Sashe 57
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Zaune yake acikin mota ya kafesu da ido yanda suke tsalle tsalle su uku ita da zainab da Ummy basu lura dashiba wasan yar gala gala suke yi, tana sanye da doguwar riga ta daura sweetar akai sai tsallake gida gidan take tana dariya daga gani wasan yakai mata, karan wayarshi dayaji shiya fargar dashi daga dogon tunanin dayake yi ganin Dr Ameenu ne yasa ya dauka daga tachan bangaren Dr Ameenu yace "kaga news?" shirun dayayi yasa Dr Ameenu yace "nama san kagani, wat is your plan yanzu kasan dai yakamata ka maidata garin su ko, ka kaita police headquarter da akace duk wanda ya ganta ya kaita, yaushe zaka kaita yanzu" lumshe ido yayi yakara budeso ya daura akanta yanda taketa guje guje su Ummy na binta, ahankali yace "i don't want her to leave Man, tun shekaran jiya nagani a news har a Twitter da Instagram saida naga hoton ta a page din Nigeria police sun saka, i don't know what to do banaso ta bar wajena, i don't want her to leave friend" anatse Dr Ameenu yace "i tot we've talked about this, Aaman tayaya zaka fada tarkon soyayyar wacce bakasan ko wacece itaba, u know nothing about her, bakasan iyayen ta ba, bakasan daga ina takeba, yarinyar daka tsinta rana tsaka kawai sabida ta zauna dakai na watanni saika fada tarkon sonta, tun wuri kama tsamo kanka da kanka, and tomorrow banda office, am off tomorrow bazanje clinic ba inka shirya kaita zan iya binku har kanon" shiru yayi har lokacin yakasa dauke kanshi akan Bilkisu yayyafi ake duksu Zainab sun shige barander suna kiranta tabar ruwa amma taki sai tsalle tsalle abinta take, ahankali Dr Ameenu yakira sunanshi. "Barrister Aaman" ahankali yace "na'am" Dr Ameenu yace "you have to make a decision now" dan lumshe ido yayi yace "wat if muka kaita iyayen ta sukazo suka tafi da ita does that mean bazan kara ganinta ba? Yaya zanyi da raina da zuciyata dake cike da kaunar ta?" "mudai fara kaita tukunna, kayi tunanin wani hali iyayenta ayanzu haka suke ciki, wata nawa basu saka yarsu a idoba wani hali suke ciki just imagine irin farin cikin dazasu shiga gobe idan suka ganta, don't think much abinda kamata kayu kenan ka maidata ladan ka naga Allah" lumshe ido yayi yace "alright Allah kaimu goben" katse wayar yayi ya jinginar da kanshi akan kujera ahankali yake karanto addu'o'i da zasu sakamai natsuwa kafin ya bude motar ya mayar ya rufe ya shigo gidan kaman ance ta daga kai ta ganshi yana tahowa wani irin ihu tayi ta taho da gudu tana murna. "oyoyo sweetheart oyoyo sweetheart dinmu, Anty Ummy sweetheart is back" ganin ya tsaya yaki cigaba da tafiya yasa itama ta tsaya tana washe mai baki tunawa da yahanata fadomai, saikuma ta turomai baki kaman zatai kuka tace "oyoyo fa nake maka sweetheart" ledan snacks din dake hanunshi ya mikamata ta karba tana washe baki tana kokarin budewa yay gaba abinshi hakan yasa ta fasa budewa ta bishi da gudu ganin zata bishi har daki yasa ya tsaya ya juyo ya kalleta ahankali yace "jeki chanza kayan nan bakiga kin jike bane" kara washemai baki tayi tana kallon fuskarshi tace "in chanza" gyada mata kai yayi da sauri ta juya tai dakinsu, cire kayan tayi tasake saka wani doguwar rigar atampa black ta daura dan kwali tabar ledan snacks din adaki tafito harda gudunta, afalo ta sameshi rike da ruwa yana sha ta zauna akusa dashi, cire ruwan yayi daga bakinshi yace "ina Ummy" "sun tafi gidan kaji" gyada mata kai yayi kawai dan bayason magana ya lumshe ido da sauri takara matsowa kusa dashi kaman zata shige jikinshi tace "sick?" yagane tambayan shi take ko baida lpy hakan yasa ya girgiza mata kai ya bude ido tareda sauke ajiyar zuciya hannunshi yasa a aljihu yaciro wayarshi daga pocket yana daddannawa kafin ya bude page din policeng inda aka saka hoton ta ya bata wayar ta karba tana kallonshi ahankali yace "look at d screen wacece wanan?" da sauri ta kalli screen din hoton ta kafe da ido sosai sanan ta kalleshi ta nunamai wayan tace "nine?" ta tambaye shi, wani irin ajiyar zuciya yayi yace "yea kene ance sunanki Bilkisu Abdul..." makemai kafada tayi kaman zatai kuka tace "my name is Ameerah ko sweetheart" shiru yayi yana kallonta daidai lokacin Ummy ta shigo tanamai sannu da zuwa ya amsa sanan yamata magana da yaren french. "ki hada mata kayan ta gobe zan kaita garin su police sun bada sanarwa chan police headquarter zamu kaita nida Dr Ameenu na kano, insha Allah once naga sun kira iyayen ta agabana nagansu dakaina saimu juyo mudawo, zainab ta tayaki kwana zanma Umar magana ya barta" gabaki daya jikinta yay sanyi hakan yasa ta juya kawai ta shiga daki dan wani irin kukane yazo mata, sanan ya kalli Bilkisu data tasashi agaba tana kallo yace "wat? Mesa kike kallona haka" dariya tayi sosai dan har tana buge filon kujera suna faduwa kasa sanan ta kalleshi cikin dariya tace "sweetheart wlh ina sonka ne" tacigaba da dariya tsayawa yayi yana kallonta he's sure awajen su Ummy takejin irin maganganun nan, mikewa tsaye yayi jin ana kiran sallan magrib yace "go and pray zanje masallaci" kaman zatai kuka tabishi da kallo harya fita sanan ta share yar hawayen daya zubo ta wuce dakinsu.
Wuraren nine yadawo lokacin hartai bacci yaci abincin da Ummy takawo mai yawuce daki duk jikinshi yay sanyi.
Wahe gari wuraren goma nasafe yafito daga dakin idanunshi sunyi jajir shima sabida uban knocking kofar shi datake tayi tanamai kuka ne, murmushi yamata bayan ya bude ganin yanda take uban kuka yace "stop crying oya je Ummy ta shiryaki mufita" ya kalli Ummy dake zaune akan kujera yamata alamu dakai hakan yasa ta mike tariko ta sukai dakinsu shikuma yakoma ciki ya shirya cikin manyan fararen kaya dasuka karbe shi sosai yafito da baban trolley dinta da Ummy tahada takawo dakinshi tun jiya da night yafito dashi yasa a boot din mota daidai lokacin motar Dr Ameenu ta danno kai compound din dan murmushi yayi yajira haryay parking yafito shima cikin manyan kaya shada blue yazo yace "guy gaskiya da motar ka zamu bazan kona maina ba kafini kudi" tsaki yay ya wurgamai key motar ya chabe yace "kai xakai driving" ya kwalama Ummy kira sabida tafito da ita shikuma ya bude motar ya shiga Dr Ameenu ma ya zaga ta bangaren driver yabude ya shiga, ita tafara fitowa da gudun ta tana sanye cikin black body hug da black straight skirt sai Ummy ta daura mata maroon kimono me shegen kyau akai ta kulle mata belt din kimono ta gaba sanan tamata rolling black vail akai da keda one one stone ta bakin gyalen tasaka mata takalmi baki maidan tudu daya fito da hasken kafarta, gabaki daya Yay nisa a kallon ta yanda tai kaman balarabiya tsaban kyau maganar ta dayaji akanshi ya fargar dashi. "sweetheart wai zamu fita?" gyada mata kai yayi batare dayace komiba, shidai Dr Ameenu waya yaciro abinshi yakira matarshi suna hira, da sauri tace "ina zamuje park zamu?" girgiza mata kai yayi yace "shiga mota garinku zamu" "inane garin mu?" tafada tana murna, dan murmushi yamata yace "shigo mota muje kigani" tsalle tayi ta bude kofar baya ta shiga tanama Ummy bye bye, kudi yaciro dayawa yabama Ummy yace "I will call u anjima" addua sosai tamusu sosai sanan Dr yaja motar suka bar gidan saida suka danyi nisa yace "ka kosan na dauko file dinta na hospital kasan police da tambayoyin banza kafin suce mumuka saceta na dauko file dinta kai ID card dinama na jikina am not ready to enter any gbese" dariya yadanyi sabida yanda ya karashe maganan yace "kai kayi aure nazaci zuciyar ka zata chanza ta dena wanan tsoro ashe babu abinda ya chanza" hararan shi Dr yayi yacigaba da tuki batare dayace komiba itakuma tana baya saiyima teddy ta mai gashi kitso take tana yar wakarta na yar gala gala yarinya yar gala gala wasan yara ahankali, ta madubi yake ta kallonta har daga baya bacci ya kwashe ta.