ya nannado ta a bathrobe dinshi shikuma ya dauro towel ya dauketa kaman jaririya yafito da ita daga bayin, shi da kanshi yaje dakinta ya dauko wata yar figigiyar riga white kaman shimi da dogon hijabi sanan yadawo yasame ta tana zaune inda ya ijiyeta abakin gado har lokacin kuka take, daure fuska yay tamau yace "ke stop dat silly cry" shiru tayi tana goge kwallan ya zauna kusa da ita dagata yayi yana kallon fuskarta ya daurata akan jikinshi yacire mata bathrobe din ya saka mata rigar daya dauko sanan yasaka mata hijabin ya koma gaban wardrobe yasaka doguwar jallabiya ya shimfida musu dadduma yazo hanunta ya kama ya mikar da ita tsaye yajata kafa ta daga tai tafiya da kyar tai maza maza ta goge hawayen azaban dasuka zubo, daukarta yayi yadaura ta kan dadduma shiya jasu sallan asuba bakaramin mamaki tayiba ganin yay salla daidai itadai a iya sanin ta ko mistake daya bataga yayiba ashe yadan san wani abu a addini shine yake iskanci. Hijabin ya cire mata ya dauketa ya kwantar da ita akan kujera, zanin gadon da bargon yakoma yacire ya je yasaka su a washing machine sanan yadawo ya shimfida wani sabon zanin gadon da kyar yana nishi dudda bawani yi da kyau yayi ba dawowa yay wurin kujeran yaga har wani wahalallen bacci yay gaba da ita, ahankali ya dauketa ya kwantar da ita akan gadon yana tunanin yanda zaiyi ya kaita gidansu ahaka yau, kwanciya yay gefenta ya rungumeta ahaka shima wani baccin yay gaba dashi.
Wuraren daya na rana ringing din wayarshi ya farkar dasu da kyar yadau wayar yaduba yaga Mami ce, ahankali yay picking anatse yace "Mami na" batare data amsa shiba tace "bakaga daman kawomin itan bane kana sane jirgin karfe shidan yamma Baffan ka zaibi ko" ahankali yace "zamuzo dan anjima kadan Mami damafa kafarta ke ciw..." da sauri Mami ta katse wayar.

*Wolla Ayaan baida kunya, anyways something is about to happen*.
[7/25, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

59 - 60

Ajiye wayar yayi ya juyo da kanshi yana kallonta idonta biyu saidai ta lumshe ido sabida yanda ya rungumeta yasa takasa tashi, dan matso da kanshi daidai saitin fuskarta yayi ya huramata iska a fuska hakan yasa takara kankame idanunta, hada forehead dinshi yay da nata yana goga hancinshi akan nata dudda haka taki bude idon, murya chan ciki yace "hey open ur eyes" kin bude idon tayi sai numfashin da take da sauri da sauri, kara daura hancinshi da kyau yay kan nata yana shakan numfashin ta itama nashi na shiga nata, batare daya raba fuskar nasu ba ya mikar da hannunshi yana lalubo nata, akan cinyarta yaji hannun nata hakan yasa ya rike ya bude tafin hanun yana murza tsakiyan dake jike da zufa yana kallon fuskar ta ganin taki bude ido yasa murya chan kasa yace "alright u asked for it" chakulkuli yamata da sauri ta bude ido tana neman yin dariya amma ta daure ta hana kanta dariyar, fuskarta yabi da kallo kafin yatashi daga gadon ya sunkuceta sukai bayi, nanma suka kara bata lokaci dan saida ya gasata sanan sukai wanka bayan yay wasa da ita son ranshi, kafin su fito ya zaunar da ita abakin gado yana goge jikinshi da towel sanan ya zauna agefenta yana kallon fuskar ta yanda idonta ke kasa sanan ya kalli gashinta daya hargitse ahankali yace "jeki shirya mufita Mami na jiranmu" yay maganan calmly, tashi tayi daga kan gadon ahankali tana tafiya kadan kadan sabida zafi tafita daga dakin dan lumshe ido yayi kafin ya mike yay wajen wardrobe.

Tana shiga daki tafara share hawaye da kyar tai salla sanan tai parking hargitsassen gashinta da ribbon, wani hadadden lace ta dauko royal blue tasaka an mata dinkin riga da skirt daya mata chas chass ajiki ta zauna akan stool ahankali, tajawo hoda ta shafa ta rangada kwali a idonta da har yanzu basu gama washewa ba tsabagen kuka, ta shafa lip gloss a lips dinta dasuka sa lips dinta yay wani irin kyau pink din yafito sosai bakin ma haka abin saiyay kaman tasaka janvaki, tai carving giranta da brush sanan ta tadau dan babban mayafinta black mai shegen kyau tasaka takalmi medan tsini kadan black shima sanan tadau jakarta data saka wayarta kadai aciki ta zauna abakin gado, ko minti daya batayi da zama ba shima ya shigo sanye da royal blue shadda gizna sai kyalli take yamata dinkin half jumber yasanya black cover shoes mai masifar kyau hakanan yau yaji yanajin saka manyan kaya bakaramin kyau yayiba ya tsaya abakin kofa turus yana kallonta hanunshi rike da tea dayan hanun kuma tablet yarike, dan murmushi yayi ganin yanda taketa wasa da bakin gyalen ta, ya shigo dakin yazo kusa da ita ya zauna har jikinsu na gogan juna yana kallon fuskarta yabata tea ahankali yace "sha mutafi" karba tayi hanunta na rawa takai baki tasha kadan tacire abaki, saida tasha kusan rabi sanan ya saka mata maganin abaki ta hadiye sanan ta shanye sauran tea ya karbi cup din kafin ya mikar da ita tsaye yana kallonta, hanunta yarike sanan yajata yanabinta ahankali suka fita daga dakin da sukazo wajen stairs da kanshi ya dauketa sukai kasa bayan ya ijiye cup din a kitchen yafito da ita ya kulle gidan har compound, saida ya bude bangaren ta yasaka ta ciki sanan ya rufo ya zagaya ta dayan side dinshi ya shiga motar ya kunna suka fita daga gidan, wakar celine dion na if walls could talk ke tashi a motar sai binta yake kaman shiya raira wakar kana ganinshi kasan yana cikin nishadi haka sukakai har gaban babban gidansu horn yayi yana rage karan music din sabida kiranshi da akai a waya, daukar Wayan yayi da hannu daya ya kara a kunne yana tuki da hannu daya ya shiga cikin gidan nasu bayan anbude gate.
Chapter 47 · 0% Book details