Sashe 4
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Wuraren takwas da rabi ta shigo dakin nasu lokacin su Layla harsun dade da tafiya makaranta, Mama tasamu tana linke kaya afalo adan tsorace ta wuce uwar daka doguwar riga ta dauko daga ghanamasgon ta na atampa kore sanan ta ciro milk hijabi daya kaimata har kusan kasa ta saka tafito tasami Mama a inda ta barta ahankali tace "Mama zanje gidan Baaba daga nan sai Muji ya kaini na dauko jakan na kai kudin" batare data kalleta ba tace "saikin dawo" fita tai daga dakin koda tafita waje gidan Baaba tacema Baba zata hakan yasa baihanataba. Samun Baaba tayi agaban murhu tana dafa dafadukan shinkafa da wake "Baba ina kwana, naga keken Muji a waje ina yake?" kallon fuskar ta Baaba tayi tace "ya zaga bayan gida yanzu zaifito, maiya sami idanunki sukai jajir haka" zama tai gefen Baaba ta goge hawayen dataji ya gangaro mata tace "faduwa nayi nabar jakata wurin kuma akwai kudin Mama aciki datace nakaima Balaraba dillaliya" cikeda damuwa Baaba ta kada kai tace "to Allah dai yasa kisami kudin ajakan yanda duniya tabaci yanzu, kai Muji ina kake ne fito ka kaita kafin rana tayi kowa ya fito ayi gaba da jakar, a ina kika fadin?" ahankali tawani narke ma Baaba tace "ahanyar makaran tarmu jiya da yamma" daidai nan Muji yafito daga bayi tareda ijiye butar hanunshi nan gaban rijiya Baaba tace "oya zoka kaita ta dauko jakarta" ta kalli Bilkisun tace "kin Karya?" girgiza mata kai tayi Baaba tace "karya to saiku tafi" girgiza kai tayi arude tace "a'a nidai samin akula naci acikin keke napep" tashi Baaba tayi ta dauko wani kula adaki ta fito ta bude tukunyar ta deban mata shinkafa da waken dayawa ta rufe tabata tace "ki tabbata kincifa kinsan cikin ki baison yunwa" ta kwalama Muji daya shiga daki abinshi kira "wai mekake yi aciki ne?" fitowa yayi rike da key ya kalleta yace "muje" tashi tsaye tayi rike da kular ta suka fita waje keken suka shiga ya tada yace "a ina ne kika yarda jakan?" tagumi tayi gabanta na faduwa tace "chan ta wuraren school dinmu, tafiya suka dingayi har sukakai wurin suka shiga layin har zuwa karshen layin adaidai ta bakin bolan tasa yay parking duk suka fito, komawa bayan Muji tayi ta labe hakan yasa ya juyo ya kalleta yana nazarin fuskarta yace "me wai? Ina jakar to? Uban meme kikazo yi anan wajen bola wakika gani anan?" nuna mishi ginin tayi tace "yana cikin nan jakar kuma wani mahaukaci ne aciki, ni tsoro nakeji ka shiga ka daukomin" tafashe da kuka, tsaki Muji yayi yajuya yana kallon ginin yay hanyar shiga tana biye dashi abaya ko ina na jikinta narawa, tsayawa Muji yay abakin kofa yana kallon mahaukacin dake sanye dawani bakin riga t-shirt daduk ta barbarke dakuma dogon wandon jeans dashima dukya barbarke, sai yago fallen littafin ta yake yana turawa abaki yanaci, jin Muji ya tsaya yasa tadan leko ta bayan shi dan taga meyake kallo, sosai taga mahaukacin yanata tura paper abaki yana taunawa daga gani kasan yunwa yakeji wani irin mugun tausayin shine taji ya shigeta saisa ashe jiya yaje ya sato buredi, da sauri ta juya takoma keken ta dauko kulan abincin da Baaba ta bata dabata tababa tadawo tabi ta gefen Muji ta shiga ciki jikinta na rawa, nesa dashi ta tsaya ta bude kulan abincin tana bashi amma ko kallonta baiyiba saima tauna takardan dayake yi abinshi, kara matsowa tayi ta mikamai har lokacin bai kalleta ba, tunawa datayi jiya yanata buga kula a bango yasa ta buga marfin kulan a bango yay kara sosai, da sauri taga yadaga kai yana kallonta wani irin faduwa gabanta yayi dum! Amma duddu haka saida ta mikamai abinci tanadan kwanto da kulan sabida ya hango abinda ke ciki, baiyi ko motsi ba saima kallonta dayake tayi yana sosa kunne, ahankali tadan tsugunna taga yabita da kallo takara nunamai kulan amma baikarba ba kaman ma baigane metake cewaba hakan yasa ta daga hannunta na dama ta nunamai sanan tasaka hannun a kulan ta debo abincin ta nunamai sanan ta kai bakinta tasaka aciki tana taunawa tanamai murmushi atsorace, da sauri taga yataso yayo kanta da gudu ta matsa baya ta jingineni da bango kaman zata shige zuwa yay gabanta ya fizge kulan da karfi harsaida abincin yadan zube ya zauna nan gabanta ya daga hanunshi shima sama ya nunamata kaman yanda tayi sanan yasaka akullan ya debo yakai bakinshi yafaraci da sauri da sauri murmushi taga yayi daya bayyana dimples dinshi daduk jikakken paper ya makale akai yacigaba daci kaman zai hada da kulan sai kallonshi take a tsorace jikinshi fatar jikinshi duk baki baki kaman mai aiki a gareji.
Shigowa Muji yayi yazo kusa da inda take a makale a bango ya tsaya tareda rike kwankwaso yana kallon mahaukacin hakan yasa mahaukacin ya ijiye abincin yayo kan Muji yana daga hannu zai dakeshi da sauri Muji yakoma baya yana kakkare fuskarshi da hannu, dariya mahaukacin yayi sosai sanan yay wani irin tsalle ya dira agaban kulan yacigaba dacin abincin, da sauri ta mike tsaye kudin Mama dake tsakar wajen ta tsugunna ta dauka tareda tattare littafan ta tasaka ajakar ta kalli Muji daketa kallon Mahaukacin tace "mutafi" hararan ta Muji yayi yace "sannu to kulan Baaba fa" kallon Mahaukacin tayi taga yanda yakecin abincin rabi na zuba ajikinshi "Ke kalli wuyanshi" maganar Muji ne yasa ta janye idonta akan mahaukacin ta kallai ya nuna mata wuyan mahaukacin yace "jibi wanan ba sarka bane a wuyanshi ba, rigar jikinshi tadan rufeshi" yay maganan yana dan matasawa kusa da mahaukacin tareda dan tsugunnawa yana leken wuyanshi dake cikin chain daketa sheki da sauri Muji yace "innalillahi ke Balkisu wlh sarkan zinare ne, zokiga, zomu ciremai naje kasuwa na saida Allah yabamu, munyi kudi" hararan shi tayi tareda jan tsaki bata tanka maiba saima tsugunnawa datayi tana kokarin daukar byron ta dake kasan wurin, Muji ya kalleta kafin ya maida dubanshi ga mahaukacin yace "Allah kadaima yasan meya haukata shin, halama irin yan iskan yaran nanne inbahaka ba meyake yi da sarka yana namiji, yan iska kesa sarka fa irin mawaka da yan party dinan" cikeda masifa tace "nidai baruwana na, baruwan ka da sarkan shi kasan ko garin hauka yasamo, kokuma ya fizgema wasu" hararan ta shima yayi yace "tunda baki da hankali ba, ta ina mahaukaci zai iya saka sarka da kanshi? Eh fadamin ta ina zai iya saka sarka harma ya boye ta tacikin riga, nidai cirewa zanyi? Dan nasan karshen ta wasu su kwacemai" "sata fa kenan Ya Muji ittakulla" karan yarda kulan da mahaukacin yayi yasa Muji yatashi da sauri yakoma baya itakuma tai hanyar waje tafice da gudu, tashi tsaye mahaukacin yayi yafara tsalle tsalle yana gudu yana zagaye wajen da sauri Muji yadau kulan yafita yana waigen mahaukacin.
*wai meke faruwane a novel dinga?*
*waye wanga mahaukaci?*
*waye mutumin nan da Dr ke kanshi*
*waye sangartattcen?*
Wanan shine last free page, idan har kanason cigaba da karanta wanan labarin dake kunshe da abubuwa da dama mai nishadantar da kayatar da zuciya zaku iya tuntubana ta watsapp number na kaman haka 07012181461.
Hanyoyin biya biyu ne kota kati wanda zaki tura MTN 200 ta number nan 07032934950 kokuma ta banki 3107021073 first bank aisha Muhammad.
Labarin ga kuwa yanxu bama komi akeyiba kudai kubiyoni kucigaba da karatu❤
[7/15, 12:17 PM] Ummi Tandama: ♦♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦♦
Maman Abd Shakur
4...
Free page
Alluran bacci Dr yasake mai sanan yay bacci, matar takara fashewa da kuka, Baba Sule da Security suka fita daga dakin dan zuwa police station danjin ya ake ciki.