← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 89

Sashe 37

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 9 min read

Zaune take yau lahadi adakinta ita kadai tana gyaran kumba da nail cutter, tun asuba takejin tashin music daga dakinshi tanata mamaki wanan wani irin mutumne, tana sanye cikin doguwar rigar atampa na poker dot blak da pink, straight gown akamata dashi akasa aljihu agefen rigar, sai kamshin turaren da Mami tahada mata takeyi, kanta ba dankwali tadaiyi parking gashinta ta kitse bakin daya sakko har bayanta takama jelar bakin da hair clip pink, wayarta ne yay ringing da sauri ta dauka ganin Mami ce bakaramin kewanta tayiba ahankali tace "ina yini Mami" daga dayan bangaren Mami ta amsa tareda tambayar lafiyanta sanan tace "tun dazu nake kiran Ayaan awaya amma number shi akashe ki kaimai wayarki zan kira nan bada jimawa ba" ahankali tace "to Mami" gabanta na faduwa kafin ta mike tsaye tabude kofar tafita daga dakinta rike da wayar, tsayawa tai abakin kofarshi tana sallama amma babu amsa, to ta inama zaiji wanan uban speaker dake tashi haka na waka, ahankali ta bude kofar dakin batare data shigaba wani sassanyar kamshi da sanyin Ac ne yamata sallama baki tabude cike da mamaki yanda taga ya tsaya gaban tv dakin ga home theater agefe yana tika uban rawa hanunshi rike da glasscup dake dauke da juice aciki, dagashi sai dogon wandon crazy jean daya zazzago kasa da belt ke jiki, babu riga ajikinshi ga jikin nan amumurde sai kace wani commando, rawa yake yanabin wakan dake tashi na Burnaby da zlatan gbese yana irin rawan, dayake yajuya mata baya saisa baigantaba baki abude take kallonshi dan tunda take a duniyar nan bata taba ganin namiji na rawaba to a inama zata gani makarantar datayi mata zalla ne, ganin yanda yake chashewa abinshi yanayi yana shan juice din hanunshi yasa ta daura hannu akan baki tareda sake kwalalo ido dan dariya ke cinta ganin abun bambaram, kaman ance yajuyo ya juyo cikin rawa karaf suka hada idanu ko kulle belt din wandon baiyiba kunen nan makale cikin daimond dankunne sai shining suke, ga wata sarka a wuyarshi dake kyallin bala'i, kirjinnan kaman zai rabe biyu tsabagen yanda yaciko, numfashin ta yakusa daukewa sabida yanda suka hada ido ta juya da gudu zatabar wajen ya dakamata tsawa. "ke come back here" juyowa tayi amma takasa shigowa sabida yanda taga babu alamun rahama akan fuskarshi, wani irin kallon daya mata yasa ta shiga ciki da sauri tazo gabanshi ta tsaya kanta akasa tana kakkama rigarta tsabagen yanda tarude. "uban me kikeyi anan?" yamata tambayan dawani irin murya dayasa taji cikinta zai fara murdawa, girgiza kai tayi ta mikamai wayarta tana kokarin hadiye kukan datake ji tace "Mami tace nakawo ma wayar wai zata kiraka" wayar ya kalla kafin ya watsa mata harara ya nunamata gaban tv stand yace "keep it there" da sauri ta ijiye wayar jikinta har rawa yake tajuya zata tafi taji yariko hanunta fashewa tai da kukan datake kokarin hadiye wa ta juyo atsorace cikin kuka tace "to menayi kuma" hadata yay da jikinshi ya watsa mata harara kafin ya daura hannunshi akan lips dinta alamun tamai shiru hadiye kukan tai da kyar ta share fuskar tass sanan ya saketa yabarta anan tsakar dakin yadau remote yadawo kan kujera yadaura kafa daya kan daya ya chanza waka zuwa wakar Mayorkun da kizz Daniel True ya daure fuska ya kalleta yace "dance" atsorace ta ware ido ta kallai ganin yanda yay da fuska yasa ahankali muryan ta har rawa yake tace "wlh ban iya rawaba" belt din dake jikin wandon shi yafara zarowa yace "kokiyi rawa ko kici dukan bala'i" yanuna mata belt din tare kara maida wakar tafara daga farko yakara volume dakin sai daukar duma yake shikuma yana kurban juice dinshi hankali kwance yana dan kada kafa, kaman zatai kuka ta daura hannu takama kwankwason ta sanan tadaura yatsu biyu agaban goshin ta tafara mai rawan yan fillo tana moving jikinta ahankali hawaye na zuba.
Wani irin kallo yake binda dashi yanda take wining tiny waist dinta, tun yana murmushin gefen baki har yay dariya daya bayyana duka fararen hakoran shi, ajiye glasscup din yayi akan hannun kujeran yataso rike da remote cikin murmushin dabaima san yanayi ba ya jawota jikinshi ya rungumeta tareda duko dakai ya daura kanshi akan gashin ta yana murmushi still ganin yanda take kuka ajikinshi, ahankali yace "you don't know how to dance bari na koyamiki" chanza wakar yay yasaka wakar ed sheeran perfect wakar soyayya ce, ahankali ya cirota daga jikinshi yana murmushi ganin yanda duk ta tsure yawani irin juyata kafin ya kwanto da bayanta jikinshi ya hade hannayensu ya budesu, sanan ya saketa ya juyo da ita tareda saka hannayenta akan wuyanshi ya daura hannayen shi a waist dinta yana wani irin tafiya da ita ahaka, ita wlh tsoro ma yake bata nishi kawai take tana ganin yanda yakebin wakar yana wani jujjuyata kaman yasami yar tsana, jin fuskarshi a wurin wuyarta yasa ta bude idanun data lumshe da sauri daukarta yay yawani shillarata sama kafin ya cabeta asaman yafara juya da ita sosai tafara ganin jiri hakan yasa ta rirrike jikinta ta dafe hannayenshi, sakinta yay kaman zata fadi hartai ihu saikuma yarike ta suka zuba akan center carpet din dake kasan dakin yana dan dariya, ringing da wayarta yayi yasa yatashi ya dauka tareda kashe wakar ganin Mami ce yay picking call din yana gaisheta, tashi tayi dudda uban jirin datake gani tazo zata tsallake kafarshi ta fita daga dakin taji yarike hanunta juyowa tayi ta kallai hada ido sukayi ya daga mata gira daya kafin yacigaba da wayarshi abinshi, dayan hannunta tadaura akan hanunshi tana kokarin bambare hanun kawai ya fizgota tafada kanshi matseta yay sosai ko numfashin kirki bata iyayi hakan yasa tai lamo hawayen wahala na zubo mata. Yana magana da Mami anatse ahankali, kadan kadan ma takeji meyake fadama Mami ahaka har bacci baccin wahala yasoma dibanta tana takure ajikinshi, "ke" tsawan dataji yay mata yasa tafarka afirgice tana neman sauka daga jikinshi amma baibata daman ba saima kara manneta da jikinshi dayay da kyau yana kallon fuskar nata. Tashi yay zaune har lokacin tana jikinshi tana sossosa ido da yatsa sabida gashin idon daya shigan mata, hannunta daya kama yacire daga idon yasa ta kallai da idanun dasuka kankance shima ita yake kallo hakan yasa ta janye idanunta ta sauke su kasa, tashi tsaye yay rike da ita kafin yadauke ta chak da sauri ta kallai itama shiyake kallo, jikinta na rawa ahaka har suka fito yasauka downstairs kitchen taga sun shiga saikuma ya bude kofar baya sai gasu a garden wurgata cikin swimming pool din da bama ta lura dashi ba yayi kawai, wani irin ihu tayi kanta na shigewa cikin ruwan tana kara fitowa tana mikamai hannu, dan dariya yay yajuya yakoma kitchen din ko 1min baiyiba yafito dauke da glasscup da yazuba non alcoholic wine aciki ya dawo bakin swimming pool din ya zauna tareda da saka kafafun shi aciki yana kallon yanda take dambe da ruwa ga gashinta dukya barbaje acikin ruwan, sipping wine dinshi yayi kafin ya ijiye ya dira cikin ruwan yay swimming zuwa inda take tareda cirota yafito da kanta amma jikinta naciki kaman yanda nashi ke cikin ruwan, fashewa tai da kuka sosai tana tarin dan ruwan data sha saida tagama tarin sanan ya rungumota ahankali yana tafiya da ita acikin pool din har zuwa bakin pool din batare daya bari tai tafiya ba ya mannata ajikin bangon yana kallon fuskarta yanda hancinta ke digo da ruwa yana zuba a lips dinta, ga yanda gashin ta ke tsiyayo da ruwa yanabin fatarta yana gangarawa zuwa kirjinta, ahankali ya matso tana matsawa ya matso tana matsawa har yawani irin danneta ajikin bangon pool din ya mika hannu ya dauko cold wine dinshi daya zuba a glasscup yadawo yadan rage danneta dayayi ganin zata sume yakai wine din bakinshi yana kallon fuskarta yanda dukta rude tama rasa inda zatasa kanta sai kalle kallen gefenta takeyi, sipping wine din yayi yacire daga bakinshi ya kara akan bakinta yana mata wani irin mugun kallo, ahankali ta bude baki tadansha kadan sabida sanyin shi dataji kaman kankara cire bakinta tayi ta kawad dakai nan da nan tafara rawan sanyi da sauri ta juya zata fita daga ruwan yawani jawo waist dinta da kakkausar murya yace "nagama dakene" labbanta har rawa suke sabida yanda ruwan taji yanamata ajiki kaman kankara tace "sas.. Sanyi nikeji" ta fizge jikinta tabi matattakalan tafita da sauri, "kikito" taji ya kwala kira wanan sunan da batasan nawaye ba tana fita daga pool din, kaman daga sama taga monkey yay wani tsalle daga saman bishiyar lemu dake garden din yawani dirko yana tsalle yay swimming pool din, "get her for me my kyky" harta saka hannu zata bude kofar kitchen din tashiga sabida yanda take rawan sanyi kawai taga biri yay wani tsalle yayo kanta, ihu tayi kafin ma tagama rufe baki yay wani irin tsalle yahau kan jikinta yanajan rigarta.
Murmushi yay har lokacin yana cikin ruwan hanunshi dauke da wine yana sipping abinshi kana ganinshi kasan yana cikin nishadi. Ihu tacigaba dayi, birin ko daga yay tsalle ya chapke nan arigarta sai yay tsalle ya chake chan arigarta yanda kukasan ya sami bishiya, ita fuskar birin kadai ma firgitata yake ballema gabaki dayan shi ajikin ta, ganin sai sama yake yowa tana kuka tana yarfe hannu yaki sakin ta yasa tai jarumtar tai baya da sauri dukta haukace. "ya Ayaan dan Allah kace yarubu dani" tai maganan tana kuka, tsallen da birin yay ya makale abayanta yasaka fuskarshi a wuyanta yana wani irin kuka kukan su na birai yasa tawani irin fadi arude amma dan iskan birin bai saketa ba saima tattaka hanunta dayake yi yana neman yadawo ta gaban kirjinta. "banison na chasa ki dakaina ne saisa nasa kikito yatayani, walkout of me again kiga abinda zan miki, kyky let go off her" da sauri monkey ya sauka daga kanta yadawo wajen shi da gudu, shafa kanshi yayi yana murmushi yana dan satan kallonta kafin yace "go to ur cage" da gudu money na tsalle yabar wajen, ya kalleta tareda daure fuska yace "zonan" tashi tayi tana kuka sosai tashiga pool din tareda runtse ido sabida sanyin datake ji hannu yasa ya jawota tareda matseta ajikin bango da lazy eyes dinshi ya kalleta yace "ke kimin shiru" ko tari bata karaba kanshi ya daura akan kafadarta yana sipping matsiyacin wine din dayake ma shan iskanci sipping daya ya ijiye, ahankali yake shafa bayanta har zuwa waist dinta, hada hannayenshi biyu yay a waist din kaman yana auna abu saikuma ya dauke hanunshi daga wurin ya komar dashi shoulder dinta bakinshi yakai saitin kunenta murya chan ciki yace "how old are you?" kasa magana tayi tsabagen yanda sanyi keshiga cikin kashinta kwankwasa ma kasusuwan ta keyi kuma yanaji ya share, maida hanun yay kan waist din yawani juyo da ita tareda manna bayanta a kirjinshi yasake daura kanshi akafadar ta ya kulle hanunshi tagaban cikin ta yace "i said how old are you" da dishashiyar muryarta tace "18" dan murmushin gefen baki yay kafin yaja gajeren saki har lokacin kanshi nakan kafadarta yana wani irin shinshina wuyarta yace "tausayin Abban ki naji nataima ka na aureki dakikai kwantai almajirin nan yace bayason ki, inba hakaba mezanyi dake kimin karanta mexaki iya bani, kawai dan kar hawan jini yakama Abban kine amma ko kadan banason ki" duka maganar nan yayine chan kasan makoshi yana wani shinshinshina wuyarta, wani irin zafaffun hawaye ne suka zubomata masu dumi muryarta narawa tace "nima bana sonka Isyaka na nakeso".
[7/21, 9:24 AM] +234 706 571 7620: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦
Chapter 37 · 0% Book details