← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 89

Sashe 31

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ahankali yadaura hannayen shi akanta yana shafa manyan da kananun kitson dake kanta batare daya bude idanun daya lumshe ba, knocking kofar da akayi yasa yadan bude ido ahankali yace "common in" yay maganar yana saukar da hannayen shi daga kanta tareda gyara bayan rigarta. Dr Ibrahim, Nurse Sameera da Anesthesiologist mai suna Moses ne suka shigo dukansu atare, da ido yama Moses alamu ya shirya alluran, hannu yasa zai cirota daga jikinshi amma taki sakinshi sai kuka take kasa kasa, daukar ta yay batare data sakeshin ba ya kwantar da ita akan gadon zai tashi takara rirrikeshi tanamai kukan dabaya fita sosai tana kallon fuskar shi, jin yanda kirjinta ke bugawa yasa yadan hadiye haushin kanshin dayake ji namata wani laushi ahankali yace "relax nafasa miki to, calm down" sake kama rigarshi tai gam gam kaman mai rada tace "dagaske" yana kallon yanda lips dinta sukai jajir tsakiyar ya gyada mata kai yakai hanunshi bayan rigar yadan bude daidai inda za'ayi allurar da Moses yagama hadawa batare data masan yayiba dan duk hankalin ta atashe yake da wukaken dayace zai fedeta, da ido yamai alamu yayi, sanan yadan kalli fuskarta yanda take kallonshi da idanunta dasuka kankance tsabagen kuka ga dogayen gashin idon duk sun jike sun mammanne da juna kaman tasa gum, iskan bakinshi ya hura mata akan idon hakan yasa ta lumshe idon da sauri, wani irin azaba dataji tabayan ta yasa ta bude ido tareda kara damke shi da karfi tana kuka sosai saikuma luuu ta komar da kanta kan gadon wani irin bacci yay gaba da ita batare data sakeshi ba, dan murmushin gefen baki yayi sanan yasa hanunshi yacire hannayenta dake kan rigarshi ya maidasu kan gadon ya ijiye tareda sake gyara mata kwanciya ya dauko wani zani yarufe tundaga kafarta har cikinta sanan ya bude daidai wajen ciwon yadau abun rufe hanci da baki yasaka tareda kunna wutar operation, samira data rike kwanon surgical blades din da tagama kirgasu tace "Sir daga gani wanan patient din is very special sai kappa kappa kake da it..." wani irin kallo daya mata yasa tai shiru bata karasa ba, wani abu kaman marker Dr Ibrahim ya mikamai nan yay layin daidai saitin inda zasu yi aikin, sanan yakara mika hannu aka sakamai wani surgical blade akai, ahankali yadan kalli fuskarta kafin yasaukar dawani labule daya raba tsakanin su, sanan yama Moses magana yakara sakko da wutar kasa sosai yanda zasuga cikin da kyau, wukar ya dauka ya yanka fatar wajen Dr Ibrahim na share jinin dake zuba.... Nan dai operation ya kankama.

Akan kujera dake hanyar wurin theater din duk suka zauna Mami, big Mummy da Baaba dasuke ta bata baki dan kuka take ganin yanzu kusan awa uku kenan ba'a gamaba balle a fito, Abba da Baba Sulaiman suna tsaye suma addu'an samun lpy ta suke.
Anyi anyi Baaba tazo atafi gida taki tafiya wai ita sai taga anfito da Bilkisu tukunna zata tafi.

Sai wuraren 12:50 nadare suka gama operation din tatas, sai kallon appendix din daya cire mata suka saka awani kwalba yake yanda yay girma sosai dan gab yake daya fashe, inda kuma yafashe da mutuwa zatayi wlh. Da kanshi ya gungurota daga gadon dan kaita dakin hutu yana fitowa kam yaga su Abba dasu Baaba sun tatashi suna kallonta, Baaba ta fashe da kuka tana tattaba fuskarta ganin bata motsi, dan murmushi yay yace "lpy ta lau bacci take zata farka, operation din was successful" Alhamdulillah duk suka ce, yace "bari nakaita dakin hutu" wani daki ya bude kofa ya shiga da ita dakin mutum dayane ga gado ga tv harda fridge sanan akwai bayi aciki, ahankali ya dauketa sabida dinkin ya daurata akan gado yadan sake kallon fuskarta kafin yajuya yafita dan zuwa dauko wani rigan asibiti danna jikinta duk yabaci da jini, tsayawa chak yayi yay folding hanunshi akirji jin yanda Abban shi ke tonamai asiri a hospital.
Dariya Nurse Sameera da Dr Ibrahim harma da Moses sukayi, Nurse Sameera tace "habawa no wonder naga Dr was extra careful sai lallabata yake kaman Kwai shida baya wani lallaba patients, ashe matar shi ce" Abba yawani kara washe baki yace "biki ma har yana neman wata biyu" Dr Ibrahim yace "lallai nema shine koya fadama" daure fuska yay yazo zai wuce wajen ya shiga theater Abba ya fizgo shi, kaman zaiyi kuka yace "Pops kaga kadena badani a wajen aiki, ni kuma zo kutafi please" ya karashe maganan kaman zai mutu sabida haushi, Big Mummy tace "dont mind them boy kuzo mutafi" ta kalli Abba tace "mu barshi yay aikin shi da kyau gaskiya Alhaji". Kaman zaiyi kuka ahankali yace "stop calling me Boy in front of them big Mum" rufe baki big Mummy tai da sauri tanaso tai dariya aiko duka wajen aka kwashe da dariya, shigewa yay theater abinshi Abba ya kalli Baaba da Mami dake zaune suna yar dariya suma yace "mutafi gida ki huta ga mijin tanan ai xai kwana da ita" hakanan suka tashi sukaje driver yajasu sai gida

Sabon kayan asibiti ya dauka ya koma dakin ya ijiye kayan akan gadon yana kallonta yanda fuskar ta yay fayau tsabagen wahala da kuka gakuma santala santalan cinyoyin ta dasuka bayyana, dan gajeren tsaki yaja yay gaban gadon yadan zauna ta baki bakin kafin yasa hannu ya dagota ahankali, dan igiyan bayan rigan ya warware yana wani ciccije lebe, sakin igiyan yayi kafin yakai hanunshi ta gaban rigar yawani ja rigar kasa da sauri ya saketa tafada gadon bam dudda cikin bacci take saida tadan yatsine, runtse idonshi yayi da karfi kafin yadan mikar da hannu yana kokarin ya maida mata rigar inyaso yafita yakira Sameera tasamata, neman rigar yake wacce ya zameta takai kan cikinta, hanunshi dayaji ya sauka akan kirjinta yasa ya matsa baya da sauri har yana bigewa da kujera yace "f*ck!" fita yay daga dakin da sauri kaman ana ingiza shi, yay hanyar office dinshi daidai lokacin Nurse Sameera tafito daga dakin wata patent daure fuska yayi yace "kije ki chanza mata riga" ahankali tace "to Ango" wani mugun kallo dayamata yasa tabar wajen da sauri tana gimtse dariya, office dinshi yakoma ya shiga ya rufe kafin ya wuce bedroom din ciki, bayi ya shiga yay wanka abinshi yafito daure da towel fridge din dakin yabude yadau Vita milk mai sanyi ya bude yakoma kan gado yana sha, agogo ya kalla yaga har daya nadare yawuce ma tsaki yayi dan bazai iya kiran Meram ba is too risky hakan yasa ya ijiye bottle din yakoma ya kwanta sai bacci ba zancen salla.

Wuraren 8:30 yatashi da kyar, ya shiga bayi yayo brush yay wanka yay alwala, yadau mai ya shafa sanan ya shirya cikin dogon black jeans da soft cotton t-shirt maroon bakaramin kyau yamai ba color, ya shafa man gashin shi dake karasa gashin kanshi kyalli sanan yadau turaren shi mai kama jiki ya fesa kafin yahau dadduma yay sallan asuban yana idarwa ya mike yana kallon agogo dan baida lokacin yin azkar, takalmi ya zira sanan yadau lab coat yafita once ya zagaye ward yaduba patients dinshi da yarinyar chan gida zai tafi ya huta tun jiya baihuta bafa.
Saida yagama duba patients sanan yawuce dakin datake tun kafin ma ya shiga yaji maganan su Abba, daure fuska yayi ya shiga dakin, Abba dake shirin fita shida Baba Sulaiman ya kalla yace "Morning Pops, morning Baffa" kanshi Abba yazo zai shafa da sauri ya doje dan bayason abinda zaisa yarinyar chan ta raina shi, Abba daya bishi da kallon mamaki saikuma yay shiru shida Baba Sulaiman suka kalli juna sukai murmushi Abba yace "muntafi office, anjima da yamma zamu dawo" daure fuska yasake yi yace "saikun dawo" murmushi Abba yay suka fita daga dakin Baba Sulaiman yace "daga zuwan matar shi yasoma girma bayason kana badashi, shiba yaro bane ba yanzu wayaga su Ayaan da iyali" dariya dukansu sukayi Abba ya gyara zaman babbar rigarshi yace "ai haka nakeso dama".
Chapter 31 · 0% Book details