← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 89

Sashe 65

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana zaune akan hadadden center carpet din falon tajawo ledan daya kawo dazu da rana chocolate din da tagani na cabry dairy milk tadauka tana fama da budewa takasa, bude kofan da akayi yasa ta mike tsaye da sauri dan tabama koma waye ya shigo yabude mata, ido da ido sukai da big Mummy data shigo rike da food flask da warmer tawani irin kafeta da ido tana kallonta tun daga sama har katsa, itama kafe Big Mummy tayi da ido kanta nadan juyawa, mayar da kofan Big Mummy tayi tarufe sanan ta tako kafa ahankali tana mata wani irin kallo tana takowa, tana shigowa tsakiyar falon ta ijiye food flask din akan kujera, sanan ta dago kai ta kalleta itama har lokacin ita take kallo kanta nadan juyawa fuskar matar nasata jin wani iri iri data rasa name ba, ahankali Big Mum ke takowa tana dumfaro inda take atsaye tana mata wani irin kallo, samun kanta tayi dayin baya, baya, takasa janye idanunta daga kan Big Mum kanta nawani irin juyawa tana ganin fuskar big mum yana kuma bace mata, jinta tayi ajikin bango kafin tayi yunkurin motsawa Big Mum ta tareta da hannayen ta, ta hanyar sakata a tsakiyar hannayen ta data daura akan bango tana wani irin zaro mata ido, wani irin yamutse fuska tayi ta kudundune hancin ta tana zobaro baki kaman Doddannuwa danta tsorata ta, da sauri ta runtse idonta kanta nawani irin zafi kaman ana ta fasa ruwa, dan harwani kara takeji daga kanta zuwa kunenta na shuuuuuu, cikin kakausar murya Big Mum tace "bude idonki shegiya yar matsiyata dake nufina da tsiya, bude nace, bude idonki!" ta dakamata wani irin tsawa tareda buga bangon datake manne ajiki, afirgice ta bude ido tana wani irin nishi, tsabagen tsorata saitaga fuskar Big Mum na rikide mata, gawasu irin maganganun datake ji daga kanta dake mugun vibrating, fincikar hanunta Big Mum tayi kaman zata cire su daga jikinta tsabagen yanda kanta ke juya mata tana ganin flash din fuskar Big Mum yana kuma bacewa yasa tama kasa ihu, murde duka hannayen ta Mum tayi tabaya hakan yasa tasaki wani irin kara tace "was..." finciko ta Mum tayi tana wani irin yimata abu kaman dodo da fuska tace "kalleni da kyau inda ace nasan su Bala bazasu kashemin ke da wlh ninai da kaina, amma listen to me, dudda kinyi losing memory ban yarda ba, inhar kika sake kika tonamin asiri wlh saina" hanunta ta daura akan wuyarta ta zagaye, arude take kallonta jikinta nawani irin rawa, wani irin kallo Big Mum tasake mata tace "nida nake tsananin farin ciki burina yakusa cika, ko bayan tafiyar ku bansamu ankamomin shi yamini signing papers din bane sabida kullum ubanshi da uwar shi natare dashi" janye hannunta tayi daga wuyanta ta fizgo gaban rigarta luuu tataho tana kukkule ido tsabagen yanda kanta ke juyawa, ganin haka yasa Big Mum tawani irin jijjigata ahankali ta ware idon tadaura akan Big Mum, dafe kanta tayi dake wani irin juya mata kaman amadubi saita fara ganin kanta awani bene tana sanye da hijab tana gudu saitai buge da kujera tafadi, saikuma taga fuskar matar nan data riketa, wani irin zubewa tayi akasa wajen asandare ta suma tsabagen yanda kanta kemata wani irin juyi. Tsayawa Big Mum tayi tana kallonta yanda ko numfashin kirki bata fitarwa, da sauri ta juya tabude kofa tafita daga dakin, leka ko ina tayi ganin babu kowa ashashin yasa ta sauke ajiyar zuciya tadawo dakin ta tsaya akanta tana tunane tunane, yanzu idan takashe ta ai koda, dat is idan ma za'a tambayan ta kenan, zata iya cewa tana zuwa ta dubata saita tafi shashin ta sabida taje tahuta itama daga biki take, hakan ma yafi this is the best chance na aikata barzahu datake dashi before tai running plan dinta, duk wanda zai shigo tsakanin ta da dukiyoyin nan da kamfanonin Alhaji wlh bazata mai raiba.

Gama zancen zucinta keda wuya tadau daya daga cikin manya manyan filolin jikin hadaddun kujerun falon tayo kanta, ahankali ta tsugunna ta daura guiwowin ta akasa tadaura filon asaman fuskarta ta danne da karfin bala'in, rashin samin iskan numfashi cikin Suman datake yasa tafara shure shure tana shushure kafa tana dukan filon da hannu, Big Mummy takara danne filon tace "die, die yar matsiyata, ki mutu dan ubanki malam, mayyar yarinya ke kikajama kanki...."

Parking yayi yafito daga motar shi rike da IPhone dinshi, dayan hanun kuma rike da ledan shoprite da abubuwa ke ciki, direct bangaren shi yayi sabida yanda zuciyar shi taki natsuwa sai kawomai Bilkisu take, da dan saurin shi yay ciki as usual yasa hannu ya bude kofar ya shiga, dayake kofar irin wacce bata karan nanne, chak ya tsaya zuciyar shi naneman ta buga gabaki daya..
Big Mum da bama taji alamun bude kofaba dan tabama kofa baya sai kara danne filon Bilkisu na shure shure, tana kara dannawa tana "die, die yar matsiyata" kaman daga sama taji wani irin azababben tsawan da tunda take arayuwanta bata tabajin irinshi ba, jitayi kaman muryoyi mutum ishirin ne suka hadu suka mata tsawan. "B..Big..Big Mum!" awani irin firgice ta mike tsaye idanunta acikin na Ayaan daya rikide yakoma kaman na zaki.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

78 - 79

Da mugun sauri ya shigo dakin ya kasa dauke idanunshi daga kan Big Mum data fashe dawani irin kuka tana shafa fuskarta da kanta kaman mahaukaciya, daidai lokacin Mami ta bude kofar ta shigo rike da bowl din wani farfesun Ganda na magani data hadama Bilkisu, da sauri ya janye katon filon daga kanta, gatanan kaman bata numfashi ya daurata akan kafarshi, bowl din hanunta Mami ne tasaki a kasa tsabagen yanda kirjinta ya buga takaraso cikin dakin da mugun gudu ta tsugunna kusa da Ayaan tana kallon Bilkisu tace "maiya sameta Ayaan naga bata numfashi" hannunshi biyu ya daura akan kirjinta yana dannawa da karfi, cikin tsananin fushi ya kalli Mami da jajayen idanunshi yace "ask her" ya nuna mata big Mum dake kuka sosai, bakinta ya bude ya zubama iska sanan yakara danna kirjinta, mikewa Mami tayi ta kalli Big Mum tace "mekika mata hajiya tadena numfashi?" cikin kuka sosai Big Mum tace "Firdausi kinsan ko dazu adakin ki nakusa faduwa ko kekika taroni, aljanu suka shigeni agidan biki, dazuma agidan biki akace mini na shake wata nakusa kasheta, inaga abinda yasame ni kenan yanzu, oh Allah nagode maka daka turo Ayaan dawuri wlh muryan shi yadawo dani hayyaci na, ko dazu yan gidan biki malami sukace sun kiramin, Firdausi na shiga uku mena dawo haka, ku taimaka mini dan ya rasulllahi, Aljanu ke damuna" wani irin kallo Ayaan ke binta dashi, Mami kam kusan mutuwan tsaye tayi itama kallon hajiyar take, ahankali yace "Mami taimaka mata tatafi shashin ta, Allah sawake" kallonshi Mami tayi ya dauke kai yacigaba da danne heart dinta da haryanzu baya feeling beat dinshi, tashi yayi ya dauketa chak ajikinshi yazo zai wucesu, kafadar shi Mami tarike batare data kirashi ba, dan lumshe ido yayi yabude yana kokarin saita kanshi ahankali batare daya juyoba yace "Mami ki kaita ta chanza kaya tahuta, ku kira malami yamata rukiya" yajuya yafita daga dakin azuciye.
Mami ma saida ta saita fuskarta sanan ta juyo ta kakalo murmushi tace "muje hajiya kidena kuka Allah baki lpy" idanunta kadai ta kalla taji ko kadan bata natsu da itaba, batama yarda bane, koma menene Allah ubangiji ya bayyana gaskiya, ya kuma karesu daga shirin duk mai shairi, cikin wani irin kuka Big Mum ta daga kafa da kyar tace "Firdausi ni fa? Nine yau zan kashe matar Boy dina habadai, nida nake cikin tsananin farin ciki tadawo" ahankali Mami tace "karki damu kidena kukan nan bakida lafiya, muje ki kwanta anjima sai akira limamu yamiki addu'a" ahaka tana kuka sosai suka fita jikinta ko ina rawa yake Allah dai yasa sun yarda, tasha da kyar.

Awajen parking yay parking ya bude bayan motar yakara taba wajen heart dinta, yana beating amma kadan kadan in bama ka natsu ba bazaka jiba, ahankali ya dauketa yay cikin hospital da ita office dinshi ya shiga da ita ya kwantar da ita akan gado kafin yafita da sauri yaje pharmacy wani irin allura ya karbo da sirinji saikuma ruwan alluran baima tsaya biyansu ba yadawo office din da mugun sauri ya fasa kwalban ya debo alluran, hannu yasa ya daga rigarta sama yamata alluran a daidai ta saitin kan zuciyar ta sanan ya zare ya daura hanunshi akan wajen yana sauraran beating din idanunshi akan agogo, wurin minti biyar alluran ya dauka kafin heart dinta yafara beating normal ajiyar zuciya ya sauke yace "Alhamdulillah" sanan yaja rigarta kasa ya gyara mata, statesocope dinshi dake kan table ya dauka ya saka sanan yadawo gadon ya daura akan kirjinta yana saurara cirewa yayi daga kirjinta batare daya cire daga jikinshi ba yafita daga office din wani alluran pcm yasiyo a pharmacy yabiya kudin sanan ya dawo office din yamata jin zazzabi ajikinta zama yayi akan kujera yana kallon fuskar ta, ahankali yakamo hanunta yahada danashi yana shafawa yana tunane tunane daban daban, kafin ya ciro wayarshi daga aljihu wani sako yatura sanan ya maida wayar aljihu, ajiye hanun nata yayi ya mike tsaye yana zagaye dakin, yakai kusan 10min ahaka sanan ya shiga bedroom din dakin alwala ya dauro yay Isha'i aciki kafin yafito ganin har lokacin bata farkaba yasa ya zauna akan kujera yasake kamo hanunta yana shafawa yana addu'a tafarka.
Chapter 65 · 0% Book details