← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 76 OF 89

Sashe 76

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Yana shiga office din da ake tracking number kira na shigowa wayarshi alamu CP yamai dayay picking hakan yasa yay picking yasaka a handsfree, cikin kakkausar murya Big Mum tace "am not going to repeat myself Ayaan ko abar tracking wayar nan kona harbi baban ka, ka ganni nan gani gashi sai kallona yake yana son yay magana amma na kulle mai baki" tai maganan tana wani irin zagaye Abba tana goga mai bakin bindiga awuya, juya ido tayi tace "au bakaji ba kenan, stop tracking my phone, tusss" Big Mum ta harbi Abba akafan haggu tasa hannu ta tunbuke tsumman da aka kulle bakin Abba dashi, wani irin ihu azaba Abba yayi har cikin zuciyan Ayaan yaji ihun dafe zuciyar shi yayi ya kalli CP amugun rude yace "stop, I said stop tracking d Goddamn number zata kashe min Pops" kafa yasa yawani irin tarwatsa laptops din jikinshi na rawa yana karajin yanda Abba ke ihu, dan kafa Big Mum tasa ta take inda ta harbai sabida yay ihu da kyau Ayaan yaji, Mami kam sumewa tayi ganin yanda big mum ta harbi Alhaji. Wani irin dariya big Mum tayi ta mikama Bala dake kusa da ita bindigar ta zauna akan kujera ta daura kafa daya kan daya tana kallon fuskar Alhaji yanda wahala yau yasa tsufan shi yafito sosai dan da baka wani gani sabida cin dadi dakuma kudi, maganar Ayaan ne ya katse mata tunani, sosai muryan shi ke breaking yace "Big Mum please, please don't kill my Pops, andena tracking din kome kikeso I will do it amma kifara hadani dashi inji muryan shi if he's still alive shida Mami na sabida nayarda baki kashemin su ba, Pops" ya kwalama Abba kira ta wayan arude, Abba da kaman ya suma tsabagen azaba jin muryan Ayaan yasa yadan bude ido yana bin wurin da kallo, wani irin murmushin keta Big Mum tayi ta mikama Bala wayar bayan ta karbi bindigar tace "sashi awaya" karban wayan Bala yayi yawani finciko kan Abba kaman zai karya saida Abba yay Kara ya kara wayan a kunen shi da sauri Ayaan yace "Pops are you okay, zan bata koma me take so am going to save u, Popsy be strong for me okay, Ina mamina, a ina ta har...harbe..k" yakasa karashe maganan sabida kuka jin yanda Abba ke wani irin nishi, kukan shi yasa wani jarumta yazoma Abba yay murmushi yace "is okay my Boy am fine, karka sake kabama makirar nan dukiyata, dakabata dukiyata gwara ka zuba musu petrol ka kona, karka sake ka bata Bilkisu stay with your wife, don't give her anything, dan koka bata kasheka zatayi, da abu yasaman min kai Boy gwara in mutu, idan wanan shine saduwar mu takarshe na yafema kome kamin aduniyar nan, ga Mamin kanan she's unconscious" sosai Ayaan ke kuka ya kankame wayar a kirji yanajin muryan Abba, CP kuma yadauko wani sabon laptop suna kokarin tracking, Bala ne yazo zai fizge wayar Big Mum ta hanashi tana murmushi tace "barsu suna bidding farewell ne shima yasan he's not leaving here alive" wani irin kallon ta Abba yake cike da tsana saikuma yakara wayan abakin shi da wani irin mugun sauri dakuma karfin bala'i yace "Boy muna wani uncompleted buildi...." tus tus Big Mum tamai harbi har biyu akafar daman shi amma dayace ta shige shi, Bala kuma ya zubamai wani irin naushi ahanci dayasa ya sume warwas.
Tashi tsaye Ayaan yayi kaman mahaukaci yana ihu a wayan "Pops Pops Pooooopsss" yawani irin ja sunan kaman wanda ya zare, maganar big Mum yaji ta wayan tace "nabaka 15 minutes take Bilkisu, documents, da yarana zuwa kasuwar kwari wurin yan kaji ka ijiye su anan kajuy.." Ayaan da zuciyar shi kaman tafashe ta fito yamata wani irin ihu a haukace da intonation dinshi daya koma nayan Austria yace "f*ck yhu mah nigga, I said f*ck yhu, f*ck yhu mah nigga, f*ck, f*ck you b*tch, I will kill you, I gonna kill yhu, u kill my pops I will gonna yhu wallah" dip big Mum ta kashe wayan jin yanda ya haukace mata kirjinta na wani irin bugawa, hannu yasa ya fizge bindigar dake cikin jakar bindiga dake jikin CP azuciye yajuya zai fita daga office din rikoshi CP da polisawan sukayi awani irin zuciye ya turesu dukan su suka zube kasa yafita amugun zuciye yana share hawayen dayake yi, su CP suka biyoshi kafin su fito harya bide wajen da kura.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

88...
Chapter 76 · 0% Book details