← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 89

Sashe 8

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu atsakar gida Umma data fito daga kitchen ta tareta tace "maiya sameki idanunki suka kumbura haka?" shiru tayi takasa magana dan ta tsani yin Karya, sai hawaye tafada jikin Umma tana kuka, Umma dukta rude tacirota daga jikinta tace "cikin newai?" girgiza mata kai tayi ahankali tace "dukana Sargent yayi amakaran ta" tai maganan tana nuna mata hannun dayay jajir "wayyo Allah sannu kinji Allah zai saka miki, jekiyi wanka kizo nazuba miki tuwo, Maman ku dasu Raiyana suna gidan Baabar ku" daki ta shiga ta cire kayan makarantar ta dauro zani akirji tafito rike da kayan makarantar ta zuba abotiki, kan window kitchen takoma ta dauko omo ta zazzaga aciki ta jawo ruwa daga rijiya ta wanke kayan fess ta shanya kafin takara dauraye botikin taja ruwan wanka tai bayi, tana tafitowa Umma ta zuba mata tuwo nan tsakar gida ta zauna ta tadashi tass dan miyan kukar harda wake yau akasa aciki, tana gamawa ta wanke hannu takai kwanon kitchen ta shiga daki ta dauko wayarta ta kunna, aiko kiran Isyaka ya shigo dauka tayi yay mata sallama anatse. "Assalamu Alaykum gimbiyar zuciyata, waya tabamin ke amakaranta idanunki sukai ja haka?" kaman zatai kuka ta harari bangon dakin tace "ba Sargent din school dinmu bane ba, yawani dakeni da bulalar inji a hannu" dan lumshe ido Isyaka yayi akan dakalin waje dan duk dalibai sun fita bara sai bayan sallan Isha'i za'a cigaba da karatu, malam ma bayanan, ahankali yace "kece kin dage saikin yi karatun nasara, mezaki yi dashi? Kinada ilimin addinin ki kin sauke yanzu kina kan hadda wacce kin kusa gamawa, kin haddace hadisai da dama kin iya littatafai da dama duk wanan ilimin addinin naki kika dage saikiyi na nasara, mezakiyi dashi, ai dole kisha duka haka kam, mutumin daba muharmin kiba yakama yana dukan ki, danba wanan makarantar ba dayanzu munyi auren mu natafi dake garin mu anya Bilkisu kina tausayina kuwa?" gyadamai kai tayi tace "kayakuri kaga watan gobe ma zamu fara jarabawan, muna gamawa komi yazo karshe" dan ajiyar zuciya ya sauke yace "shikenan Allah ya bada sa'a, sanan gobe zamuje school din saina koyama Sargent din hankali waye shi dazai tabamin gimbiyar mata, mar'atu saliha" dariya tayi sosai tana auna Isyaka da Sargent hakan yasa yace "mekike ma dariya?" murmushi tasake yi tace "babba nefa Sargent din?" "kina nufin banda karfin dukan shine kome?" zatai magana taji yakatse wayar, wayar tabi da kallo kafin ta fashe da dariya harda rike ciki tace "to daga fadin gaskiya Sargent ai babba ne kaiko bama kakai girman Sergent ba balle nasa rai zaka iya ramamin" kwanciya tayi kafin ta ijiye wayar akan kujera ta lumshe ido haka nan taji tana tunanin mahaukacin nan.
Wuraren 9 ta shigo dakin nasu dan daga dakin Abba take ta tsugunna agaban Mama dake kada lagwani, "Mama inje gidan Baaba?" "saikin dawo" da sauri ta zuri hijabin ta dake kan kofa har kasa tasaka sanan ta wuce uwar daka ta tsugunna karkashin gado ta ciro asusun ta tadawo palo ta zauna kan kujera tana jijjigawa, Mama ta kalleta tace "mezakiyi da asusun?" adan tsorace tace "fasawa zanyi Maman mu?" "kiyi meda kudin?" Mama takara jefa mata wani tambayan kasa amsawa tayi saima wasa da hijabin ta tahauyi, kafin ta dago kanta a tsorace tace "gidan Baaba zankai" dauke kai Mama tayi daga kallonta tacigaba da abinda takeyi hakan yasa ta saci kallon maman nasu kafin tadau asusun tafita daga dakin da saurin ta.
Akofar gidansu Baaba ta tsaya ta fasa asusun dayake na katsa ne, ta tattare kudin ciki ta kirga dubu biyu da dari uku ne sanan ta shiga gidan, Baaba ta gani gaban murhu Baaba tace "yar arziki kinzo" shiga dakin Muji tayi tace "ina zuwa Baaba" samunshi tayi yana shiryawa zai fita hakan yasa tazo kusa da shi tawani yi laushi dan tasan halin shi, ahankali tace "Ya Muji inkanama Allah ka kaini muyi aikin lada" "aikin ladan mene?" ya tambaye ta yana kokarin daukar sabuwar wayarshi daya saya ta gionee, wayar tabi da kallo kafin tace "dan Allah ka kaini muje muba mahaukacin nan abinci sanan in sharemai wurin nan dayake bacci kaji" wani kallo Muji yabita dashi hakan yasa ta tsugunna agabanshi tafashe da kuka, cikin kuka tace "ya Muji karka manta akwai karuwar data shiga aljanna sabida kare, taimako da kyautatawa sune dabi'un dakowani musulmi yakamata yanada shi, bamusan dame Allah zai dubemu yaji kanmuba yasamu a aljanna, kaji dan Allah, kuma karka fadanma Baaba sirrin mune wanan dan Allah ka kaini, nibanaso naje ni kadai ne, tsoro nakeji kaga jiyama ya yanke sosai akafa saisa nafasa asusu na musaimai takalmi ahanya da riga sabida ya chanxa yagargiyar jikinshi" kudin datake nunamai ya kalla mamaki dukya kasheshi ya tabe baki yace "lamarin ki akwai ban mamaki, daga ganin mutum saikace ubanku daya, nidai mutafi karki batamin lokaci" wani dadine ya kasheta ta shiga dakin Baaba, kula ta dauko tazo tukunya ganin baba na bayi ta bude dafadukar taliyar hausa ta gani ta deba sanan tarufe suka fito ta ijiye a keke sanan takoma ciki Muji yace "ina kuma zaki" bata bashi amsaba saidai tafito da jarkan ruwa da tsintsiya dawani ledan daki da Baaba tacire dan tasa sabo, dukta saka akeken Muji yabita da kallo, tai murmushi mai karamata kyau tace "muje" kunna keken yayi suka tafi. Ahanya suka tsaya tasaimai bakin takalmi kito size 43, irin takalmin nan damasu noma kesawa inzasu gona wanda yake arufe sanan tasai babbar t-shirt blue suka taho.
Tun kafin suyi parking ta hango shi abola yanata tsintse tsintse, ahankali tafito daga keken bayan sunyi parkin rike da kulan, mahaukacin na hangota yataho da gudu har saida takoma baya da sauri amma ya bita ya fizge kulan hanunta yana dariya, da sauri ta kalli Muji daya bisu da kallo tace "kama gani yaganeni wlh" tabe baki Muji yayi yataya ta daukan jarkan ruwan itakuma ta dauko tsintsiya da leda suka shiga gidan. Yana zaune akasa sai kiciniyar bude kulan yake hakan yasa ta budemai ya fizge da sauri zai saka hannu ta rike hanun nashi gabanta na faduwa tace "tsaya in wanke ma hannun da datti" ta kalli Muji hakan yasa ya tabe baki yakaraso wajen yabude jarkan ya daga itakuma takai hannunshi tana wankewa Muji na zuba musu ruwan sanan ya fizge yahau ci, murmushi tayi tana kallon ciwon kafar nashi sanan ta yayyafa ruwa a wajen tasa tsintsiya tafara shara har takai waje ta shinfida carpet din dayadan yayyage, nan da nan wurin yay kyau, yana gama cin taliyar yayar da kulan da sauri ta mikamai ruwan ya karba yasha sosai yay wata irin katuwar gyatsa, takalmin ta dauko tazo ta gabanshi tana kallon kafarshi daduk yay datti, ruwan tasa ta wawwanke mai kafar yanata kallonta kafin ta saka mishi takalmin aiko yamai daidai, ya mike tsaye yanata tsalle yana kallon takalmin, ta kalli Muji kaman zatai kuka tace "toka sakamai rigar dan Allah" atsorace yace "ni? Ni wlh tsoro nakeji" dariya tai tace "Allah bazai maka komiba baya komi" ta mikamai rigar suka karasa kusada shi tare, ya juyo yana kallonsu duk suka tsaya chak suna kallon juna, daga mai rigar Muji yayi yana juyawa asama hakan yasa yadinga bin rigar da kallo sanan Muji yasa hannu zai ciremai ta jikinshi da sauri ta juya musu baya saida Muji ya ciremai sanan ya samai wacce suka siyo aikuwa tamai daidai, da sauri Muji yace "juyo kigani" murmushi tayi tana dafa Muji tace "laaa ashe na cinka size din daidai" ganin yanda yaketa tsalle yasa muji yace "bari namai hoto" ciro wayarshi yay yadinga daukan shi hoto yanda yaketa tsalle tsalle ya kalli Bilkisun daketa dariya yace "dalla malama mu matsa kusa dashi dukmuyi selfie, selfie da mahaukaci" yay maganan yana dariya yana janta har inda yake ai kuwa mahaukacin na ganinsu ya dena tsallen yana kallonsu duk suka tsaya a gefenshi, Muji ya dau hoton. Tace "zomu tafi to tunda mungama" fita sukayi suka barshi yanata tsalle tsalle.
Chapter 8 · 0% Book details