← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 89

Sashe 79

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Abuja kuwa Bilkisu ta tasasu agaba kuka badare ba rana d only maganan da take yi shine ina yake ina yake, Aaman kaman zai haukace yanda kukan ta ke tadamai da hankali tun yana kiran number Ayaan ya shiga har yazo yadena shiga gabaki daya, hankalin shi dukya tashi maiya sami Ayaan? So yake yaje Abujan amma yakasa dan inhar bashi yazo ya lallabata yace mata gashinan zuwa yana hanya ba batacin abinci, yaudai ya yanke shawara zai tafi Kanon yaje yadubo meke faruwa sati biyu bawasa ba gashi wani irin mugun zazzabi ta tashi dashi yau, da kyar Mum ta lallabota tai wanka tafito tana rawan sanyi, kaya tabata tasaka, tabata tea mai zafi tana karban tea ta ijiye tana girgiza kai tana yatsine fuska, ahankali Mum ta rungumota jikinta tace "yakuri kisha kinji daughter yauwa yar albarka sha nabaki magani" Mum tai maganan tana kai tea din bakinta yatsine fuska tayi ta kurbi kadan, ture tea tayi da sauri tana kokarin yin amai da sauri Mum ta ijiye tea tanason ta dagata amma harta kwaro aman anan kan gado. "subhannallah sannu yar nan" dagata Mum tayi da taimakon ta tai bayi da ita ta wanke mata fuska da wuyan data bata sai uban kuka take, jikinta yay mugun zafi hanunta Mum tarike tafito ta ita tai dakinta da ita kasancewar tariga tabata gadon, abakin kofar dakin sukaci karo da Aaman duk yay wani irin yana kallon fuskar Bilkisu dake kuka awahale, kallo daya Mum tamai ta shige da ita dakinta kwantar da ita tayi akan gadonta ta lulllubeta ganin sanyi takeji ta kashe AC tadawo kusa da ita tana share mata hawaye tana bubbuga bayan ta tana girgiza mata kai tace "stop crying yar albarka sleep" haka tadinga mata har wani wahalallen bacci yay gaba da ita tamike tafito daga dakin har lokacin Aaman na inda ta barshi tsaye ya daura kai abango. "Aaman" takira sunan shi anatse, bude ido yayi ya kalleta kasancewar Mum nurse ce yasa da sauri yace "Mum meke damunta wani magani zan siyomata?" girgiza kai tayi tace "don't worry" saikuma ta matso kusa dashi ahankali tace "Aaman ka shirya kaje kano kanemo Ayaan musan halin dayake ciki, matarshi is pregnant" da sauri Aaman ya kalleta, gyadamai kai tayi tace "yes she is, please go and find out meke faruwa, kaga magungunan brain dinta sun kare by now ya kamata tana shan wasu ne dan stage by stage medications ake baka, yanzu kusan 4 days batasha any ba, please get ready and leave for kano" gyada mata kai yayi ya wuce jikinshi yay wani irin mugun sanyi da sauri ya share hawayen dasuka dan leko daga idanunshi yay part dinshi wanka yayi ya shirya cikin white shadda yafito yazo yama Mum sallama sanan yatafi.

*Kano*
Ahankali idanunshi ke motsi yana kokarin budesu da sauri Abba yakama hanunshi yace "Boy, Boy gani nan anan open ur eyes am with you mah Boy" da sauri Baba da Baba Suleman ma suka taso suka tsaya akanshi Baba sai tofamai addu'a yake, ahankali yabude idanun dasukai ja sosai ya daura shi akan fuskar Abba yana kallon su gabaki daya asanyaye, Abba kaman zaiyi hawaye ya shafa gefen fuskarshi yana murmushi yace "ya kakeji yanzu Boy mekema ciwo? Sulemanu kira Ibrahim yadubamin shi" bakaramin nauyi zuciyar shi kemai ba kaman an daura dutse akai shikadai ne abinda kemai ciwo, ahankali yake bude baki ganin haka yasa Abba ya matsa kusa dashi sosai yakai fuskar shi saitin fuskar shi yace "talk to me mekake so?" murya chan kasa da kyar yace "wife" sake kallonshi Abba yayi saikuma yakamo hanunshi Wanda ba karin ruwa ajiki yarike yana kallon fuskar shi anatse yace "Boy bamu ganta ba, dama jira muke katashi muji ina ka kaita?" shiru yayi idanunshi nadan jujjyawa hakan yasa Abba yahau shafa goshin shi ganin yana kokarin magana yasa Abba yakai kunenshi saitin bakinshi ahankali yace "Aaman" da sauri Abba yace "wurin Barrister Aaman?" lumshe ido yayi yabude alamun eh daidai lokacin kuma Dr Ibrahim ya shigo tareda Baba Suleman.

Taxi daya dauko daga airport bayan ya sauka ne ya sauke shi agaban gidan su Ayaan, fitowa yayi bayan ya salami driver sai uban kamshi yake farin shaddar jikinshi sai wani wal wal yake, uban securities din d aka zuba akofar gidanne suka tareshi "wakake nema?" ahankali yace "Dr Ayaan" jin yakira sunan dan masu gidan yasa suka budemai kofa shikuma ganin basu cemai komiba yasa yace yana nan Kenan yay cikin gidan, inda aka taba shiga dasu da farkon zuwan shi yayi a natse, agaban kofa ya tsaya yay sallama batare daya bude kofar ba, Raiyana dake kitchen da Mami, girki suke yi zasu tafi asibiti Abba yakira wai Ayaan yafarka Sai murna suke. Kasancewar Mami dukta sallami yan aikin ta yasa ta kalli Raiyana dake sanye da doguwar rigan atampa ja da dan kwalinta tace "jeki bude kofa naji ana sallama" akunyace tace "to" tajuya da gudu tafita daga kitchen din tai falo, bude kofar dakin tayi gabaki daya hankalinta nakan TV dake aiki a falon ana wani film din fada, wani irin dukan uku kirjinshi yayi ganin yarinya mai kama da Bilkisu exactly bambanci kawai shine wanan tafi Bilkisu tsawo sosai dan doguwa ce, dan gyaran murya yayi hakan yasa tajuyo da sauri adan rude suka hada ido, dauke kai tayi da sauri ganin yanda ya tsareta da ido ahankali tace "Mami tace wai ka shigo" juyawa tayi da sauri ya bita da kallo saida ta shige kitchen sanan ya sauke ajiyar zuciya ya shiga dakin ya zauna akan daya daga cikin hadaddun kujerun falon.
Ko minti biyu ba'ayi ba Mami tafito daga kitchen din cikin babban mayafin ta tana ganinshi ta ganeshi murmushi tayi shikuma yadan zamo ya gaidata yace "ina yini Mami, ashe abinda yafaru kenan Allah kare tsarewa ya kiyaye gaba" Ameen Mami tace "sannu da zuwa Aaman, ya hanya" murmushi yayi yace "lpy lau Mum, ina Ayaan Mum inata kiranshi baya shiga" nan yabata labarin komi kaman Mami zatai kuka itama ta sanar dashi abinda yafaru bakaramin tausayi yaji ba kaman zaiyi kuka ahankali Mami ta mike tace "bari nasa akawo maka lemu muhada abincin a flask saimu tafi asibitin, mungode sosai da taimakon dakamana" wucewa kitchen tayi ko minti daya ba'a karaba saiga Raiyana tafito da tray dake dauke da exotic mai sanyi da ruwa da cup sai dambun nama da cake yanda ya kafeta da ido yasa ta dauke kai jikinta na rawa tazo gavanshi table taja tadaura akai, ahankali tana kallon kasa tace "Mami tacewai kafara sha gatanan zuwa" tajuya da sauri zata tafi yace "ke kanwar Bilkisu ce" da sauri ta juyo suka hada ido ta gyadamai kai tareda sauke idanunta kasa, gyadakai shima yayi saikuma yace "ya sunanki?" batare data dago kaiba tace "Raiyana" da sauri ta juya tacigaba da tafiya kaman daga sama taji yace "Raiyanah" dan dago kai tayi suka hada ido da sauri ta juya ta shige kitchen din kirjinta na bugawa. Ciro wayar shi yayi yay dailing number Mum dinshi dake zaune adaki kusa da Dad, ringing biyu ta dauka kafin tai magana ma yaji kukan Bilkisu dake kusa dasu, Mum tace "yaya ka ganshi kuwa" gyada kai yayi saikuma yafada mata anma harbeshi ne ashe yanzu haka yana asibiti, Abban shi dake wurin yace "bari kawai mutaho da ita kaga shi kawai taketa tambaya" Mum tace "baban ka yace zamu kawota yanzu" ahankali yace "okay idan kun sauka za'a zo ataho daku" katse wayar yayi daidai lokacin Mami da Raiyana sun fito rike da manyan basket dake dauke da kulan abinci da flask, nan yafadan ma Mami su Dad zasu kawota bakaramin murna tayi ba ta tura driver airport yaje yajurasu sukuma suka wuce hospital.

Ahankali Mami ta tura kofar dakin da aka kwantar da Ayaan ta shiga Aaman da Raiyana biye da ita kowanen su idanunshi akan Ayaan dake zaune akan gado yay wanka danhar kaya ya chanza yana sanye da 3quater daya tsayamai a gwuiwa saikuma white t shirt dayasa amma anannade ta saman cikinshi kadan, bowl din dake dauke da sliced fruits ne a hanunshi yanaci kadan kadan yana lumshe ido ko kadan bayajin dadin fruits din danma su Abba sun tursasa shine baiyi niyyan sha ba, da sauri Mami tai kanshi Abba kuma yana ganin Aaman ya washe baki yace "oyoyo son" shigowa dakin Aaman yayi yana gaida kowa, ahankali Ayaan yadago kanshi daga kafadar Mami ya kalli Aaman hakan yasa Mami ta tashi takoma kusada Abba shikuma Aaman yadawo kusa dashi ya zauna zaiyi magana Aaman ya girgiza mai kai yana murmushi yace "don't worry Mum da Dad dina are on their way zasu kawoma matar ka" dudda yanda zuciyar shi kemai nauyi saida yay murmushi, dan murmushi Malam yayi Raiyana kuwan boyewa tayi abayan shi tana dariya itama Allah bata mai sonta haka irin mijin Anty Baby, karfe uku da minti ishirin wayan Aaman yadau kara dauka yayi da sauri Ayaan dake kwance yafara kokarin tashi, murmushi kowa na dakin yayi Aaman ya taimaka mai yatashi ya zauna tareda jingina da pillow, mikewa yayi ya kara wayar a kunne ahankali yace "okay Mum saikun zo" ya katse wayar yanda Ayaan ke kallonshi yasa yay murmushi yace "gasunan zuwa wai sunga driver da Mami ta tura" dan lumshe ido yayi, Abba baisan lokacin daya mutsili Mami tariga ba murya chan kasa yace "look at our handsome Boy" murmushi tayi ta ture hanunshi ta kalli Raiyana tace "tsabagen doki bakici abinci bafa Raiyana zokici" murmushi tayi akunyace tana kara labewa abayan Baba dan ita kunyan su takeji barin ma mijin Anty Baby da abokin nan nashi, ido Ayaan yabude ya kalleta murmushi ya sakar mata kafin ya kara lumshe idon, Baba yace "badake wai ake magana ba" dan dago kai tayi karaf suka hada ido da Aaman, murguda mai baki tayi ta kalli Mami tace "Mami banajin yunwa ne yanzu" Abba ne yatashi rike da sandar shi ya kalli Baba Suleman da Baba yace "kunga muje waje mujira bakin mu, mu shigo dasu" tashi duk sukayi suka fita dakin yarage daga Ayaan dake zaune jingine da bango ya lumshe ido sai Aaman dake kusa dashi Mami dakuma Raiyana dake kusada ita tana wasa da yatsun ta.
Chapter 79 · 0% Book details