← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 89

Sashe 29

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read

Fita yay daga asibitin yaje wani eatry yaci abinci iya cinshi sanan yayo musu takeaway dan ita yanzu daza'ama operation bazata iya ciba, wuraren 7:30 ya shigo asibitin saida ya tsaya ya karbi report dinta yagama dubawa sanan ya kalli Nurse din wajen yace "set d theater" yawuce office din nashi, yabude ahankali tareda yin yar gajeren sallama zaune ya ganta akan gadon ta make da bango tana kuka kuka gyangyadi gyangyadi dan yanzu hakama bama taji shigowan shiba, juyowa yay yace "sannu Baaba" ya ijiye ruwa da takeaway din abincin agaban ta ahankali yace "Baaba ga abinci kici, nakira su Mami zasuzo sutafi dake gida kihuta dan theater zamu shiga yanzu, nariga naduba hoton da aka mata dole aiki za'ayi acire" tagumi Baaba tayi tace "oh ni Salamatu shikenan anjama yar karaman yarinya operation, duka duka sha takwas take fa, inda tunda cikin yafara ciwo Malam ya kaita asibiti ai da abu baikai hakaba, amma shi ina saida addu'a da magungunan hausa yarinya sai wahala take" dan murmushi yayi ya mike ya bude wani kofa ya shiga wani hadadden dakine ya bayyana, bathroom ya shiga yayo wanka sanan yafito ya shirya cikin wani green riga ta likitoci wacce ta tsayamai a cinya an rubuta Dr Ayaan ata wurin kan aljihun dakuma doguwar wando yasa hular kayan blue yadau wayarshi yafito yana kamshi daidai lokacin nurse din tai knocking office din afirgice ta farka tana kokarin bude idanunta duka, dan kallonta yayi kafin ya dauke kai ya kalli kofar yace "yes come in" shigowa nurse din tayi tana gunguro wani hadadden gado tace "sir everything is set" gyada mata kai yayi tareda nuna mata Bilkisu dake kuka wanan karan mara sauti dantai bala'in gajiya, ahankali nurse din tadafa Bilkisu tai murmushi tace "my shagwaba friend yama sunanki" cikin kuka ta turo baki tace "Bilkisu kuma niba shagwababbiya bace, ciwo yakemin saisa nake kuka ai" kama baki nurse din tayi dan tasan aikin ta ta iya lallaba patients tace "ai yama rage ciwon tunda gashi baki ya bude, dazu ko uppan baki cewa sai uban ihu dakike mana kunenmu duk ciwo suke yanzu" kara matso wasu sababin hawayen tayi batare datace komiba, hanunta nurse din takama tana dariya Baaba ma dariya tai tace "Bilkisu uwar raki" nurse din tanuna Baaba tace "nuna mata keba mai raki bane taso kihau gadon da kanki" baki Baaba ta rike jin dariya na neman fitomata Bilkisu dai data sani inbadai tadane jin zafin gabaki daya bane shine zata mike da kanta amma inhar tanaji ko kankanu ne wlh bata mikewa, kallon Baaba tayi idanun nan sai shining suke sabida hawayen daya cikasu da sauri Baaba ta mike tsaye tana lullube fuskarta da hijabin ta tace "ke nifa ba dariya nake ba haba mai gadon zinare yar wajena guda" karaf suka hada ido da Ayaan da tuntuni yake tsaye yana daddana waya kaman da gaske nanko kallon su yake kawad dakai tayi kafin ahankali tai yunkurin mikewa tsaye ihu sosai tayi. "wayyo Allah na Mama" komawa tayi zata zauna da sauri nurse din tarike ta daurata akan gadon ta kwantar, fashewa tayi da kuka sosai danji tayi gabaki daya wurin yafara wani sabon ciwon dan dan baccin datayi yasa ya lafa amma yanzu yafara, gungura ta nurse din tayi suka fita daga dakin, dan murmushi yayi yatura wayar aljihun wando ya kalli Baaba yace "ki zauna anan, zaki iya shiga ciki kiyo alwala idan zakiyi salla su Abba nanan zuwa saiku tafi tare dan bansan lokacin dazamu fito daga operation dinba" kaman Baaba zatai kuka tace "to dannan ubangiji Allah yasa ayi a sa'a, Allah yabata lpy Allah kuma yabaku nasara" Ameen ya amsa ciki ciki sanan yabude kofa yafita.
Chapter 29 · 0% Book details