← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 89

Sashe 72

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mutanen daya gani a unguwan su dayake shiru shiru police namusu magana akan su koma gida babu wani matsala dan karan bindiga yafito dasu yasa Ayaan yay parking da sauri ya shiga cikin gidan dayaga bullet sun huhhuda bango wasu akasa dayake akwai hasken nefa bau, dayake polisawan sun sanshi basu hanashi shiga falon ba, CP yagani tsaye yay folding hannu a kirji yana kallon wani likitan police dake bama mai gadi daduk hancinshi ke jini taimako, da sauri yay wurin ya karbi abin hanun likitan kaman zaiyi kuka ya kalli mai gadi yace "Isya" yama kasa magana sai taimakon daya shiga bashi saida ya tsayar da jinin sanan ya samai bandeji ya gyara kafar dasuka yanka, CP yace "banace karkazo ba Ayaan" "bazan iya zama ba kawai bayan rayuwar matana na cikin hatsari" daidai lokacin mai gadi yabude ido da taimakon Ayaan yatashi ya zauna CP yazo gabanshi yaja table ya zauna yace "Ya kake ji dafatan zaka iya amsa tambayoyi na" gyadamai kai Isya yayi Cp yace "good, meya faru fadamin" nan ya basu labarin duka abinda yafaru yakara da "amma lokacin daya yankamini cinya dannace kana gidan Abba cemin yayi karyane Hajiya tacemai kuna nan" da sauri Ayaan yamike tsaye yace "Hajiya kace?" gyadamai kai yayi, hannu Ayaan ya daura akan kirjinshi dake wani irin bugawa da sauri CP ya dafashi yace "lafiya kasan hajiyar ne? If u know anything tell us sabida mukai karshen case dinan" wani irin dunkule hannu Ayaan yayi ya daki iska yace "f*ck" dafa kafadar shi da karfi CP yayi yace "calm down, sit" zama yay da kyar CP yace "wacece hajiyar wakake suspecting?" shafa kanshi yayi ya fuzar da iska yace "Big Mum, Hajiya Saratu, but my question is me Bilkisu tamata why did she wanna kill her?" yana gama maganar ya mike tsaye da sauri yafara maganan zuci "yes, ranan da aka dauke Bilkisu dudda he was talking to Dr Ibrahim awaya yaga yanda Bilkisu tafito daga shashin Big Mum arude, and apart from that tanata damun shi amota cewa zata fadamai wani magana har suka kai gida, suna kaiwa gida before he could listen to wat she was trying to tell him big Mum takira wai batada lpy, yatafi, kafin yadawo babu Bilkisu saidai jini a stairs, and ranan nan yakamata tana shirin kasheta could all dis be coincident? No" dafashi da akayi yasa yadago jajayen idonshi ya kalli Cp, ahankali Cp yace "mesa step mum dinka ce suspect dinka" "sabida itace" nan yabama CP labarin komi yagama da. "ita takirani jiya tana tambayana muna inane nace mata muna gida because I don't trust her tun kamatan danayi lokacin tana shirin kashe Bilkisu" girgiza kai CP yayi yace "mutafi gidan ku, dan from all this she is a suspect so dole zamu mata tambayoyi ta amsa mu" ahankali Ayaan yace "nasa Mike yamin fixing CCTV camera a Palo da falon sama ta tun randa takusa kashe min matata" Cp ya gyada kai yace "good hakan zai taimaki aikin mu sosai, meanwhile zan kira once angama gyara kafarsu achan headquarter amini interrogating dinsu muji wani information zamu samu a wurinsu, muje" fita sukayi daga dakin bayan su bar police biyu tareda Isya motocin suka shiga shikuma ya wuce tashi sukai gidansu

Ana kiran sallan asuba suka isa anguwan su horn sukayi securities suka bude parking sukayi suka fiffito da saurin su sukai part din big Mum ga mamakin su abude sukaga kofar awangale da sauri Ayaan yay sama dakinta ya bude babu kowa ciki sai uban kayan data zuba akan gado ga wardrobe abude, da sauri yafita ya shiga sauran dakunan babu kowa, sakkowa yay da sauri ya kalli Cp yace "batanan" da sauri CP yace "what" sa yaranshi yayi su dadduba ko'ina shikuma Ayaan yay waje yana kwalama Mike kira da sauri Mike dake bacci yafito wasu keys yakarba daga hanun Mike daidai lokacin CP sun fito Ayaan ya wurgamai key yace "ga key dakin da computer CCTV suke ciki Mike kaisu, bari naduba Mami na" yay shashin Mamin shi da saurin shi ga mamakin shi abude yaga itama kofar, ciki yay da gudu sai yaga yan aikin su guda biyu azaune kan dining sunyi zugum wani irin tsawa ya daka musu yace "ina Mami na?" arude sukace "sir hanayi yan su yatashe mu daga bacci ita da hajiya saratu kaman fada sukayi, saikuma mukaga hajiya saratu ta taso Mom dinka agaba suka fita bamusan inda sukaje ba" "innalillahi wa innalillahi raji'un, wai wat is happening ne, Big mum!" fita yayi da gudu yay dakin Computers din yasame su suna a daidai inda Big Mum ta tura Mami cikin mota takafa mata bindiga tabaya tayanda su kadaine sukasan da bindigar, innalillahi wa innalillahi raji'un kawai Ayaan ke maimaita wa baima farga daga tashin hankalin ba wayarshi tai ringing kasama dauka yayi saida CP yace yadauka sanan ya dauka, sunan Big Mum ne baro baro ya bayyana agaban screen din hakan yasa ta kafe screen din da ido da sauri CP yace "waye ke kira itane?" gyada kai yayi da sauri CP yace "dauka sa a speaker muji mezata ce" ahankali yay picking yasaka a speaker tsabar bakin ciki yakasa magana ma, wani irin dariya big mum tayi tace "Ayaan, Ayaan, yaro man kaza! Well nakira ne nafada maka abu biyu zuwa uku dan nasan karkiga kasan koni waccece yanzu dan nasan yarana dakuka kama sun kira sunana" tai wani irin murmushi dasuke iyajin sautin shi tace "inhar kanaso ka kara saka mahaifiyar ka a ido abu nafarko danake so kayi shine duka kamfanin Alhaji da dukiyoyin shi daya maida sunanka kamaida su sunanan wato su zama mallaki na, nabiyu inaso yarana dakuka kama dan nasan yanzu haka police natare dakai asake min su, na uku wanda yake na karshe inhar kana son ka kara saka mahaifiyar ka da mahaifin ka wanda yanzu haka yakusa isowa hannuna a id...." da sauri ya katse ta ta hanyar cewa "Pops" yafada yana dafe kirji, murmushi tayi tace "kwarai kuwa Pops, pilot din Alhaji hmmm" tai wani irin murmushi dazan kirashi dana keta, tace "pilot din Alhaji yanda kasan tip da taya haka muke, shikemini komi dan baban ka karfi yakare kuma gani nikuma da kuzari ta" wani irin runtse ido Ayaan yayi jijiyoyin kanshi na fitowa tace "mahaifin ka nakiranshi yace yazo suzo sutafi nigeria akwai matsala yakirani, kafin yakirani Bala yariga yafada min halin da ake ciki, yanzu haka ubanka na cikin jirgi baisan inda kanshi yakeba anmai wata alluran bacci" kara danne kirji Ayaan yayi zaiyi magana CP ya girgiza mai kai, Big Mum tace "abu na uku inhar kanaso ka kara ganin mahaifin ka da mahaifiyar ka shine zaka bani Bilkisu amadadin su" "wat!" Ayaan yay wani irin ihu tareda dukan computer dake kan desk jikake kakakakak sun tarwatse, da sauri CP ya girgiza mai kai, Big Mum tai wani irin dariya tace "daka natsu dayafi shinema abu mafi alkairi, Bilkisu wato matar ka itace silar komi ya bacin mini haka har asirina yatonu, dan haka dolene na kasheta ita tafara jiyo asiri na aranan na kiraka itakuma natura aka dauketa akaje Bauchi aka yarda ita, saikawai gata tadawo saisa naso na kasheta ranan kafin tafadi komi amma ka kamani, Ayaan ka ganni nan akan dukiya zan iya komi wlh, bazan iya hakura bane uban dukiyar mahaifinka ka gaje komi ba, my initial plan was nakamo ka kamin signing komi yadawo nawa saina kasheka kai kadai, bayan ka mutu kaga ai bakin cikin rashin ka shizai halaka tsohon mahaifinka, uwarka kuma nabarta da ranta dan babu abinda zata iyamin, shine fa makirar matar ka tabata mini komi, Ayaan!" ta kirashi dawani irin kakausar murya tace "inhar kanason ka kara ganin Pops da Mami kamaida dukiya komi yadawo nawa, kasa asaki yaran aikina, sanan ka bani matar ka Bilkisu itace dan silar komi, kasan mezan yi inhar baka bani Bilkisu ba" tai wani irin murmushi mai kara kafin tai shiru tace "kadaisan nasan gidan su Bilkisu ko, saina sa ankashemin kowa nagidan su, fara daga kan Malam, Mamar ta, kishiyar mamar ta, kaninta mata biyu Raiyana da Layla, Baaba wacce tazo gidan mu da danta Muji, Ayaan! Rai daya tal dinan danake nema wato Balkisu inhar baka bani ita ba saina kashe rai bakwai hada da iyayen ka yakama rai Tara kenan, nabaka awa ashirin da hudu I lokacin ya cika zakaga kira" ta katse wayar kit.

Jama'a yaya kenan?
In nine Ayaan hakanan zanbada Bilkisu akashe ta gaskiya koya kukace?
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

85...
Chapter 72 · 0% Book details