← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 89

Sashe 40

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yana gama sa bituran hannun rigar yadau wallet dinshi dake kan bedside drawer yasaka a aljihun bayan wando, sanan ya mika hannu yadau wayarshi kiran iPhone xmas, mistakenly wayar yafadi anan kasa gefen gado, dan gajeren tsaki yaja kafin ahankali ya tsugunna dan daukar wayar dayaga yanakan wani farin yadi dayaga yadan leko daga karkashin gado, tsugunnawa yayi yadau wayar ya mike tsaye yasa kafa zai tura farin yadin dabemasan nameba dayadan leko yakoma ciki sai kuma yasake tsugunnawa hakanan yaji zuciyar shi na fizgar shi daya duba kome, ahankali yasa hannu yajawo farin yadin gabaki daya, yanayin yanda yajawo da karfi yasa abubuwan suka barbaje babban roban hoda yay tsalle yay gefe saikuma gashin dokin arna yay gefe daya saikuma ga yadin dayake aduddunkule, da mamaki yake kallon kayan dama yarinyar nan nasa attachment ne, saikuma ya mika hannu yadau farin yadin ya mike tsaye ya warware rigan yana tabe baki, rigan yabi dawani irin kallo daidai lokacin ta bude kofar ta shigo hanunta rike da black cover shoe dinshi, rigar bashi tsoro dataga ya warware yana wani irin kallo yasa ta zaro ido ta kallai, tsabagen yanda jikinta ke rawa batamasan sanda ta yar da takalman ba wani irin kallo yamata yasa arude tafara komawa dayaba tana tafiya. "dan girman Allah ka yakuri, wlh so nake kawai ka gyaru ka dinga salla saisa namaka hak..." da gudu ta kwasa tai downstairs ganin yanda yayo kanta, shi dayaga rigan yadaiga yay kama dana aljanna but ko kadan baikawo wani tunani aranshi ba maganan datayi yasa yagane kenan itace ta tsorata shi, take yaji rashin yana wani irin soyuwa, ganin binta yake yas ta kwasa da gudu tafita daga gidan mai gadi namata magana kota kanshi bata bi tafita babu hijabi ajikinta daga ita sai doguwar riga da dan kwalin ta, tana ko fita taci sa'a daidai wani keke napep yay dropping wata mata wup ta shige duk ta rude tana kallon waje ganin harya fito daga gate shima fuskarshi babu alamun rahama yasa tace "malam kama Allah mutafi kafin yazo ya kasheni, GRA zamu" da sauri mai keken ya kunna kafin Ayaan ya iso harsun waske, da sauri yakoma cikin gida ya shiga mota yabi bayansu dan baisan inda zataba, sune har GRA batadai san sunan layinsu ba amma tasan gidan, hakan yasa tana ganin gidan tanuna mai yana parking ko tsayawa mai magana batayi ba ta shiga gidan da gudun bala'i daidai nan Ayaan shima yay wani irin wawan parking awaje ya biyota a haukace, Mami, big Mummy, da Abba ne afalon, Abba da Big Mummy na zaune Mami kuma na tsaye daga ta wurin dining tanama wata yar aiki magana, tana shiga dakin bama ta lura dasu Abba ba ganin Mami yasa ta fasa wani irin ihu tai wurinta ta shiga bayanta ta kankame ta sosai tana nuna bakin kofa tace "Mami karki bari yadakeni wlh kasheni zaiyi yau" kafin Mami tama gama gane kan zancen ta shima ya shigo dakin ya dumfaro su idanunshi dasuka kankance tsabagen bacin rai akanta, yanda ta rirrike Mami tana neman ma fadir da itama tsabragen tsoro, "Ayaan!" Abba yakira shi da kakkausar murya, hakan yasa ya tsaya chak batare daya karasa wajen ba, Abba yataso yace "lafiyan ku kalau kuwa meya hadak...?" ko karashe maganan Abba baiyiba cikin kuka tafara tonama kanta asiri cikin kuka tace "Abba dama, uhm dama bayason yin salla ne shine nai shiga kaman dodo da daddare nabashi tsoro nace ance nazo na tunatar dashi yabi Allah ne...." nan tabasu duka labarin abinda yafaru habawa zokaga dariya gun Abba da Mami banda Big Mummy data daure fuska tana hararan Bilkisu data labe abayan Mami tana kuka. Juyawa yay zaifita daga falon azuciye Abba yakamo hannunshi yana cigaba da dariya abinshi, ya kalli Bilkisu dahar lokacin kuka take amma kadan kadan yace "Allah yamiki albarka yar arziki irin albarka mace tagari, ke Allah ya zundumaki a aljanna, Allah nagode maka dakabama Boy mata kaman Bilkisu" Mami kam harda mata kiss a goshi tana share mata hawayen datake tace "kin kyauta ina alfahari dake daughter na stop crying" Big Mummy cikeda fada tace "haba dai adinga adalci mana, sa'an tane da zatazo zo tana tsorata shi da daddare, yaro dan gata baisaba da irin rayuwar taba, baisan me wahala da sauran suba shine zata tsorata shi, gaskiya sam wanan abu bai daceba bata kyautaba kuma yahukun tata wlh" tunda Mami take bata taba kula Big Mum idan tafara kananun maganganun taba amma yau takasa hakura tace "dan tana neman shi da shiriya tana son yakoma ga Allah shine bata kyautaba? Shi yaro ne salla saiya gadama zaiyi aduk lokacin daya nishadan tu dayayi, haba mana hajiya" afadan ce Big Mummy tace "to ita waye dazata mai haka? Ai Allah gafurun raheemu ne, nannan mukaga karuwa data shiga aljanna sabida kare, Ayaan kobaya salla yanada dabi'u da dama masu kyau, yaro dai kin haifa amma kinkasa sonshi kullum kyaran shi kike, yanzu kuma namasan hala kece nan kikasa yarinyar nan ta tsorata shi, mai bakin hali kawai wacce ta tsani dan.." "saratu!" Abba yakira ta da kakkausar murya yana nunata da yatsa.
[7/21, 9:18 PM] 0mmer Farouk: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

51 - 52

Cikin fushi Abba yace "idan bazaki fadi alheri ba kiyimana shiru anan kona sassaba miki mara mutunci kawai da rashin sanin yakamata" ya karashe maganan yana kallon Ayaan dayama daskare awurin sai kallon fuskar ta yake, yakasa daina mamakin yanda yar yarinyar nan tai fooling dinshi haka on top of dat kuma tafito ahaka ba hijabi ba mayafi, juyo dashi Abba yay yana murmushi tareda shafa kuncin shi cikeda jin dadi yace "ashe saisa jiya darana dakazo office naganka a sahun farko a masallaci" dariya Abba yay sosai yace "masha Allah, am so proud of yata, and" yaja hannun Ayaan din ya zauna akan kujera ya zaunar dashi agefen shi yakara gyara zama yana kallon Ayaan din da shi yake kallo yace "wlh inhar ka daketa ban yafeba kaji nace wlh" ya kalli Mami dahar lokacin Bilkisu ta makalkaleta yace "dauko mata mayafi Firdauisi su tafi gidansu, janyeta Mami tayi daga jikinta tai sama tana murmushi, Abba ya kalleta yamata alamu datazo, tsugunnawa tai agaban shi yay dariya yace" inhar yatabaki bayan kun koma gida kifada min kinji, Allah ya baki duk abinda kikeso a duniyar nan, akaro nabiyu kina kara taimakon dana jibi yau babu wanan arniyar dankunen da sarkan da tun yana yaro nake fama dashi yadena dayake ya rainani yaki, nagode kinji yar arziki" itadai ko numfashin kirki bata iya fitarwa daidai nan Mami tafito dauke da babban mayafi ta yafa mata, aiko har waje suka rakasu saida suka shiga mota ne sanan suka dawo gida.

Gudun bala'i yake akan titi batare daya kalli koda fuskar taba, kadan kadan take satar kallonshi ganin ko kallonta baiyiba yasa tadan saukar da ajiyar zuciya, akofar gida yay parking batare dayace mata komiba sumsum tafita tai cikin gida, dakinta ta shiga da gudu harda saka key.

Yau kimanin kwana uku kenan basu haduba, sai taji batajin motsin komi agidan ne zata fito tanemi abinda zataci sanan ta gyara gidan tasake komawa daki ta kulle kofa.
Chapter 40 · 0% Book details