← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 89

Sashe 27

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

**************
Tun tanama su Umma, Mama da Baaba kuku asaurareta ana lallabata har yazo kowa yafita harkan ta to uban ma me zasu iya aure dai anriga an daura saidai kuma abisu da fatan alheri, ganin babu mai sauraron ta danhar su Walawa sunfison Ayaan sunce mezatayi da Isyaka daya wulakan tata ranan daurin aure yace bayaso, tama godema Allah yaro dan gayu yace yanayi, hakadai ta tattara ta manta da alamarin tacigaba da zuwa school abinta ta dage da karatun exam, Mami na yawan kiranta ganin haka yasa duk Friday saita turama Mami Friday message mai dadi da ma'an hakan ko ba karamin faranta ran Mami yakeba.
Cikin iko na ubangiji ta fara zana jarabawan ta abinta sosai ta dage tana karatu ta manta zance wani Ayaan da Isyaka, inbama su Walawa sun kirata da matar Ayaan ba wanda yanzu shine sunanta har mantawa ma take ita matan aure ce, kumama wai Matar dan iskan nan maisa sarka da dan kunne hmm.

Zaune yake akan daya daga cikin kujerun platinum table dake cikin club din wanda aka jerasu mussam sabida mayan, non alcoholic wine mai sanyi waiter ya zubamai a glass cup kasancewar sunsan shi bayashan alcohol, gefenshi wasu maza ne hadaddu guda biyu wanda suke friends dinshi tare sukai school, daya daga cikin sune mai suna Fawaz yace "wai kai bazaka je ka dubo matar kaba yanzu more than a month kenan da bikin ku da baka gayyace muba" jan tsaki yayi tareda kara relaxing ajikin kujeran dayake kai yanabin wankan dake tashi a club din na Drake, dariya su biyun sukayi banda shi daya wani lumshe ido dayan ne mai suna Paul yace "yo wai tayaya ma wanda zai aureta kace yafasa awurin daurin auren, mekayi Ayaan? I know u have something to do with him saying bazai aureta ba" sai a lokacin yadan yi murmushi kadan kafin yawani tabe baki yana girgiza kai yace "nothing much, I just threaten d poor guy, bayan nasa an kamomin shi na kusan harbinshi da bindiga ya tsorata harda kuka fa wai bayason ya mutu yanzu he's just 25, yadan ban taudayi so saikuma na cikamai aljihu shikenan" dariya sukahau yi dukan su Fawaz yace "shege mugun iche, ashedai kana son yarinyar" da sauri ya kallesu kafin ya murtuke fuska yace "guys banson iskanci, ni" yanuna kanshi yace "ni, ni, me fa, inso yarinyar nan wanan yar kauyen? God forbid, Allah ya kyauta, she is not my type infact tamamin kadan as my woman, i did wat i did for Pops, u know he's old yo, so banison abinda zaisa yay breaking down, i gats make d old man happy now" atare samarin suka gyada kai suna "yeah hakane, we gats make our Pops happy kam" drinks dukansu sukai sipping atare Fawaz ya kalleshi yace "wat about ur Meram?" kallonshi yadanyi kafin ya maida mai da tambayar. "wat about her?" Fawaz yay yar dariya yace "i mean baka sonta bazaka aureta ba ita? Me relationship din dake tsakanin ku dont u have feelings for her" tabe baki yay yace "Gee, get this straight nifa aure ko soyayya bayama ajenda na, infact inda baku tunamin da dat low life girl da Pops yahadani da itaba ninama manta inada wata so called wife, and Meram, Meram" yakira sunan sau biyu yanadan rolling eyes dinshi saikuma ya tabe baki yace "ina more rayuwana da ita ne kawai anytime am in d mood, babu komi tsakanina da ita, she's just a girl dat love giving her self to me okay" dariya duka sukayi Fawaz yaciro wayarshi yace "lemme call my babe nima" tabe baki yayi kafin ya mike yaje dance floor yafara rawa abinshi yana sipping wine din glass cup din hanunshi.

Sai gurin sha biyu suka fito daga club din kowa yaja motar shi dan zuwa gida. Abangaren shi yay parking yafito yana kwance belt din wandon shi ya bude kofa ya shiga daki, zaune yaga Abba a kujera ga dukkan alamu shiyake jira, dan sosa kai yayi yamaido kofan ya rufo yazo kusa da Abban daya kafeshi da ido dan murmushi yayi yace "Pops bakayi bacci ba" yay maganan yana zama tareda daura kanshi akan kafadar Abba, sosai yay niyar mai masifa amma saiya sassauta murya cikin lallashi yace "Boy lokaci yayi da u will stop clubbing, da nabarka ne sabida inama kallon yaro but yanzu ai ka girma tunda ma har ka ijiye mata, ehen talking of mata wat do you mean ne eh? More than a month yanzu bakasan kaje ka duba matar kaba, ina so gobe goben nan ka shirya kaje" daure fuska yay tamau kaman zai fashe yace "zanje hospital gobe akwai aikin da zanma wata" "karya kake" Abba yatari maganar shi afadace ya nunashi da yatsa yace "wlh inhar baka tattara komi ka ijiye gefe ka wuce kadubo matar ka gobe ba saina saba maka" ya kamo kunnenshi tareda daye dankunen diamond din daya makala da gum kara yayi. "Pops zafiiii" ya dafe kunen kaman zaiyi kuka Abba ya cillar da dankunen yace "wlh karna kara ganin ka dasu, wanan shegiyar sarkar ma kacire, kai ai ba mace bane" turo baki yay yace "sarkan ma ai bana mata bane, baka gani bane Pops namaza ne fa" "I've said my own, first thing tommorow morning kabar gidan nan kawuce kaje ka dubo matar ka, hakkin ta na kanka be careful" Abba ya wuce yafita yana masifa.

Da gudu take tafiya danyau ko tsayawa karban waina batayi ba daga wurin Baaba, yaune take rubuta last paper ta Civic education kuma karfe biyu ranane paper bacci tayi babu wanda ya tasheta dan Mama da Umma sunje barka, biyu saura minti goma ta tashi hakan yasa ta zabura tasaka kayan makaranta tafito tana kaiwa bakin titi tasami Bus ta shiga, abinka da bus sauke dauka ba ita takai makaranta ba wuraren karfe biyu da rabi, sunayen Allah kawai take kira ta shiga makarantar da gudu tai exam hall atsorace takai bakin class din ta tsaya yan aji sai kallonta suke su Walawa dake rubutu suna mata alamu data shigo, kallon fuskar invigilator tayi ganin baice karta shigo ba saima wani kallon wulakanci dayake mata irin na kinyi latti kinkuma tsaya awaje dinan yasa ta kwasa da mugun sauri tai cikin hall din, tsayawa tasake yi dan tsoron zuwa ta karbi booklet da question paper take ganin ya mikomata daga inda yake zaune yasa tai inda yake da saurin ta, zuiiii tai wani irin mugun faduwa sakamakon bawan ayabar dake kasa data taka wani irin mugun ihu tayi dan saida ajin duka ya dauka sakamakon faduwa datayi gabaki daya ta saitin ciwonta, dan ciwonne ma yafara buga kasa kafin sauran ilahirin jikinta, da sauri shi kanshi invigilator ya sauko daga kan kujera su Walawa ma haka duk aka zagaye ta, Walawa tasamu ta damke da karfin bala'i cikin kuka tace "Walawa na bige ciwona uhm uhm uhm" wani irin nishi take tana kuka sosai tama kasa magana, invigilator yace "ku kira principal dinku" da gudu yan ajin aka fita aka kira principal koda tazo tuni Bilkisu tafice hayyacin ta sabida azaba kuka kawai take da ihu, Keke napep principal tasa aka kira ta dubi dabilan ajin tace "wayasan gidansu?" su Walawa ne suka daga hannu hakan yasa principal din tace "kuzo ku maidata gida wurin iyayenta ku dawo yanzun nan sabida kuyi jarabawar ku" kokarin mikar da ita ake ta kankame Walawa tana ihu "dan Allah dan Allah nace wlh inna tashi fashewa cikin nan zaiyi" tana maganan tana kukkule ido kaman mai shirin suma, principal tace sudauketa, taruwa sukayi suka dauketa suka saka a Keke Walawa da Aisha shehu suka bita sai gida.
[7/17, 12:04 PM] +234 814 359 8303: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

35 - 36

Yafi minti biyar da parking a kofar gidan nasu amma yaki fitowa saima kallon kofar gidan yake daba kowa dan duk almajiran sun tafi bara, yana sanye da dark blue shadda da akamai aikin hannu mai shrgen kyau, jumper ne rigar danshi ya tsani tazarce, kanshi ba hula saidai gashin shi dayay lub lub dashi sai uban kamshi yake, tsaki yakara ja ya dunkule hannu ya daki iska "f*ck! hanayinyar dayaji yasa yadan dago kai, yan mata biyu yagani da fararen hijabi da purple dankwali da purple wando alamun yan makaranta ne sun tsaya gaban keke suna mika hannu suna magana alamun da wani akeken dasuke ma magana, daya daga cikin su yaga ta juya ta shiga gidan su da sauri chan sai gashi tafito da Baba yasa babban kaya kanshi da rawani irin ta malamai, magana yaga Baba natayi baya iyaji sabida glass din motar arufe suke fararen hannu yaga an miko daga keken wanda kumbunan hannun ke zagaye dajan lalli dayay jajir, hannun Baba ya kama, ya kara daya ta bayan wuyan shi da kyar ta sakko da kafa daya kasa saikuma ta kece dawani irin kuka da shida kanshi saida yaji daga motar, kamota Baba yayi hakan yasa tafado jikinshi tama kasa mikewa da kyau tana neman yin kasa tana wani irin kuka da sauri su Walawa suka taya Baba riketa dukansu, hankali tashe Baba ya rikota da taimakon su sukai cikin gida tana mugun kuka, dan tabe baki yayi kafin yace "wats wrong with her?"

Shimfideta Baba yayi akan tabarman dake dakinshi sabida tsakar gida yajiku dan dazu anyi yayyafi, Baaba dasu Umma suka zagayeta dan bama su dade da dawowa daga barka ba, ganin yanda take ihu tana kuka yasa Malam ya tsugunna ya daga hijabin tareda rigar ya janye farar shimin datasa ya kalli ciwon bugewan datayi yasa wurin yay ja sosai abunku dafara, mikewa tsaye yay yakalli Mama yace "cire mata kayan nan iska yadan shigeta kotaji dadi, bari naje na nemo taxi abakin hanya saimu kaita asibiti" to Mama tace jiki asanyaye ta tsugunna tana kokarin maida hawayen dataji yana kokarin zubomata, cire hijabin da rigar tayi ta barta da farar shimin kadai sai kuma wandon makaranta jikinta zata mike ta cafko hanunta tana kuka tace "ina zaki Mama? Dan Allah ki rikeni, Umma, Baba" takirasu duk awahale, dan uban kukan datake yasa ta galabaita, zuwa wajen Umma tayi ta rike, Baaba kuma dasu Raiyana duk suka tsaya akanta suna mata addu'a.
Chapter 27 · 0% Book details