← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 89

Sashe 56

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Yauma kaman kullum karfe biyar na asuba ta farka sabida wani shegen ciwon ciki daya tada ta, da kuka ta tashi hakan yasa Ummy dake kusa da ita ta farka daga baccin datake dafata tayi da sauri ta ture mata hannu tana murguda mata baki dariya Ummy taso tayi amma saita gimtse inda sabo yanzu ai tasaba Ya Aaman ne kawai bata murguda ma baki amma kowa kam shan murgudan baki yake, tashin datayi ne yasa taga blood akan gado da sauri tace "ina zaki Ameerah" juyowa tayi tana share kwalla tace "Uncle" dirowa Ummy tayi daga gadon da sauri ta kulle kofar tace "haba my sweet sis muje kifara yin wanka zan baki maganin ciwon cikin zai dena mp kikeyi" da sauri tace "mp?" "eh mp amma karki fadama Uncle fa, muje kiga nahada miki ruwan wanka" saida tasake murguda mata baki sanan tai gaba suka shiga bayin tana hada mata ruwa tafito ta cire zanin gadon ta shimfida wani sanan ta fito mata da kayan dazata saka dakuma magani, fita kitchen tayi dan hado mata tea suka hadu da Ya Aaman yana shirin zuwa masallaci sanye da farar jallabiya kafin ma ta gaishe shi ya jefo mata tambaya. "kin tashe Ameerah tai salla?" "eh yayan mu natashe ta, good morning" juyawa yayi yay hanyar fita sanan ya amsa da "morning" ya sakai yafice.
Wuraren 8 ya shigo gidan dan yabiya gidan kajin su dubusu, yana shigowa tafito daga dakin nasu da gudu tana sanye da bakin riga abaya mai stones kanta har yanzu kitso biyu ne akanta sabida bandejin da aka sa har yanzu ba'a cireba, jiki asanyaye ta fito tazo ta xauna kusa dashi ba kaman kullum data saba zuwa dazaran yadawo daga masallaci da gudu ba, hakan yasa yadan kalleta yana kokarin ciro wayar shi daga aljihun jallabiya, kaman zatai kuka ta lankwasa kai ta kalleshi tace "good morning uncle" shima kallon fuskarta yayi nayan sakanni kafin ya dauke kai ahankali yace "baki da lafiya ne u look somehow" kaman jira take tafashe da kuka daidai nan Ummy tafito daga kitchen dauke da tray data daura cups din tea akai sakin baki tayi tana kallonta tace "kedai Ameerah kinada kukan banza" hararan ta tayi kaman idanunta zasu fadi kasa ta kalli Aaman da tunda tafara hararan ta yake kallon manyan idanuwanta yanda suke sama da kasa tace "Uncle Ummy is looking for my trouble" dan murmushi yayi yace "bakin riga kin harare taba to" wani irin ihu tayi ta mike tsaye tai dakinsu tana kuka dudda uban kiran da Ummy kemata ko juyowa batayi ba, hannu ya mika yadau coffee da Ummy tahada mai yakai baki saikuma yakasa sha sabida yanda kukan ta ke tabamai rai ya kalli Ummy daketa kallonshi tana murmushi yace "me kika mata take rigima yau?" "wlh Ya Aaman babu abinda na mata" shiru yayi kafin ya ijiye coffee yadau tea dinta da chips yay hanyar dakin nasu ahankali ya bude kofar ya shiga tana kwance ta kifa kanta a pilo tana kuka, ajiye tea da abinci yayi ya zauna a gefen gadon yay dan murmushi yace "Ameerah" make mai kafada tayi tace "oh'oh" tai maganan tana dan juyowa tana lekoshi, folding hanunshi yayi a kirji ya daure fuska yace "why are you crying" lankwashe kai tayi ta nunamai kofa tace "Ummy" ahankali yace "okay to sorry tashi kiyi breakfast" tashi tayi ta zauna tana goge kwalla ya juya zai fita da sauri ta riko hanunshi hararan ta yayi. "bana hanaki tabani ba" turomai baki tayi tace "sit down" ahankali ya zauna abakin gadon dan nesa da ita da sauri ta matso kusa dashi tana leka fuskar shi ta washe baki tace "Uncle daga yau i will be calling you sweetheart" da sauri ya kalleta sake washemai baki tayi tace "kaga ko Ummy na kiran saurayin ta sweetheart" yadade yana kallon fuskar ta kafin yace "to ni saurayin kine dazaki kirani da sweetheart" da sauri ta gyadamai kai tace "eh kai saurayi nane Sweetheart" tai maganan harda wuntsula kafa tana murna sanan tadau chips dinta ta daura akan cinya tasa fork ta debo takai bakinshi tace "haa sweetheart" dan hararan ta yayi kafin ya mike tsaye yafita daga dakin wani irin tsalle tayi tana rawa adakin. "yeeeee uncle is my sweetheart"
Afalo yasami Ummy harta gama chan tea wani irin kallo yamata ya daura kafa daya kan daya yadau coffee shi sanan yace "wato soyayya kike koyama Ameerah ko?" ware ido tayi tace "laaa haka tacema" saikuma tai murmushi ganin shan coffee shi yake hankali kwance, ahankali tace "Ya Aaman nidai wlh inason ka da yarinyar, she's very pretty and lovely, kaga dama Abba nata damunka kafito da mata why don't you go for her" yakai kusan 5min maganar na waka aranshi harta cire rai dazai amsata saikuma yace "I wouldn't risk dat, yarinyar datai loosing memory saina fara soyayya da ita, wat if tanada wanda takeso kafin abinan yasame ta, karma ki kara irin maganan nan" kaman daga sama yaji tace "amma ai kana sonta" da sauri ya kalleta ya nuna kanshi yace "nina cemiki ina sonta" yanayin yanda yake kallonta ne yasa taji wani irin tsoranshi ya shigeta bakinta har rawa yake tace "dama dama naga ka taimake ta ne, kuma yanzun nan datake kuka ka kasa cin abinci saida kaje ka lallaso ta and a whole lot of things danake ta noticing dis past few days" yadade yana kallonta yana karkada kafa idanunshi har sun dan soma chanza kala har yabude baki zaiyi magana Bilkisu tafito da gudun ta tazo ta zauna kusa dashi tana murmushi tace "sweetheart i want teddy" ko kallonta baiyi ba yace "stop calling me sweetheart" make mai kafada tayi tace "ni u are my sweetheart ko Anty Ummy" sumsum Ummy ta mike tabar falon kafin tasata abala'i, Bilkisu tabita da kallo sanan ta juyo ta kalleshi hada ido sukayi dan ita yake kallo yanason yagano me Ummy tagani harta ce yana sonta, washemai baki tayi tace "sweetheart teddy bear" kaman ba zaiyi magana ba saikuma yace "i want to sleep now anjima zamuje musiyo" tashi tayi tana murna tace "yeeeee" tai dakinsu da gudu da sauri ya runtse ido yana dafe kai ahankali yace "please please don't do dis to me, tayaya zanso wacce bansan ko waccece ba, tayaya zanso wacce ita karan kanta batasan kanta ba" ahankali ya ijiye cup din coffee a wurin yatashi ya shiga dakinshi.

Bayan kwana hudu.
Chapter 56 · 0% Book details