← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 89

Sashe 2

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaure tawuce tana bin almajiran wajen da kallo kafin ta fita kofar gida tai wajen Baba da tunda tafito ita yake kallo, tsugunnawa tai agabanshi tawani kwaye fuska kaman zatai kuka ahankali tace "Baba natafi makaranta amma ni banci komiba ba'a gama abincin ranaba" girgiza kai kawai Malam yayi sanin halin yar tashi, hakan yasa ya saka hannu cikin aljihun babbar rigar dake jikinshi yaciro dari yabata da sauri ta karba tana murmushi tace "nagode Babana, Allah biyaka natafi" "ya cikin?" ya tambayeta anatse, tashi tayi tana kokarin saka kudin ajaka sanan tace "yadena Baba tundazu, natafi" "adawo lpy" tajuya ta fita tana waige waigen zauren, fitowa tayi tafara tafiya a layinsu daya yawaitu da bishiyoyin dogon yaro, dadan sauri take tafiya sabida takai bakin titi tahau boss dazai kaita school, wani gida dan madaidaici dake nan cikin layinsu ta shiga harda dan gudan ta dan sauri take wata matace yar dattijuwa haka, tana zaune tana tuyan waina anan tsakar gidan ahankali kaman wacce kwai ya fashewa aciki ta karasa kusa da matar wacce batama lura da itaba saidai kawai taji mutum akanta, fashewa tayi da kuka kaman wacce aka doka hakan yasa matar ta rike baki tace "mekuma aka miki iya shagwaba iya sonjiki Bilkisu" kara fashewa tai da kuka tana buga kafa akasa cikin kukan tace "tun safe banda lpy kokizo ki dubani kinata wainar saidawa abinki ko Baaba" arude matar tace "ni? Haba tagidana ai kema kinsan inda nasan bakida lpy tuni xan ijiye wainar nan nazo, dena kukan keko, halan cikin ne yatashi?" gyada kai tayi tana share hawayen Baaba tace "shiga daki ki dauko kular ki nasaka miki wainar ki kitafi kinga yau kinyi latti" da sauri tashiga dakin Baaba tana kokarin daukar kulan tace "Baaba ina Muji?" daga tachan waje Baaba tace "yafita da Keke napep waiko zai sami fasinja, saiyau ya daukota daga gareji" daidai nan tafito tamika ma Baaba kular, karba tayi tazuba mata wainar dayawa sanan ta baza mata kuli dayawa akai ta rufe kulan tabata tareda ciro hamsin tace "gashi adawo lpy" karba kulan tayi tace "kibar kudin Baba yabani, natafi Baaba saina dawo" "adawo lpy yar albarka banda wasa a aji kinji yar gidana" fita tayi tana murmushi tana mugun son Baaba, yayar mamanta ne haka suke kiranta, bayan tai aure data haifi Mujittapa (Mustapha) danta na farko shine Maman su lokacin kafin tai aure tazo tayata raino aiko malam yana ganin Maman su ya like mata ya nace yanaso, bayan wani dan lokaci fa suka tafi kauyen su dake chan hanyar gombe kauyen bojude lokacin tun kafin iyayensu su rasu akai bikin aka kawota gidan malam, Umma bata da matsala hakan yasa malam ya hade kansu suna zaman lpy, yayan malam 8, Umma yaranta 5 duka maza wanda duk malam yatura su nijar wajen wani babban abokin shi malami yin karatun addini awani babbar makarantar shi, yanzu ma watan su daya da tafiya kenan sai bayan shekara biyar zasu dawo dan makarantar har certificate ake badawa inka gama, sai kuma maman su data haifi su uku Balkisu, Raiyana da Layla, dukan su malam yasasu a government girls secondary school ne Raiyana da Layla na safe suke zuwa, itakuma dayake SS ne rana ne nata.

Karasowa bakin titi tayi ta tsaya tana jiran Bus wata makauniya tagani ita da yarta suna ta bara a shagunonin kan hanya wai tun safe basuci abinci ba, ba karamin tausayi suka bataba, tana kallonsu suka koma kan dakali suka zauna yarinyar nata kuka, jakarta ta laluba taciro naira darin da Baba yabata ta karasa kan dakalin dataga sun zauna, yarinyar nata kuka wai yunwa takeji maman na lallashin ta, ahankali ta duka darin ta mikama yarinyar tareda mata murmushi tace "dena kuka gashi" karba yarinyar tayi tana fadama maman ta bakaramin dadi matar tajiba tace "mungode yar nan, ubangiji Allah ya miki albarka ya raya miki yaranki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "Ameen amma nibanyi aure ba mama" washe baki makauniyar tayi tace "to ubangiji Allah ya baki miji nagari wanda zai saki farin ciki sama da wanan dakika samu" ahankali tace "Ameen nagode" ta dagama karamar yarinyar hannu sanan tajuya ta tare bus din dake zuwa ta shiga har lokacin yarinyar nata dagamata hannu itama daga mata hannun tayi har bus yawuce ta daina hangosu.
Allah yasota koda ta shiga school ana gab dafara taran latti, da sauri tafara yin masallaci tai salla sanan tafito tai aji lokacin duk yan aji sun zauna ana ganinta akai tsit kowa nata kallonta hakan yasa tasha jinin jikinta, kujeran layi nabiyu ta wuce ta tsaya agaban sit din ganin duk su Aisha Shehu sun cike Walawa ta zauna awurinta, daure fuska tayi ta kalli Walawa tace "wlh kitashin min daga wuri ai chan ne sit dinki" tanuna kujeran bayan nasu, hararan ta Walawa tayi ta cigaba da zanen flower datake yi a paper, su Aisha Shehu dai sai dariya suke kasa kasa dan dama dagangan Walawa tazauna neman tsokana ne, ganin ko kulata Walawa batayi ba yasa taji abin ya mugun bata mata rai hakan yasa ta fizge byron hanun Walawa afadace tace "badake nake magana ba, kinga kitashi" kaman jira Walawa takeyi ta mike tsaye fuska a daure ta kalli su Fateema da Fa'za dake kusa da ita suma duk suna dariya kasa kasa tace "ku matsamin na fitan ma almasifatu daga wuri" gyaggyara kafa sukayi Walawa tafara tafiya hakan yasa Bilkisu tazo daidai bakin sit din tana jiran Walawa tafito itakuma ta shiga fuskar nan nata adaure fitowa Walawa tayi, saida tazo gab da Bilkisu tasa hannu ta taba mata nono, atsorace Bilkisu ta tsugunna a wurin tareda fasa ihu "wayyo Allah" ta kankame jikinta, aiko duka ajin sukahau ihu da dariya, su Aisha Shehu dasu Fa'iza harda buga benci suna dariya, Walawa ko hanyar kofa tayi ta tsugunna tana dariya harda rike ciki, gabaki daya ajin dariya ake Aisha Shehu tace "babu wacce ba'a tabama nono a ajinan ba, kece kullum kiki yarda yar malam, yaudai an taba dama gasu manya manya" aikuwa kowa dariya suna bubbuga benci irin abun yay musu mugun sugar dinan, saida ta goge hawayen datake yi sanan ta mike tazo gaban Aisha Shehu tace "eh aini kinsan ba yar iska bace irinku ba masu wasan taba nono a school" tana fadin haka tai hanyar kofa wurin Walawa, Aisha Shehu tabita da harara tace "to uban waye yan iskan, ba wasa bane kowa ajin nan an taba nashi saike, koba hakabane?" ta tambayi su Fa'iza da Fateema suma duk dariyan suke harda kama ciki danba karamin dadi abun yamusu ba yau yanda aka kama na Bilkisu yar malam yau, dan ita kadaice bata yarda amata wanan iskancin a aji gashi yau an shammaceta anyi kowa dadi yakeji. Kan Walawa Bilkisu tayi wacce tun kafin tazo kanta tahade hannu tana dariya tace "haba Billy yar malam, yakuri mana kawas ai bankama ba tabawa kawai nayifa dan nasan bakiso wlh bazan karaba, yakuri" kamota Bilkisu tayi ta durma mata duddu abaya daidai lokacin wata malamar english dinsu ta shigo aji hakan yasa duk suka koma wajen zamansu kowa ya natsu.
(oya name abunda kukayi zamanin secondary school?? Barinma wayanda sukayi girls school kadai😂)

Wuraren 4 suka fito break da salla, bayan sunyi salla duk tare suka tayata cin wainar dan dama sune kawayen nata Aisha Shehu Walawa da Fa'ixa saikuma Fateema, bayan sungama ciyeciyen su sanan suka koma class, sai wuraren biyar da rabi aka tashe su duk suka fito suna tafiya har suka gangaro bakin titi suka shiga bus kowacce tai gidansu.
Gidan Umma tafara biyawa ta ijiye kulan sanan tafito akofar gidansu tahadu da Isyaka yana alwalan sallan magriba, murmushi tamai hakan shima yamata murmushi da sauri ta shiga gida ta gaida Baba sanan tawuce cikin gida. Babu kowa a tsakar gidan duk sun shiga daki hakan yasa taja ruwa tazuba a buta tai bayin su bayan tafito ta tsugunna a makwarara tai alwala sanan ta shigo dakinsu, salla taga Mama dasu Raiyana nayi hakan yasa ta zauna akan kujera tana kokarin kunna fitila, kunnawa tayi ta ijiye daidai lokacin sun sallame Layla ce tafara tasowa Raiyana tabiyo ta abaya duk suka zauna kusa da ita Layla tace "me kika kawo mana daga school Anty Baby?" murmushi tayi ta bude jakarta gwaiba taciro da topi ta basu duk suka karba cikeda jin dadi Mama ta ballamata harara tace "aikin kenan" dariya tayi ta tashi tasaka hijabi tai sallan magriba tana idarwa ta daura kanta akan cinyar Mama ahankali tace "yunwa nakeji Mama sosai" mika hannu Mama tayi ta dauko kular tuwo dake gefenta tace "gashi nan zuba muku kuci keda kaninki to" tashi tayi ta dauko faranti ta zuba tuwon tasa miya asama ta kalli su Raiyana tace "ku sakko muci" sakkowa sukayi zasu sa hannu Mama ta harareta tace "bazaki je kicire kayan makaranta bawai" kaman zatai kuka ta tashi tawuce uwar daka tacire kayan ta fito daure da zani akirji ta zauna tana turo baki sanan suka saka hannu duka suka faraci.
Chapter 2 · 0% Book details