Sashe 5
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Layla ne ta shigo dakin ta kalli Bilkisu dake kwafe note tace "Anty Isyaka na falon Baba yana jiranki" satan kallon Mama dake tsefema Raiyana dogon gashin ta tayi taga ko kallonta batayi hakan yasa taidan murmushi tadau dogon hijabin ta tafita daga dakin, dakin Baba tai sallama ta shiga, daki ne mai fadi wanda kusan littatafan addinine suka cikashi, koina agyare ga kamshin turaren wuta, daga gefe kuma isyaka ne dayaci gayu cikin normal shadda abinshi sai kamshin turaren duri yake yanata kallonta akunyace ta zauna nesa dashi akan tabarman tana wasa da hijabi tace "ina yini" kara gyra zama yayi tareda lankwashe kafa ya hade tafukan hanunshi yana murzawa yana murmushi yace "barka da zuwa Bilkisu gimbiyata, gimbiyan duka matayen garin nan, gimbiyar dake mulka zuciya ta, saurayinyar mata mai gadon zinare" dariya tayi ta kawad dakai dan ba karamin kunyan shi takeji ba, Isyaka amintaccen almajirin Baba ne, tun yana karamin yaro aka kawoshi almajiran ci wajen Baba harya girma, shekaran shi 25 yanzu, yanada aikin hannu dan ya iya aikin hula da aikin su shadda, Baba yariga yabashi Bilkisu tun tana yar yarinya, yanzu haka ita yake jira dazaran ta zana jarabawa za'ayi auren su yakoma da ita kauyensu nachan hanyar sokoto.
Dan gyara murya yayi yace "bakice komiba mar'autul saliha? Ya karfin jiki" anatse tace "Alhamdulillah na warke ai tun dazu" wata torchlight phone yaciro daga aljihun rigar shi yazo gabanta ya ijiye mata akan hijabi yace "gashinan ki rike inaso mudinga waya tanan" da sauri ta kallai sai kuma ta make kafada ta kwaye fuska kaman zatai kuka, ashagwabe tace "a'a nidai bazan karba ba, Baba bayason muna amfani dawaya Allah kabarshi nagode" tunda take maganan yakafe ta da ita hakan yasa ta dukar da kanta kasa, dan ajiyar zuciya ya sauke kafin ahankali yace "har yanzu kinki dena shagwaban nan ko, dan Allah kidena mini ji nake kaman zan mutu idan kinayi, ina kaunar ki dayawa Bilkisu, yanzu dai Baba yariga yaga wayar ai yama yarda nabaki saisa nakawo miki, gwara munayi munadan taba waya ko? Muma muyi soyayyar yan gayu" gyada mai kai tayi tana murmushi daya bayyana fararen hakoran ta tace "nagode" dariya shima yayi cike da murna yace "bari namiki waka" dan zaro ido tayi tana kallonshi yamata wani irin kallo yace "dukda ina malami ai dole na koyo waka nama gimbiyata dan na faranta mata rai" dariya ta sake yi harda rufe fuska, dan gyara murya yayi hakan yasa ta tsayar da dariyar tana kallonshi, yawani kalleta yana nuna ta da hannu yace "Bilkisu na yarda dake, dauki amanata ki rike, kin dace da zama dani, Bilkisu gimbiyar raina, Bilkisu hasken idaniyata, Bilkisu ina kaunarki, Balkisu tauraruwan raina, Bilkisu abun kaunataaa" bakaramin dadi wakan yayi mata ba sosai ta dinga dariya tareda boye fuskar ta cikin hijabi, "ya isa haka dariyan to yawan dariya baida kyau a addinin mu, tashi kije ki kwanta akwai school gobe" addu'a yayi sanan ya mike tsaye yace "saikuma gobe ko, kiyi alawa kafin ki kwanta zan kiraki tawaya cikin dare sabida kitashi kiyi salla ko" gyadamai kai tayi yafita daga dakin yana mata murmushi, hakan yasa itama ta tashi sanin Baba nadakin Umma yasa takoma dakinsu ganin Mama tai bacci da Layla aka gado, yasa ita tadawo falo ta kwanta kan dagon kujera 3 sitter wacce dama anan take kwana itakuma Raiyana 2 sitter take kwana kokuma wani zubin su kwana akasa.
Da asuba bayan sunyi salla duk dakin Baba sukaje karatu ya koya musu Qur'ani, hadisi da fiqhu, bayan sun biya wanda yabasu jiya harsai wajajen karfe shida sanan suka fito, kitchen ta shiga dan hura wuta Raiyana kuma taja ruwa dan wanke bayi da makwarara, itakuma Layla tadau tsintsiya sharan tsakar gida, suna gamawa duk suka diba ruwan zafi sukaje wanka sukaci dumamen su da kokon da Bilkisu ta dama sanan suka tafi makaranta. Gyara dakin Mama tayi fess ta kunna turaren wuta sanan tawuce dakin Baba ma ta gyara tana gamawa yafito daga dakin Umman hakan yasa tawuce nan ma ta gareshi Umma sai shimata albarka take, dakinsu ta dawo tadau hijabi tasa ta kalli Mama dake shan koko tace "indanje gidan Baaba Mama?" dari biyar din kan kujera Mama ta dauka ta mikamata tace "gashi nanma daganan kibata kice nace kudin zubi na nayau" da sauri tafita saida takara gaida Baba da wasu alamajiran data gani taredashi sanan ta wuce ta tafi, akofar gidan ta hango Muji yana kokarin tada keke da sauri ta karasa wajen ta daure fuska tace "biyani dari biyuna yaya Muji" saurayin wanda da kadan yafita tsawo da jiki ya dago kai tareda daure fuska har zaiyi magana saiya ga wayar hanunta da sauri yasa hannu yakar ba yana jujjuyawa yace "iyye waya saimiki waya dan aramin?" make kafada tayu tace "bindi salon kaje kabata min, jiya jiyan nan fa Ishak dina yabani" tsaki yayi yace "yarinya anjima nan nima zan dawo da tawa sabuwar wayar yau xan bada karamar tawa na siyo mai camera ma, soft touch, tunda hakane bazan baki daniba, kuma bazakimin hoto dawayar ba" tabe baki tayi tace "kai Yaya Muji Karya kasa, a ina kasami kudin siyar irin wayar nan daka kira wurin dubu ashirin fa ake sayar da irin wayoyin nan?" dariya yayi yace "kinga tafiya ta nidai, kuma bazan biya daribiyun ba" yana fadin haka yaja keken shi yay gaba, fashewa tai da kuka ta shiga gidan tafada jikin Baaba daduk ta rude tana tambayan ta lpy cikin kuka tace "ba yaya Muji bane yaki biyana kudina ba" share mata hawayen Baaba tayi tace "bari yadawo saiya baki dan gidansu, tashi kitayani wanan wankin dama dukna kosa kizo" karban wankin kayan tayi tama Baaba tsaf tana gamawa Baaba ta zubo mata shinkafa da miya zama tayi ta cinye harda kari kai Bilkisu badai ciba wolla.