← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 89

Sashe 18

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Misalin karfe biyar na yamma suka fito daga cikin school dan anatashi su biyar ne na yamma, suka jero ita Aisha shehu, Walawa, Fa'iza dakuma Fatima, itace a tsakiyar su cikin dogon farin hijabin ta dayasha guga da wandonta purple kafarta sanye da farar safa tasaka brown takalmin makaranta mai igiya, babu komi a fuskar ta sai kwalli dakuma mai data shafa a lips dinta bayan sallan la'asar wanda yasa har yanzu pink lips dinta ke shining sosai da black din abin sai yay kaman tasa jan baki, murmushi dukan su sukeyi dan Fa'iza ke basu labarin yanda sukai da saurayinta jiya dayazo tadi sunata murmushi, bayan Fa'iza tagama duk sukai dariya, takara yin wani irin murmushi daya lobar da dimple dinta tana dan tunani tace "niko jiya da Isyaka yazo ko" sai kuma tai shiru tana fari da ido hakan yasa Walawa ta dafata tace "fada mana yar malam meya faru dayazo ke badai ya mammatse kiba" hararan ta tayi tace "Allah kyauta bama iskanci mu" murmushi duk sukayi suna kallonta, sai kuma tasake yin fari da ido tace "anbiya shi kudin aikin hannu shaddan dayayi aiko ya siyomin ice cream jiya, muka sha nida su Raiyana" ihu suka hau yi suna tafi. "woh ke woh ke, ashe dai ustaxai sun iya soyewa su isyaku an iya sawo ice-cream" dariya tai kafin ta dauke kai tace "an sa fa, nan da 2weeks da some days ne?" "mene!" dukan su suka tambayeta atare Aisha Shehu ce tace "amma kin cika yar iska Billyn Malam, keda kikace mana sai bayan kun gama exam?" kaman zatai kuka tace "wlh bahaka bake fa, Babane yace ranan walimar shi kawai ahada da auren" duk shiru sukayi suna tafiya ahankali saikace ba gida zasu ba sai kallon su take tana murmushi, chan Walawa tace "inko hakane bazamu yarda ba wlh dole mutaba mu mulmula su kafin Isyaka yataba" ihu sosai tayi da saida sauran daliban gabansu suka juyo ta arce da gudu sosai tana dariya saida ta musu nisa sosai dan har bata hangosu sosai sanan ta jingina dawani mota tana mayar da numfashi tana dariya tana kallon layin data kusa kurewa da gudu, kirjinta ta dafe tace "wayyo Allah na" jin yanda ya wani irin buga sanan tacigaba da nishi tareda lumshe ido tana kokarin saita numfashin ta, wani irin kamshin turaren kamshi daya daki hancin ta yasa ta bude ido ahankali ta saukesu akanshi ya tsaya agaban ta yay folding hannu akirji yana sanye cikin wani black bodyhug daya kama shi dan kana ganin layi layin six pack dinshi, da fadadden kirjinshi dake nan kaman ya rabe biyu, sanan hannun rigar yakama muscle 💪 dinshi jijiyoyin sun fito, kafara shi cikin wani original tomford sneakers, ya sanya wani dan iskan crazy jeans dayay tokin rigar aciki sanan yasaka belt mai bala'in kyau, kana iya hango sarka dake kyalli ta wuyarshi gawani sheken dan kunne na diamond wanda maza ke makalawa da gum, dan dan kunnen da gum dinshi yake zuwa, idanunshi sanye cikin dark shade da bata iya tantance mema yake kallo, yanda ya tsaya a gabanta sosai yasa tama kasa janye jikinta daga motar dan go tafiya daya kacal tayi zata iya gogan jikinshi ta lafe ajikin motar numfashin ta nafita da sauri da sauri, hannu yasa a aljihun bayan wandon shi yazaro bandir din kudi yan dubu daidai ya rike kudin kafin ya kalleta, kanta akasa tana wasa da bakin hijabin ta, wurgamata kudin yay a fuska wanda har saida ya bugi bakinta kafin ya fadi akasa tsakakanin kafanta, yabi kudin da kallo sanan ya tabe baki yace "Pops ne yadaman nabiyo ki school dinku namiki kyauta, so here u go" yajuya yay inda ya paka mota zai shiga, bin kudin tai da kallo ranta ya mugun baci da sauri ta share hawayen dataji ya zubomata ta tsugunna ta dauki kudin ta mike ta kalli motar daya shiga ganin baibar wurinba yasa tai wurin motar, kai tsaye tabude daidai lokacin ya dauko bottle water ya bude zaikai baki, ajiye mai kudin tai akan cinya ahankali tace "nagode amma ni bana bukatar wani abu daga wurin ka" tajuya zata tafi karaf taji yarike wutsiyar hanunta, da sauri ta juyo taga bama ita yake kallo ba saima kai bottle din dayay bakinshi yana shan ruwan shi a natse, duk iya karfinta takasa kwance hanun gashi duk yan makarantar su dazasu wuce nata kallonsu duddu su Walawa basu riga sun karaso ba, zafin dataji hannun nayi yasa hawaye ya gangaro mata a kunci, saida yagama shan ruwan sanan ya ijiye bottle din ya juyo da kanshi ya kalleta tareda cire bakin glass din idonshi ya ijiye a gefe ya kafeta da idanu da sauri ta janye nata ta cigaba da kokarin fizge hanunta, muryar ta har rawa yake tace "ka sakeni natafi gid..." "ke!" ya daka mata tsawan da batasan lokacin data fashe da kuka ba ta hadiye sauran maganan, wani irin mugun kallo yamata dayasa ta hadiye hawayen tarasa mesa take shakan shi haka, cikin wata irin kakkausar murya yace "kinsan wayeni kuwa?" dan murmushin gefen baki yayi dayawani irin karamai kyau kafin yasake damke fuska yace "Am Dr Ayaan, a doctor, double degree holder, masters holder and PhD holder, am a surgeon and a pathologist, mace bata kawomin wargi, babu abinda bansani ba na mace, so ki kula! Ki natsu! I don't take shit! dan haka pick dis money and get out of my sight" yafada cikin tsawa tareda jawo hanunta daya damke tun dazu ya daura kan kudin yamata wani irin kallo dayasa ta bude hannun da sauri ta dauke kudin sanan ya turata dahar saida tafadi kasa yaja motar dawani irin gudu yabar wajen yana tsaki, baisan mesa Popsy kemai wanan abinba wlh me zaiwani sa yazo nan, thank God yau zasu bar garin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: [7/13, 10:15 PM] ‪+234 802 916 3341‬: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

23 - 24

*For Sell! idan baka biyaba dont F*ck*ng read it in Ayaan voice. Aha*

Hawaye ta share tabi wutsiyar hanun nata da kallo yanda yay ja abunku da farar fata ahankali tace "kuma ban yafeba mugu kawai" ta tashi da gudu tana kuka tai bakin titi batare data waigi su Walawa dake kiranta ba, ta tare Bus ta shige tana share kwalla ahaka har gida. Tana zuwa gida kofar gidan su tai turus tana kallon baban trailer company Uniform, suna sauke katipu irin na boarding school dinan ankawo ma almajirai kowa daidai, aiko sai tsalle suke suna murna wajen ya kacame da hayaniyan su, karasawa tai wajen Baba dake tsaye yay shiru yana kallon masu sauke katifar tace "Baba waya aiko da wayan nan katipun?" "mutanen dasuka zo jiya ne suka aikoma dalibai dashi, wai suna Allah kadai zai iya biyan mu amma ga wanan abama dalibai" shiru tayi tama rasa yanda zatayi tabama Baba kudin daya bata dan kunya takeji fada zai mata mesa ta karba hakan yasa ta wuce cikin gida tana satan kallon Isyaka dake rubutu a allo yana binta da kallo shima, murguda mai baki tayi tana nunamai allon ta shiga gida tana dariya, da sauri yabi allon da kallo yaga ashe afarar rigarshi yay rubutun baima saniba garin kallon ta muurmushi yay ya shafa gemunshi daya cika kaman wani babba sosai yacigaba da rubutun dayake yi. Tana shiga ta debo ruwa daga rijiya ta shiga tai wanka tadawo daure da zani, tana bubbuga kunenta dan ruwa ya shiga gajiya tayi da goge kunen kafin ta zauna gefen mama hanunta Mama tabi da kallo yanda yay ja tace "maiya sameki a hannu?" girgiza kai tayi tace "bakomi bugewa nai a school" kofin magani Mama tabata ta karba tasha sanan a ijiye tana yatsine baki, jakarta tadauko taciro bandir din kudin ta ijiye kusa da Mama tace "Mama mutumin nan najiya nahadu dashi a makarantar mu yabani wanan" kudin Mama tabi da kallo tace "aisai ki kaima Baban ki tunda kinada hannun amsa ni meruwa na" kaman zatai kuka tace "Mama dan Allah kibashi nidai tsoro nakeji, fada zemin wlh" tai kaman zatai kuka ta mike ta shige uwar daka dan saka kaya.

*******
Yau kwanan su biyu kenan da dawowa daga kano.
Chapter 18 · 0% Book details