← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 89

Sashe 64

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Maman Abd Shakur

76 - 77

Kafin ma tai yunkurin yin wani abu yahada bakinshi da nata yana kokarin zame rigar gabaki daya daga jikinta, wani irin kuka take jikinta duka narawa hanunta tamika ta dauko filo ta bugamai akai tana ture kanshi da filon jikinta nawani irin rawa tana kuka, yamutsa ta yacigaba dayi batare daya saki bakinta ba, jin ana kiran sallan la'asar yasa yasaketa ahankali yatashi ya zauna abakin gado tareda dafe kanshi yana kokarin saita kanshi, filo ta dauka tana bugamai abaya da duka karfin ta tana kuka sosai tama kasa magana, da kyar ya dago kanshi dasukai jajir ya kalleta yanda take kuka na sosamai rai shima ba'a son ranshi bane yake mata wani abuba, filon dake hanunta takara bugamai akai tana ihu kaman mahaukaciya, ahankali yarike filon tareda saka dayan hanunshi yajawota tana tutturjewa saida yahada ta da jikinshi, ya ijiye filon, tana kokarin tashi yaki bata daman yin hakan ya matseta tareda daura kanshi ata wuyanta yana bubbuga bayanta alamun tai shiru dan bazai iya magana ba ayanda yakeji, tun tana mutsu mutsu har bacci yay gaba da ita. Ahankali yaciro ta daga jikinshi tareda manna mata kiss agoshi ya kwantar da ita ya rufeta da bargo sanan ya mike tsaye idanunshi sun kada sunyi jajir, bayi ya shiga yay wanka yafito ya shirya cikin riga da wando yadau car key da waya yafita daga gidan.

Baiwani dade da fitaba tafarka daga baccin tana kwalla, saikuma kukan ya kankama sosai sosai take kuka tana kiran sweetheart yazo ya dauketa batason gidan nan mutumin nan sai tabata yakeyi. Da kyar ta mike tsaye taje bayi, wanka tayo shima da sabida jikinta daduk yamata tsami ne, sanan tai alwala tafito daure da towel din data gani abayin, wani dan gown data gani white me hanun shimi a wardrobe din tadauko ta saka tana goge kwalla tana harare harare kafin tadau hijabi daya bata dazu tasaka tai sallan la'asar, tana idarwa ta kwanta akan dadduman tana birgima tana kuka. "sweetheart where are you? Katafi kabarni, why?" tafashe da kuka.

Aaman tunda suka koma bauchi rashin lafiya yatasa shi agaba bana wasaba, shi kanshi baisan cewa haka son Ameerah ya shiga ranshi ba, ganin yanda yake yasa Dr Ameenu ya sanya Ummy kiran Maman su, da kanshi ya sanar da ita komi, aiko washe gari saiga Maman da baban su aka tattara aka tafi dashi Abuja gabaki daya. Alhamdulillah yadan samu sauki danhar abinci idan mum tabashi yanaci, yanada wata cousin Usaida datake sonshi nan Abba yahada auren su aka saka rana wata daya kuma baiwani musu ba dan Usaida yarinya ce mai hakuri gata yar gayu.

Ayaan na fitowa daga masallaci hospital dinsu yawuce dan sosai yakejin rashin lpy, office din Dr Ibrahim yawuce bayan yaduba shi ya daga kai yace "dude wai menene matsalar ka, kaifa Dr ne bazaka guji abinda zai batama raiba wai, well I know u already know zuciyar ka na gab da buguwa" awahale yaja gajeren tsaki saikuma yamike tsaye yace "thanks lemme get drugs" fitowa yay daga office din yana tafiyar nan da isa ana gaidashi yana daga kai kawai kaman bashine me babbakama Bilkisu kuka ba.
Magunguna yasiya da drip da wasu allurai a pharmacy sanan yadawo office dinshi, saida yasha maganin da kyar dan ya tsani magani kafin ya kalli alluran tsaki yayi yadau wayarshi yakira Dr Ibrahim, ko minti biyu ba'ayi ba ya shigo office din yace "Boy gani" wani irin mugun kallo Ayaan ya watsa mai, dariya sosai Ibrahim yayi yace "dan nadan dana sunan da Abba ke kiran ka dalla" dauke kai yayi ya bude kwalban alluran ya zugo da sirinji ya mikamai kaman ance yay maganan dole yace "yimin kuma ahankali" karba Ibrahim yayi tareda daukan auduga ya juya yamai, ahankali yace "aaauchh" bugemai kafada Ibrahim yayi yace "ashe da zafi kake parke different patients kullum" dan murmushi yayi yace "thanks Man" kwanciya yayi adogon kujeran office din ya lumshe ido, Ibrahim yabishi da kallo daga ganinshi kasan ciwo na cinshi dakuma tunani dan alluran nan ma na kwantar da sha'awa ne, drip din daya ajiye akan saman table ya dauka yana dubawa wanan na ciwon da heart dinshi keyine dakuma magungunan suma haka, ajiye magungunan yay ya karaso wajen kujeran yana gangaro dogon karfen da ake makala drip ajiki ya kalli fuskarshi yanda ya lumshe ido ahankali yace "nama fixing drip dinne?" gyadamai kai yayi, hakan yasa ya tsugunna yakama hanunshi ya makala mai sanan ya gyara ruwan yana shiga jikinshi, saida yajira na kusan 3mins sanan ya daura hanunshi akan heart dinshi beating din dayake yi yasoma dawowa normal normal hakan yasa yajuya yay hanyar fita yace "zan zo anjima" gyara kwanciya yayi tareda sake lumshe ido yana tunanin Bilkisu, ahankali yaciro wayarshi daga aljihu number Dad Fawaz yakira, Neurologists ne likitan brain, sanan babban Consultant ne akan any matsala na kwakwalwa, yana kiranshi bayan sun gaisa yasanar dashi zaizo hospital dinshi gobe wurin shi da matarshi, nan dai yafada mai matsalanta.

Saida taci kukan ta tana kiran sweetheart tagaji sanan ta tashi daga kan dadduman ta cire hijabin tabude kofa tafito falo, zama tayi akan kujera tadau teddy ta tanama kitso tana kallon Channel din cartoon din da tasa yasaka mata dazu. Gajiya tayi ta mike tsaye tana dirke dirke akan kujera tana dariya gabaki daya ta hargitsa falon dan kanta tagaji tadau ruwa tana sha sanan ta kwanta tana dariya ita kadai, harta fara gyangyadi taji ankira salla da gudu tana tsalle tai bedroom tadauro alwala tafito tahau kan dadduman dawani irin tsalle kafin tafara sallan.

Wuraren magrib Big Mummy ta shigo gidan akatuwar jeep dinta driver ta shikejan motar, parking yayi tafito tana sanye cikin jan ashobin biki mai shegen kyau dayaji uban stones, securities ne sukazo ta nuna musu babbar jakarta tace "awuce dashi shashina" tanunama driver jakar da abubuwa ke ciki wanda aka raba nabikin tace "biyoni da wanan" tafiya takeyi na isa kaman wata boss tana danna waya har zuwa Shashin Mami, murmushi lullube akan fuskarta ta shiga falon Mami na fitowa daga kitchen kenan taga hajiya fadada murmushin kan fuskarta tayi tace "oyoyo hajiya saukar yaushe" dan tabe fuska big Mummy tayi tana huro hanci wanda idan da Sabo Mami tasaba, ta karbi jakan dake hanun dreba shikuma yajuya yafita Mami ta karaso wajen tana mata sannu da zuwa Big Mummy tamika mata jakar tace "gashin nan inji Atine tunda bakizo ba wai" karba Mami tayi tace "sabida jikin Ayaan ne ai da nazo bikin zinatu, Hajiya kinkosan wani abin farin ciki da ikon Allah kuwa daya faru kuwa" "saikin fada" Big Mum tafada agadaran ce, cikin nuna tsananin farin ciki Mami tace "wlh anga Bilkisu, jiya wayansu suka kawota daga bauchi, inata so nakira ki nagaya miki Alhaji ya hanani wai surprise zamu miki, dan wajen ki har ya warke anga Bilkisu haji..." baya da Big Mum tayi zata zube yasa Mami tariko ta da sauri cike da mamaki tace "baki da lafiya ne hajiya?" arude Big Mummy tace "Bilkisu Bilkisun mu dai matar Boy kikace angani?" gyada mata kai Mami tayi tana kokarin zaunar da ita akan kujera ganin tarude sabida good news din, kin zama tayi tarike hanun Mami tace "tayaya aka ganta? Meta ce muku?" "kaman ya metace?" Mami ta tambayeta tana kallon fuskarta, da sauri Big Mum ta kakalo wani irin murmushin dole tama Mami, ahankali Mami tace "yarinyar da bama ta yarda damu, tasami shafewan kwakwalwa ne, duk bata ganemu ba, tana ma dakin Ayaan" da sauri Big Mummy tana share zufan daya keto mata tace "ina boy din nawa nata ya shi murna" tabe baki Mami tayi tace "yaje Clinic wai" zumbur Big Mum tamike jikinta har rawa yake da kyar ta saita kanta ta kakalo hawaye tace "Allah Akbar kabiran! Allah mai girma da daukaka, bari naje nadubo matar Boy dina" Mami tace "gama abincin su chan angama bari nasa Salamatu takai musu tunda tahada a food flask already" da sauri Big Mummy tace "basai kinsa yan aiki ba tunda chan zani, ban in wuce musu dashi" bama tajira Mami tamike ba tai dining tadau food flask da plate da spoon din data gani ta fice daga shashin har tana harde kafa tana maganganu da kanta tace "Bala yace tamutu, Bala yace tamutu, Bala eh yace tamutu" haka tadinga sumbatu kaman tababba hartai shashin nasu.
Chapter 64 · 0% Book details