Sashe 10
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Kasa bashi amsa tai ganin maganin Baba yay aiki gashi yaji sauki, bayan hannu tasa to goge hawayen dasuka zubo ta juya ahankali tana dingisawa batare data sake kallonshi ba ta tsugunna da kyar sabida kafarta tadau hijabin ta dake kan carpet tasaka tai hanyar fita daga dakin, wani irin fizgota taji anyi arude tajuyo baiyi watawata ba ya dauke ta da mari mai kyau hakan yasa tafasa wani irin uban ihu ta dafe kuncinta tana wani irin kuka, nuna kanshi yay da yatsa yana kallon fuskarta cikin husky voice dinshi yace "ke kinsan wayeni ina miki magana and u dare walk out of me, F*ck!" yawani dunkule hannu ya daki iska, Muji da tuntuni yake tsaye abakin kofa ya shigo da sauri yazo wajen dan tun jiya da daddare ake nemanta agida, hankalin kowa yatashi, dazu dasafe ma su Umma sukazo duba ko agidansu ta kwana, kotadawo da latti tsoro yasa ta kwana amma batanan hankalin Baaba duk yabi yatashi, yanajin haka yadau keke yafito batare da kowa yaganshi ba hakanan zuciyar shi yace yazo yadubata anan. Karasa shigowa yay yabita da kallo yanda take kuka sosai ga hanunta akan kuncinta da sauri Muji ya kama hanun ya cire daga kan kuncinta ya kalla yanda wajen yay ja duk shatin hanunshi sunfito, fadawa kan Muji tayi tana sheshekan kuka da kyar ta iya cewa "mutafi Ya Muji yariga ya warke" Cireta Muji yay daga jikinshi ya kalli Mahaukacin dasu yake kallo, azuciye Muji yace "uban me kanwata tama ka mare ta haka eh adam, butulu kawai, kasan irin dawainiyar datai dakaine mahauka..." da sauri tarufe mai baki tana kuka tace "dan Allah nidai mutafi gida, yaji sauki shikenan ai" ture ta Muji yayi hartana neman faduwa cike da masifa yace "wlh karki bari na daura miki wani marin nima, tun dazu na tsaya anan ina ganin abunda yamiki uban wayeshi dazai mareki haka? aida kinbarshi anan yacigaba dacin abincin bola banza dakiki mai dukan mata" cakumo shi yayi azuciye da idanunshi dasukai mugun ja ya shake Muji sosai, Muji yafara tari abunku daba karfi daya ba, tashi tayi daga tsugunen datake tana kuka tafara dukan kakkarfan hannunshi da karfi tana kuka. "ka sakeshi, ka saken min wana, wlh ka sakeshi, zaka kashe shi" cire hanunshi daya yay daga kwalar rigar Muji yasa hannun ya hankadeta tafadi kasa, wani irin mukurkusu tayi sabida ciwon ta daya kama mata tafasa ihu sosai. "wayyo Allah na cikina, Ya Muji zan mutu, zan mutu wayyo" juyo da kai yay ya kalli Muji da tsabagen wuya idanunshi sunyi ja sosai, jijiyoyin kanshi sun fiffito yace "duk randa ka kara haduwa dani watch ur tongue and know how u speak to me, bana tolerating raini one single bit get it?" ya tambaye shi fuskarshi a mugun daure dan ranshi yay tsananin baci, gyadamai kai Muji yayi ahankali dan ya shaku wlh, hakan yasa ya sake shi yana kai hanun hancin shi yana tsaki, da sauri Muji yay kanta ganin yanda take kuka kaman zata mutu, dagota yay da karfi tareda saka hanunta daya ta bayan wuyan shi ya taimaka mata ta mike tsaye da kyar, fasa ihu tasake yi zata koma kasa. "Ya Muji bazan iya tashi ba, cikina, Wayyo Allah na jama'a, wayyo na shiga uku na lalace ku taimakeni" ta rirrike shi, Muji dayake ji da bakin cikinta dan ita tajamai wanan muguwan shakan gakuma tausayin ganin yanda dukta rikice, ahankali yace "toyi tafiya ahankali muje waje mu shiga napep muje gida" girgiza mai kai tayi tafashe da kuka sosai tace "ni kadauke ni idan nai tafiya barkewa ciwon zaiyi ayanda nakejin yakemini" kwalalo ido Muji yay ya harareta yace "to ta ina zan iya daukan ki wai Balkisu, kinga wlh ko kiyi tafiya konabarki anan baruwa na narantse" kara maida hanun nata bayan wuyanshi yayi tana kuka, ya jata da karfi dayaji kaman zasu fadi dan kin tafiya tayi sabida ciwon dake mata sosai, yafita da ita daga ginin ya sakata a keken yana hararan ta yace "ai Allah yakara uwar taimakon cikin ma yafashe banziya kawai" ya watsa mata mugun hararan jiyake kaman ya gwabje ta, ya shiga gaba azuciye danhar yana buge kai, harya kunna keken yakasa hakura ganin yanda take kuka daga gani bakaramin buge ciwon tayiba gakuma wuyan shi daya rikemai dan har yanzu bai dena zafiba. Wlh bazan yarda ba" fita yay daga keken yay hanyar ginin daidai shima mahaukacin yana fitowa sai wani kyankyani kyankyani yake yana kallon kuturun takalmin kafarshi injishi, ganin bolan wajen yasa yay turus ya tsaya yana tunanin yanda zaibi ya wuce, ganin Muji yadawo yasa ya zubamai mayun idanunshi masu kama dana mage, dan komawa baya kadan Muji yayi dan yaune rana tafarko dayaji mahaukacin nan ya mugun cikamai ido, sanan ya kallai yace "wlh Allah ya isa bamu yafema ba dukan mu dakayi, kaga yarinyar chan daka tado mata da ciwo" ya nuna Bilkisu dake cikin keke ta cusa kanta a cinya tana kuka yace "da kana mahaukacin ka, duk uban dattin dakayi bata kyamace kaba ta kula dakai, ta gyara inda kake zama, tasaka ledar dakake kwana dinchan aciki wanda tundaga gida ta dauko, kullu yaumin saita debo abinci daga gida takawo ma kaci sabida dukan ka ake idan kasatoma yan shaguna buredi, tafasa asusun ta tasiyo ma wanan takalmin dake kafarka sabida yankewa dakayi akafa sabida rashin takalmi, tasaima wanan rigar jikin naka dan na jikin ka yagama yawo, sanan ta karboma addu'a wajen Baban ta, tabaka kasha ka warke shine ka zanemu ko, to Allah ya isanmana wlh, da marinta da shakeni dakuma fama mata ciwon ta bamu yafeba" yana fadin haka yajuya da gudun bala'i ya shige keken dayariga ya kunna yabar wajen dan gani yay kaman zai biyosu.