← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 89

Sashe 17

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wuraren biyar da rabi ta shigo gidan nasu da sallama a gajiye, tun awaje take mamakin babar motar data gani a pake akofar gidan su, gashi kuma gidansu nawani fitinannen bakon kamshi, abakin kofar su ta zaunar ta ijiye jakan makarantar ta agefe tana kokarin cire takalmi da safa dan bama ta lura da takalman dake gaban kofar dakin Baba ba, cikin yar siriyar muryan ta ta kwalama Maman su kira "Mama nadawo" safan tacire tarike su ahannu tana kallonsu ganin sunyi datti yasa ta taka farar kafarta datama jan lallin salatef jiya dayay kyau sosai zuwa wajen botikin dake gefen rijiya ta wurga zafan tajuya zata shiga daki taji muryan Baba daga dakinshi yana kiranta. "Bilkisu" "Na'am Baba" tajuya zata tafi da sauri Raiyana dake falo zaune tace "Baby bakine fa kizo ki chanza kaya" turus tai a tsakar gidan tana kallon takalman da sauri tadawo daki hijabin makarantar kawai tacire sanan tadau pink hijab dinta data goge dake makale ajikin kusa tasaka, har kasa hijabin ya kaimata mai hula aiko bakaramin kyau yamata ba yafitar da baby face dinta sosai, ko silifas bata sakaba tai hanyar dakin Baba, abakin kofa tai sallama sanan ta shiga, gani tai kowa na dakin ita yake kallo banda mutum daya da kanshi ke kasa, murmushi tadan kakalo daya lobar da dimple dinta sanan ta shiga tsakar falon, dukawa tayi tafara gaida wanda bata ganin fuskarshi danya dukar dakai, sanan tadan matsa batare data jira amsar shiba ta gaida tsohon na tsakiyan su wanda tunda ta shigo yake kallonta yana washe baki ahankali tace "ina yini Abba" murmushi Abba yay yace "andawo yan makaranta Bilkisu ya karatu?" a kunyace ta sunnar dakai tace "Alhamdulillah Abba" sanan tagaida Baba Sule da shima ya amsa mata cike da fara'a kafin ta koma gaban Baba ta tsugunna kusa dashi tace "gani Baba" Baba da tunda tashigo yake kallonta yadan nisa yace "wajen ki akazo?" dan zaro ido tayi dan bataga wanda tasani cikin suba hakan yasa Baba ya gyara zaman shi ya fuskanceta da kyau yace "yaushe kika faramin karya Bilkisu? Maisa baki gayamin gaskiya ba ranan dakika zo kika karbi addu'an nan? Eh? Inda nasan gaskiyar zancen aidana hadaki dasu Isyaka kun kawoshi nadinga mai magani agida" rasa abinda zatace yasa tafashe da kuka mara sauti, jikinta ta har rawa yake tasa bayan hannu ta goge idanunta ahankali tace "Baba kayakuri, tsoro nakeji na dauka xakamin fadane" takarashe maganan cikin kuka, akaro nafarko kenan daya dago kai yadan saci kallonta da sauri ya kawad dakai kuma. Malam ya nisa yace "shikenan ya wuce haka Allah ya kaddara faruwan lamarin, gashin nan shida iyayen shi zunzo yimana godiya tun dazu ke suke jira ki dawo daga makaranta, daga kano suke"Juyo dakai tai tadan saci kallon su daidai lokacin shima yasake dago kanshi suka hada ido da sauri ta janye nata kirjinta na bugawa, yanzu wanne ne dama mahaukacin nan kai anya kuwa. Maganan Baba yadawo da ita daga duniyar tunani ya kalli su Abba yace "bari indan leka yaran nan Alaji" Abba yace "to Malam, saimun fito muma" fita Baba yayi Abba ya gyara zama ya kalleta yace "yar arziki Allah yamiki albarka y'ata, yabiya miki bukatun ki duniya da lahira, duk mai taimako baya tabewa ladanki na wajen Allah, Allah ubangiji ya baki duk abinda kikeso anan duniya da lahira banda abinda xan ce miki Bilkisu amma nagode, nagode, Ayaan yafadan mana abinda kika mai shine mukazo mu gode miki, Allah ya saka da alheri" wani irin kunya ne ya lullube ta mutumin da yamafi Baba tsufa ne yaketa gode mata haka lullube fuskar tai da hijabi kanta akasa hakan yasa Abba yay murmushi sosai ya kalli Baba Suleman yace "kaga yar albarkan kunyamu take ji, zomu basu waje sabida shima yamata tasa godiyar" yay maganan yana hararan Ayaan dake kallonshi kaman zaiyi ihu, fita sukai daga dakin sukai zaure wajen Baba, hakan yasa dakin yay shiru tamaki dago kai sai wasa take da yatsunta dasuka sha jan lalle a kumba.
Daga chan tsakar gida Raiyana ta kwala mata kira. "Anty Baby kizo wai" tashi tayi ahankali batare data kalleshi ba tafita daga dakin, Raiyana dake wurin zaure tace "Baba yace kikai mai charbin shi" tana fadin haka tafice daga gidan ahankali tajuya jiki asanyaye tai hanyar dakin Baban idanunta ne suka sauka akan Layla dake labe a kitchen tana mata game da waya, "lalala wayata Layla jeki ijiye kafin kija arufemin sim" tai maganan tana tafiya, tana kaiwa bakin kofar Baba takara juyowa ta kalli kitchen din dan taga ko Layla ta ijiye wayar ganin bata ganta ba yasa tahau kan dakalin da zaka tsallake ka shiga dakin Baba, ta kama labulen ta rike gam kafin ta daga kafa tana leken kitchen din ta window ko ta labene awani wajen, daidai lokacin shikuma yazo zai fita yasa hannu yakama labulen yaja zai bude, jan labulen dayayi yasa kafarta ta turgude tayo baya gabaki daya tafada jikinshi tabaya tareda sakin labulen yakoma jikin kofa, mugun firgitan datayi ne yasa takasa motsi saima sauke ajiyar zuciya datake yi jin kirjinta kaman zai fado waje gashi takasa juyowa takuma kasa barin jikinshi, kafarta datasha jan lallin salataf yabi da kallo yana kallon gashi gashin ta daya leko ta hular hijabin ta zufan datayi yasa sun kwanta luplup, yafita tsawo sosai hakan yasa har kwakwalwanta yana gani, hannu yasa ya juyo da ita atsorace ta kallai, daure fuska yay kaman baitaba dariya ba yace "banason rawan kai, ki natsu, karki sake barin irin haka yasake faruwa" yay maganan yana mata wani irin kallo sanan yawuce yafita daga dakin cike da izza duk takun dazaiyi saitaji a kirjinta harta dena ganinshi, tafi minti biyu a tsaye a wurin sanan ta share yan guntun hawayen dasuka zubomata ta rufo kofar tafito tai dakinsu.
Sai bayan sallan magrib suka tafi Baba yamusu rakiya har wurin mota sanan yakoma ciki, ba'a dadeba saiga amajirai sun kawoma malam manya manya ledoji da rapan kudi yan dubu daidai guda biyu malam baiyi niyar karbaba yafita waje da sauri dan ya maida musu amma harsun tafi haka yadawo yabama su Isyaka leda daya su rarraba tunda kayan kwalama ne dayan ledan kuma ya shiga gida dashi da kudin.

Abba ne zaune gefen Ayaan dayay bacci abinshi a dakinshi na hotel yay tagumi yana kallon fuskar Ayaan yayinda dayar hanunshi ke shafa kwantacen gashin shi, sosai ya zurfi a tunani hoton Balkisu yakasa barin ranshi, for d first a duniyar nan yaji lokaci yayi da Ayaan zai ijiye mata ya ijiye iyali zaizo yaga jikokin shi kafin yabar duniyar nan, yana mugun kwadayin ma Ayaan Bilkisu, yarinya hafiza, ga ilimi natsuwa da kunya ai itace tafi dacewa da Ayaan sanadinta hala ya natsu. Sai wajajen karfe daya sanan yabar dakin Ayaan din yawuce nashi.
Chapter 17 · 0% Book details