Sashe 3
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Dr ne akan wani magidancin da akalla zaikai 75 years sa'an Baba buhari😂 acikin wani katafaran falo sai sumbatu yake yana "Dr Ayaan dina zaka kawomin, Ayaan" shiru yayi sabida alluran da likitan yamai daidai lokacin wani security dake sanye cikin uniform ya tsaya agaban falon yana sallama, izini matar dake falon cikin shiga ta alfarma tamai, hakan yasa ya shigo hanunshi rike da wata ipad, Karasowa yayi gefen Baba Sule wanda shine kanin magidancin dabaida lpy, cike da girmamawa yace "Alhaji wanan shine CCTV footage din natun ranan da Ayaan yafara rashin lpy abangaren shi, da lokacin daya fita daga gidan" ya kalli matar datai tagumi tana kallon fuskar mara lpy yace "Hajiya akwai bukatar kema kizo ki kalla dan wata da kayan yan aikin gidan nan ne tafara kawomai abinci lokacin yana garden tace kece kika aikota takawo mai, to ayanda dai CCTV footage din yanuna yanacin abincin yafara rashin lafiya saikuma..." yadanyi shiru cikeda damuwa yace "zodai ki kalla dakanki wata kila ki gane yarinyar dan munemo ta dole zatasan wani abu kan batar shi" tashi matar da aka kira da Hajiya tayi ta dawo gefen Baba sulen ta zauna jiki asanyaye tana kallo, tunda tafara kallo ta dafe zuciyar ta tana buga salati saikuma tafashe da kuka sosai ta kalli Baba Sule tace "Baba Sule ina dana yayi? Yanzu adai yanda yafitar nan a ina zamu ganshi, innalillahi wa innalillahi raji'un wanan wace irin musib.." shiru tayi ganin mara lafiyan yakara farkawa yarike hanun Dr dake kanshi yace "ina Ayaan dina? Eh Ina ka kaimin shi?".
[7/15, 12:17 PM] Ummi Tandama: ♦♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦♦
Maman Abd Shakur
5...
Free page
Iska da kiraye kirayen sallan magrib ne yashiga kunnenta yana ratsa har brain dinta, ahankali take bude ido ganin inda take yasa ta mike tsaye a firgice tana karanto ayatul kursiyu ko ina na jikinta na rawa, karan buga abu dataji shiya kara firgita ta hakan yasa mahaukacin kara juyowa ya kalleta, baya tafara komawa jikinshi ko ina rawa yake, juyar dakai mahaukacin yayi yacigaba da bubbuga kular nata abango yana dariya kafin yakamo bakin rigar shi ya cusa abaki yana ci, hannu tasa tarufe bakinta tacigaba da komawa baya sadaf sadaf, haushin kare taji abayan ta yasa ta buga wani irin mugun ihu ta shiga cikin gidan da gudun bala'i dan ta tsani kare, karan yazo ya tsaya ta bakin kofan yanata haushi, zuciyar ta kiris ne yarage bai fitoba, mahaukacin ya dena buga kular dayake yajuyo dakai yana kallonta, yanda ta makale jikin bango tana kuka kaman zata suma, rigar shi yakara turawa abaki yana kallonta yana wani irin lankwasar dakai yana taune rigar hakan yasa ta tsugunna awurin tareda runtse ido da karfi tana cigaba da karanta ayatul kursiyu, wani irin mugun kuka da haushi karen yasake yi "wu wu!" hakan yasa mahaukacin ya juyo daga dena buga kulan abango ya kalli karen, zare rigar yayi daga bakinshi ya fashe da dariya sanan ya tsugunna shima yace "wu wu" da karfi sosai, haka yadinga wu wu yana matasawa kusa da karen yana tsalle har karen yabar wajen, shirun dataji yasa ta dago kanta ta kalli hanyar fita taga ba karen littafin ta dake watse akasa taga mahaukacin ya dauka yanata yayyagawa yana kara da wasu gwalangwalan yanaci, jikinta har rawa yake tana kallonshi ganin hankalin shi nakan litttafin yasa ta ruga aguje tafita daga wajen, haka ta dinga gudu harsai da takai bakin titi, machine ta tsayar tahau sai goge hawayen dasuka ki tsayamata take tayi, saida suka kai anguwar su daidai kusa da gidansu ta sauka malam tagani tsaye yanata kallonta da alamu dama ita yake jira, kallon mai machine din tayi tace "bari na amsoma kudin" ahankali ta karasa wurin Baba tana share hawaye anatse yace "meya faru? Ya akayi kikai datti haka daga ina kike?" fashewa tai da kuka tace "faduwa nayi Baba akan karfe kaina zafi yake yi ma" hannu yatura a aljihu yace "sannu kidinga yi ahankali nawa zaki bashi?" "naira dari" tafada batare data daina kukan ba, mika mata yayi taje tabashi sanan tadawo ta shige gida hada Ido sukayi da Isyaka dake biyama wasu almajirai karatu ya mata alamu da hannu na sannu ta gyada mai kai asabari ta daga tareda bude kofa ta shiga cikin gida. Babu kowa a tsakar gidan hakan yasa tawuce dakinsu su Raiyana tagani tareda Mama suna bata haddan dazasu bama Baba gobe da asuba yaji, zama tayi akan kujera tana share hawaye Mama ta kafeta da ido tace "daga ina kike Bilkisu? Kin kaima Balaraba kudin nata?" wani irin racing heart dinta ya shiga yi hakan yasa takara fashewa da wani sabon kukan tace "Mama wlh faduwa nayi namaji ciwo akai?" kallo Mama tabita dashi gashi tayi wani irin mugun datti hakan yasa tace "a ina kika fadi? Ina jakan ki? Ina kudin dana aikeki dashi?" tashi tayi a tsorace tai hanyar kofa hakan yasa Mama ta bita da kallo, a tsorace cikin kuka tace "kudin nacikin jakata nabarta a inda nafadi amma gobe da safe zancema Muji yakaini na dauko saimukai mata" hawaye takara sharewa tana kallonta tace "kiyakuri dan Allah Mama" da sauri ta juya tafita daga dakin danba karamin aikin Mama ba ta maketa dan akwaita da saurin hannu, dakin Umma ta shiga aiko duk hankalin Umma yatashi anan ta kwana.