Sashe 35
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ahankali ta turo kofar, Baaba ce kadai tanata faman daddanna touching screen wayar da Abba yasai mata tana ganinta ta ijiye tace "zonan tawaje na" harda dan gudun ta tafada kan Baaba sai kuka, cikin kuka tace "Baaba dan Allah karki tafi ki barni, dan Allah mukoma gida tare banason mutumin nan" girgiza mata kai Baaba tayi fuskarta ba alamun wasa tace "da auren akan ki, ai auren kenan, kifara zama dashi kafin ki tantance ko bakison shi yaron me halaye na gari haka, hakanan zaki daure kindaiga iyayen mijinki yanda suke sonki saiki bisu sau da kafa, kima mijinki biyayya inya kiraki kije karna karajin kince bakison shi" nan ta shiga yimata wa'azi mai shiga da ratsa jiki. Mami ce tashigo dakin da sallama tana murmushi ganin yanda Bilkisu ke kuka ta kankame Baaba tace "wanan kuka haka daughter kiyakuri kinji bagamu nanba" tashi Baaba tayi tana tureta tace "kinga sakeni nafara latti banison nai dare fa ahanya" tafita da sauri dan batason tai kukan da takeji, tashi tayi Mami tarike mata hannu tafashe da wani kuka sosai, hannu Mami tasa ta share mata hawayen tana murmushi tace "daughter nafa jaruma ce, dena kukan zomuje mumata rakiya" hijabi ta dauka tasaka suka fita sai uban kuka take mara sauti har waje, tsaye yake kusada Baaba sai magana suke wanda bata iyaji amma fuskarshi dauke da lallausar murmushi, budema Baaba kofar bayan mota yayi da gudu taje ta kankame Baaba tana wani irin kuka cirota Baaba tayi daga jikinta tana lallashi tanuna Ayyan dayay kaman bai gantaba tace "baga mijinki nanba kikema mutane kuka, ke dalla rabu dani karna makeki" Mami da Big Mum duk suka mata fatan alheri ancika boot da kayan atsaraba takaima yan zaria, ta kalli Bilkisu data kasa daina kuka ta shafa kumatun ta tace "Allah bada zaman lpy ki rike abinda nafada miki kinji" ta shiga motar da sauri tana boye kwallan daya zubo mata Ayaan yarufe motar yanama driver alama yatafi, tanaji tana gani Baaba ta tafi abinta tabarta. Batare daya sake kallonta ba yay wucewar shi wurin big Mum yace "big Mum yunwa nakeji" murmushi tai cike dajin dadi tace "muje nabaka abinci my boy" sukai wucewar su sukabar Mami daketa lallashin ta saida tai shiru sanan suka wuce part dinta.
Apalor suka zauna kanta akasa Mami ta kunna kallo tasa mata zee world tana janta da hira sai asanan tadan saki jikinta ganin haka yasa Mami tai sama dan akwai kiran datake so tayi.
Kallonta take dudda rabin tunanin ta na gida, dan bawani gane kan film din takeba, yadade tsaye abakin kofa kafin ya shigo dakin fuskarshi adaure yana tafiya cike da izza, kamshin dataji yasa ta daga kai da sauri tana ganinshi ta mike tsaye da sauri zatai stairs da hannu ya nunamata kujeran data tashi gabanta na faduwa takoma ta zauna, Apple yadauka dake kan hadadden bowl asaman dining table sanan yadawo cikin falon shima akan kujeran ya zauna yadau remote din da Mami ta ijiye mata akusa da ita ya chanza channel zuwa na wrestling kafin ya kwanto ya daura kanshi kan cinyarta yana gutsuran apple din dake hanunshi yanaci, dudda yanajin yanda jikinta ke rawa hakan bai hanashi gyara kwanciya da kyau ba yanacin apple dinshi batare daya kalli fuskarta ba, stairs ta kalla dan ko kadan bataso Mami tazo ta gansu ahaka sanan ta kalli fuskarshi ta fashe da kuka tana share kwalla ko kallonta baiyiba, ahankali Mami ke saukowa daga stairs bayan tagama wayar datake yi da Ummu Haneef tsayawa tai chak hango Ayaan yanda ya daura kanshi akan cinyar Balkisu yana kallo abinshi girgiza kai tayi tajuya da sauri rashin kunyan Ayaan ya girmi tunanin ta wlh, bari baban shi yadawo yauyau dinan zata bashi matar shi sutai gidansu.
Kallon agogon dakin tayi ganin karfe uku kuma tun kafin azahar take dakinshi bataga yay sallaba yasa ahankali tace "anyi sallan azahar fa" sai a lokacin yadan birkito da kanshi ya kalleta ya daure fuska tamau yace "ke nakema sallan dama?" girgiza kai tayi atsorace yace "gud, to banga damar yiba nd u shut d f*ck up kona natsar dake" "daughter" daga sama Mami ta kwalamata kira ahankali tace "na'am" sanan ta kalleshi ganin baida niyar dagata yasa ta daura hannuwan ta akanshi ajiyar zuciya ya sauke wanda yasa ta tsorata ta janye hannuwan dan tazaci dukanta zaiyi, jin Mami takara kiranta nabiyu yasa yadagata tareda lumshe ido da sauri tamike tai sama da gudu yabita da kallo yana murmushin gefen baki, dakin Mami ta shiga da sallama kanta akasa, cup Mami ta mika mata tace "shanye wanan ina zuwa" karba tayi Mami ta tashi tafita daga dakin ahankali ta kafa cup din abaki ta shanye ta zauna akasa tana jiran shigowan Mami, ba'a jimaba tadawo da dan babban bowl dauke da farfesun kaza dayaji magani ajiye mata tayi tace "zoki cinye kafin ya huce" murmushi tayi dan wlh tanason kaza kafin akunyace tazauna akan gadon data ijiye mata tafara ci ahankali Mami kuma nawaya har taci iya cinta taji tai dam, Mami batare data yanke wayarba ta kalleta tace "idan ya isheki toki shanye roman tass" gyadakai tayi ta shanye roman kafin ta mike tsaye tafita daga dan kai plate din kitchen hada ido sukayi da sauri ta dauke kai ganin har lokacin wrestling yake kallo kenan la'asar ma baiyiba wanan wani irin dan iskan mutum ne, astagafurullah tace ta shiga kitchen ta ijiye kafin takoma sama dakinta ta shiga kasancewar bata salla yau tai zaman ta tana wasa da wayarta.
Koda daddare bayan Abba yadawo da Mami tasame shi da maganan abama Ayaan matar shi sutafi gida bakaramin murna da dadi yajiba, waya yadauka yakira Ayaan dake Part dinshi yazo itakuma Mami takoma ta shirya Bilkisu cikin wani hadadden lapaya maroon sanan tahada mata magunguna datace tadinga sha kullum kafin tarike ta takaita falon Abba, hadasu Abba yay yamusu wa'azi sosai sanan yakara bama Ayaan amanar ta, big Mummy ma tamusu Mami ma tamusu sanan suka rakosu har mota sai uban kuka take itadai yau tabanu Mamin datake gani taji dadi ma yanzu tafiya zatayi ta barta kuma gidan wanan mutumun, a motar shi suka sakata ya kunna motar yabar gidan yana murmushin keta. Ganin tana neman kashemai dodon kunne da kuka yasa yawani irin taka burki akan hanya arude ta dago kai da kakkausar murya yace "wlh koki natsu kona wurga ki kan titin nan na takeki na wuce" gum tayi ko tari bata karayiba harsuka kai gidan yay horn mai gadi ya bude mai ya shiga yay parking ya kalleta yace "wuce kitfita ke" adan tsorace tabude kofar ta fito tamaida mai tarufe hararan ta yayi sanan ya kunna motar yama mai gadi horn yana budemai yafita da gudu dan sauri yake club zaije su Fawaz tun dazu da Pops keta maganganun shi suke kiranshi, takai minti shabiyar a wurin kafin tai hadadden flat din da tagani ahankali ta bude kofa ta shiga tana kallon ko ina yanda yamata kyau yanzu itane agidan nan da wanan mutumin dako salla bayayi itadai rayuwa bata mata adalci ba wlh. Upstairs tayi tanata waige waige koda takai tarasa gane wananne dakinta saida taga akwatunan aure a saman wardrobe yasa tagane wanda take cikine nata. Ahankali ta zauna abakin gado tafashe da wani irin kuka zuciyar ta namata zafi maisa Isyaka zaimata wanan abin, ita yanzu bama fasa auren nata yake mata ciwo ba abinda yafi mata ciwo shine hadata da wanan mugun mutumin da akayi, dama taimako kan zama haka? Sosai take mugun jin kewan Baba su Raiyana da Layla Umma da mama, kankame filo tai tana kuka ga wani tsoro tsoro datake ji ahaka bacci yay awon gaba da ita.