← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 75 OF 89

Sashe 75

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Babban gidane da ba'a gama ginewa ba, dan Mami bataga hanya ba sabida wani bakin yadi da big Mum tarufe mata fuska dashi, zaune take akan kujera tun isowan su ahaka take an daure mata hannayenta tabayan kujera da kafa, an taushe mata baki sanan anrufe fuskarta da bakin kyalle, muryan big mum kawai takeji dawasu maza, addu'a kawai take aranta Allah ya kareta daga shairin big Mum sanan ubangiji Allah ya karemata Ayaan da Bilkisu, alamun tafiya mutane dayawa taji ana shigowa inda take batasan meke faruwa ba tadai ji Big Mum na cewa ku kulle shi da kyau, saikuma wuf aka yaye bakin abin daya rufe fuskarta, haske ranane bau awajen ahankali tabi wurin da kallo gini ne babban gaske da ba'ai plasta ba kawai block ne saikuma katakwayen roofing sama da aka jera kaman ana shirin saka kwano ne saikuma ba'a sakaba, ahankali ta juyo da kanta ta kalli Big Mum dake zaune kan wata kushin ita da pilot din Abba tanamai murmushi, kwalalo ido Mami tayi tanason tai magana amma ba halin yi sabida taushe mata bakin da akayi, wani irin mugun kallo Big Mum ta watsa mata saikuma ta kalli Bala dake tsaye shida wasu samari guda biyu tace "budemai fuska ya ganni Bala naga ya farka yana motsi da kafa" da sauri Mami ta kalli gefenta kirjinta na bugawa wakuma aka kamo ko Ayaan ne, Alhaji! Tafada aranta tana wani irin salati da sallallami tana sanar da ubangiji halin dasuke ciki, kwalalo ido shima Abba yayi yanaso yay magana ganin yanda aka daddaure Mami amma ba hali kaman daga sama yaji muryan big Mum tace "Alhaji" da sauri ya juyo dakai ido da ido sukayi da big Mum da pilot dinshi suna wani irin kallon juna, murmushi Big Mum tayi tawani lashe baki tace "dan ka yazaci yanada wayau yasa polisawa suncika airport yazaci anan zaku sauka ne? Hahaha, karkai mamaki fa, bawani abu yasa nai hakaba sai dukiya, dukiyar ka kawai nake bida, nariga nafada ma danka ya maida duka dukiyoyin ka sunana sanan ya saki yarana da aka kama na uku kuma yabani Bilkisu na kashe dan itace taja asirina ya tonu haka bazan taba yafe mata ba, ayanzu dai nabashi awa ishirin da hudu ko my man" tai maganan tana shafa gemun pilot dake sanye da uniform yana kallonta, girgixa mata kai yayi tareda fuzar da iska yace "hajjaju ta aganina awa ashirin da hudu sunyi yawa fa, ko Ina neman mu ake Kuma kinsan atsakiyan filin daji nai parking koda yaushe wani abu kan iya faruwa, ki rage lokacin, shidan yamma nayi ki kirashi yabamu abinda mukeso muje mu shiga jirgi mubar garin nan. Gyada kai tayi ta mikama Bala hannu alamun ya bata wayanta, kawo mata wayar yayi Abba duk yanabin su da kallo da idanunshi dasukai jajir kokarin magana yake amma ba hali, kunna wayan tayi bayan tasaka wani sabon layi ya sanya mata nashi, number Ayaan tai dailing daidai lokacin Ayaan da CP sun shiga dakin da ake tracking number, wayar yaciro yana kallon number da sauri yay picking yasaka a speaker yanama me tracking din alamu da ido, dan hakanan yaji aranshi big Mum ce, picking yayi yasa a hands free wani irin dariya tayi tace "bazaku taba iya kamani ba duk sim din dazan kiraka dashi dazaran nagama magana nake ballawa, nakira ne nafada maka nafasa baka awa ashirin da hudu karfe shidda daidai zan kira nafada maka inda zakaje ka ijiye Bilkisu" katse wayar tayi da sauri Ayaan yay wurin computer inda CP ke tsaye akan me tracking number yace "how far" girgixa mai kai CP yayi alamun ba'a samuba tsaki yayi hankali atashe, fita yayi yawuce masallaci alwala yayi ya shiga yabi jam'i yay azahar yana fitowa motar shi ya shiga ya zauna yaciro wayar shi number Bala dayariga yay saving yaciro yay dailing akashe, wani irin ihu yayi ya daki kujeran motar, kunna motar yayi ya wuce MTN office wani abokin shi ne babba awajen hakan yasa ya wuce upstairs direct knocking yayi ya shiga abokin shi mai suna Musa na ganin shi yay dariya yace "Dr ana ganin ka dama" dan murmushi kawai yayi ya zauna Musa yace "why is ur face like this" girgiza Mai kai yayi yace "I need a favor" wayar shi ya ciro yajawo wata yar memo dake gabanshi da byro ya rubuta Mai number Big Mum, da number Bala ahankali yace "please track this two numbers for me in hakan baiyuba inaso kabani any other number da masu layin suke amfani dashi sanan amin tracking dinsu" yanda yake magana yasa abokin nashi yatashi da sauri ya bude yar fridge din office dinshi ya dauko bottle water yadawo ta gabanshi ya bude yabashi, kasa karba Ayaan yayi saima kafe goran dayayi da ido yakasa karba dudda yanajin kishi, hanunshi mutumin ya kama ya saka goran ruwan aciki ahankali yace "Dan Allah kasha abokina" kafawa abaki Ayaan yayi yasha kadan sanan ya ijiye, ahankali mutumin yace "tashi muje adubama dudda dai kaki gayamin mecece matsalar" fita sukayi daga dakin, wani office suka kara shiga, Musa ya mikama wani dake aiki takardan yace "binciko mini wayan nan numbers din" karba yayi ya kwafe number yana danne danne a system din sai yace "sunan layi daya Saratu gwanaye dayan kuma Bala Mubarak, banda wanan layin Bala nada layi biyu kuma daya bude da sunan nan" da sauri Ayaan yaciro wayar shi yace "kiramin numbers din please" kira mishi akayi ya kwasa yajuyo yace "please ku gwada min tracking din numbers din konawa ne zan biya please, zan tafi yanzu once kunyi kutaramin address din tawaya na" yanda yake maganan ne yasa Musa yace "wats happening Ayaan?" dauke kai yayi sabida hawayen dayake ji ahankali yace "anyi kidnapping su Abba ne" da sauri yafita daga wurin bakaramin tausayin shi Musa yaji ba Ayaan mutum Mai kirki tun kafin yasami aikin nan lokacin da matarshi ke labour Ayaan yamata CS kyauta sabida baida kudi, da sauri ya kalli Yaron yace "don't rest saika samo location dinsu" yafita daga office din dukya damu.

Ahanya ya tsaya yay la'asar kafin ya wuce gidan su, gashi nan kawai kaman zararre, parking yayi a compound ya wuce shashin big Mum, hargitsa dakinta ya shiga yi yana neme neme ko zai sami any clue, daga bayama rigarshi yacire yay hanging akofa yazo ya daga katifar ta ya daga gado yana dube dube, yakoma wajen drawers din bedside yahau bubbudewa, wardrobe dinta yakoma yana ciccciro kayanta yana wurgawa kasa kaman zararre, kaman da kayan yake fada, finciko kayan ya dinga yi yana yarwa dan kara dayaji akasa yasa ya kalli kasan da sauri, wayansu kayane daya zubar hade dawani file babba, da sauri ya tsugunna ya dauko file din ya bude takardu ne daban daban, ahankali yakoma gefen gado ya zauna yana duba takardu falle falle yawancin su takardun gidajen Abba ne da papers din filaye wanda duk yasan da zamansu, idanunshi ne suka sauka akan wani takardan owernship din gida wanda sunan hajiya Saratu ne ajiki, da sauri ya cigaba da budewa yana going through d content, rufewa yayi yana dan tunani yaushe which house is this? Address din gidan ya duba hakan yasa ya saki file din anan kasa yaja rigarshi daga kofa yasaka yafice harda dan gudun shi, yana shiga mota kiran CP na shigowa wayarshi da sauri ya dauka yana driving, daga ta dayan bangaren CP yace "Ayaan kazo headquarter sabida dazaran takira ka mu samu muyi tracking dinta down, this is five thirty kai sauri all team dinmu damuka zuba babu wani vital information, munje gidan da yaran damuka kama sukafada mana suna zama suda Bala amma ba'anan suke ba, hurry up karta kiraka kana hanya".
Chapter 75 · 0% Book details