Sashe 38
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Maman Abd Shakur
48...
Wani irin juyo da ita yayi azuciye ta fuskantoshi sahketa yay kaman mahaukaci yana zazzaro ido "me kikace?" kasa magana tai sabida yanda ya shaketan yana wani irin jijjigata kaman zararre ganin idanunta na rurrufewa kaman zata mutu yasa ya hankadeta gefe azuciye yafita daga ruwa tareda yin kwallo da glasscup din wine dinshi ya shiga cikin gida, wani irin kuka tafashe dashi tana tari kafin ta lallaba tafita daga pool din tai ciki itama, tundaga kasa takejin yanda karan music ke tashi daga dakinshi kaman zai fasa gidan, lallavawa tayi tahau stairs tai dakinta tana shiga tasaka key, bayi tafada tai wanka da ruwa mai zafi sosai kafin ta dauro alwala tafito tai salla, haka tawuni adaki batare data fitoba tai girkin abinda xataci ba, har bayan magrib waka ketashi daga dakinshi kenan bai fita yay salla ba, tayaya zata zauna da mutumin da baya bin Allah, babu abinda ya damu dashi to yanzu ma tayaya zata chanza shi?. Jin shiru dakuma alamun takunshi yafito daga daki ya sauka kasa, sai chan taji karan fitan mota yasa tasan yafita daga gidanne, saukowa tai taje kitchen ta dafa Indomie kafin ta dawo dakinta taci tai sallan Isha tai karatun Al Qur'ani har wuraren goma nadare sanan tai baccin ta.
Ko a cikin bacci ma mafarke mafarke taketa yi har da asuba ta tashi tadauro alwala tazo tai salla nan kan dadduma ta zauna tana ta addu'o'i har gari yay haske sosai, wuraren 9 tafito babu kowa agidan hakan yasa ta gyara gidan ta gyara ko ina ta kunna turaren wuta a burner tea kawai ta iya sha ta zauna tai shiru tanata tunane tunane, kafin ta dauko wayarta ta kunna data ta shiga goggle ta tai typing ya ake chanza mutumin dabaya bin Allah yakoma yanabin Allah, nan dai taga amsoshi da dama daga ciki akwai yimai wa'azi, a tunatar dashi mutuwa da sauran su dai, tabe baki tayi wanan maisa sarkan yanajin wa'azi ne, awani page ne taga sun rubuta za'a iya tsorata shi hakan zai iya sa ya chanza, bata ma tsaya ta tantance me suke nufi da tsoratashin ba kawai zuciyar ta yakama maganar sosai, tana ta tunane tunane tsorata shi, tsorata shi, tayaya zata tsorata shi yabi Allah, sai chan kuma tai dan murmushi da sauri ta bude contact dinta tunawa da Mami tasa mata number kowa na gidansu awaya, number shi ta shiga tamai sending message "please i want to go out and buy something very important" yana zaune a office yana shirin shiga theater yaga sakon ya shigo dogon tsaki yaja yace "ina tasani mtsww" yaja tsaki ya ijiye wayar garin ijiyewa mistakenly ya danna k, aiko tana ganin k taji dadi da gudu takoma sama tai wanka, riga da zani tasa na atampa tasaka hijabi tadau kudin da Mami tabata dayawa tasaka a jaka da wayarta ta dauka tafito, mai gadi tacema tana son ya kira mata keke napep aiko sai gashi yakira mata, shatan shi tayi har kasuwa tabashi kudi dayawa tace yajirata zai maidata gida, aiko yadinga murna
Yace xai jirata anan, shiga tai cikin kasuwan saika shagunonin saida yadi, na farkon ta shiga, farin yadi ta yanka har yadi shidda ta biya kudi mai dinkin wajen tabamawa tasa yay mata doguwar riga mai shegen fadi da dogon hannu shima mai fadi akai abu abaaya kaman fiffike, murmushi tai ganin yanda rigar tayi tabiya kudi tafito tanata kalle kalle wurin, shagon wasu arna masu kitson attach tagani ta tsaya tanata kallon dogon gashin wig din data gani ajikin kan roba dasuke daurawa, kaman mai tunani kafin ta nisa ta shiga shagon ta tambaya nawane aka cemata dubu goma hakanan ta biya tafito tasai wani farin hodan yara na pears tabiya tafito sanan tabi hanyar data shigo kasuwar tafita mai keken ko nanan ta shiga suka koma gida kara bashi kudi tayi yanata mata godiya itakuma ta shiga gida rai fess, akarkashin gadon dakinta ta tura duka abubuwan gabanta nafaduwa tai sallan azahar harda rokon Allah yasa ya tsoratan sosai, sanan ta sauko kasa ta dafa white rice da stew ta dibi iya cinta takoma sama taci ta kwanta sai bacci, haka dai tawuni tana tunane tunane da neman nasara wurin Allah, wuraren goma tana shirin kwanciya taji shigowar shi gidan hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya tai fixing alarm awayarta karfe biyun dare kafin ta gyara kwanciya tai addu'an bacci sai bacci.
Karfe biyun dare alarm yafara ringing da kyar ta mike tsaye ta bude ido tana dafe kai, bayi ta shiga ta kukkuro baki tafito, agaban gadon ta tsugunna ta jawo kayan daga karkashin gado, doguwar farin rigan ta warware ta daura akan yar figigiyar rigar baccin dake jikinta, rigan ko har kasa yake jan mata, hannun ma yafi hanunta tsawo gashi da fadi saitai kaman wata fatalwa fatalwa aciki, hular dogon gashin tasaka da kyar dan bata iyaba, da sauri ta kalli kanta amadubi yanda tai kaman wata aljana mayya yasa ta ware ido, hodar ta dauka ta zazzaga sosai a hanunta ta lapta a fuskarta sosai saitai kaman aljanna da gasken, tasa hannu ta barbaza gashin ta gaban fuskarta sanan takara kallon yanda tai ita karan kanta bama kanta tsoro take ga kirjinta wani irin dukan biyar biyar yake, ahankali ta bude kofar dakin ta fita tai gaban dakinshi tadade a tsaye tana addu'a kafin ta tattaro jarumtarta takira sunayen Allah, sanan tabude kofar dakin ahankali ta shiga babu hanske sosai dakin sai dan dim light daya bari tana iya hango shi yanda yake baccin shi hankali kwance akan lumtsatsan gadonshi, ya lullube tundaga kafarshi har zuwa cikin shi yana baccin shi daya karama fuskarshi kyau, karasawa gaban gadon tayi ta tsaya zuciyar ta kaman zai fashe wani irin ajiyar zuciya ta sauke tana dafe kirjinta kafin ahankali ta mikar da hannunta tareda girgiza kanta tayanda gashin wig din ya yabazu sosai, dan gyara murya tayi kafin tai wani irin murya tace "Ay yaaaa nuuuuu, Ay yaaaaaa nuuuuuuu, Ayyyyyy Yaaaaaaa, Nuuuuuuuuu" dan motsi yay kaman yasan ana kiranshi, wlh takusa fitsari ajiki da kyar ta daddage ta kirashi da karfi bala'i "Ayyy Yaaaa Nuuuu" firgigit ya bude ido ya daurasu akanta, takusa sumewa amma bata bari yagane ba saima kara mikar da hannunta da rigar yaboye tayi tai wata irin murya tace "Ayy yaaa nuuuuu nu" wani irin ihu Ayaan yayi yamatsa baya da sauri dan sai yanzu idanunshi suka sake clearing, kara matsowa tayi tana wani jujuya kai dan yahango farin fuskarta da kyau tai wani iri da hannu kaman zata kamoshi ihu yay "Popsy" yakira atsorace wani irin murya tai tace "am yourrrr spirittt, kai saaakoo aaakkaaa baan in kaawooomaaa" wlh gabaki dayan jikinshi rawa yake bilhakki ya tsorata yana komawa baya me wanan waye wanan a tsakiyar daren nan, tana biyoshi tana wani irin jujjuya kai kaman zombie tace "ance-idan-har-aka-koma ga Allah-ba-zaka gamu da fishin ma'aiki, kadena wasa da salla, sallan ma ajam'i zaka dinga yi, ka gyara rayuwar ka, kaaa naaatsuuu kaaabi Allah yakai wanan bawan kanaji na kona maidakai biri" gyada kai yayi da sauri kaman zaiyi kuka yakasa kallonta saima shishigewa dayakeyi a bangon gado, itama yanda takejin wani irin tsoranshi na shiganta idan har takara koda minti dayane zai iya kamata hakan yasa tace "kulle idanun ka zan kooomaaa duniiiyarrr mu" da sauri ya kankame ido ganin haka yasa ta juya sadaf sadaf ta bude kofar ahankali tafita ta shiga dakin ta da gudu, ta cire rigar ta goge hodar fuskarta dashi sanan ta cire gashin tahadesu ta dukunkune ta tura karkashin gado tahau gado da gudu tareda jan bargo tana numfashi sama sama kirjinta ko kaman zai rushe sabida tsoro.
[7/21, 9:27 AM] +234 706 571 7620: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Maman Abd Shakur
49 - 50