← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 89

Sashe 39

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Yay kusan minti biyar idanunshi arufe jikinshi ko ina na rawa bai taba ganin abu hakaba in his life kafin ya bude idon ahankali yana bin dakin da kallo, ganin kaman tanamai gizo a ido yasa ya fasa ihu. "Popsy" ya sauka daga gado da gudu yafita daga dakin yay downstairs, tana cikin bargo taji ihunshi tafashe dawani irin dariya tana taushe bakinta dudda yanda kirjinta ke bugawa amma bakaramin dariya tayiba. Haka ya zauna a falon ya kalli nan ya kalli chan sai kiran sunayen Allah daya dade bai kiraba yake dan wlh ya tsorata har ranshi, haka ya zauna a wurin yana istigifari har aka kira sallan asalatu mikewa yayi da sauri ya shiga bayin falon ya dauro alwala tsabagen yanda yake tsoron dakinshi yasa yakasa komawa, car key daya bari anan center table yadauka yafita tsakar gida yabude mota yanada wasu kaya awurin yadauko jallabiya yadawo daki yasaka sanan yafita shine harda tashi mai gadi su tafi masallacin tare, akan kunenta yabude kofa yafita aiko bakaramin dadi abin yamata ba harda sujjada tana godema Allah, ta shiga bayi ta dauro alwala tazo ta tada salla, saida gari yay haske sosai wuraren 9 sanan ya shigo gidan daga masallaci sama yatafi ahankali saida ya bude dakinshi ya dade abakin kofa yana kallon dakin kafin ya shiga ya kwaso kayan dazaisa yaje asibiti dasu sanan ya sauko kasa ya ijiye kan kujera, abayin falo yay wanka ya shirya yafita agurguje dan yay latti kuma yanada aikin dazaiyi.
Wuraren biyar na yamma yadawo gidan dauke da leda ahannu, bataji dawowan shiba tana zaune afalo cikin riga da sket na atampa tai nisa cikin karatun novel awayanta taji ana kokarin bude kofa, tashi tai a tsorace zata gudu dan gani take kaman yana ganin idonta zai gane itane aiko garin gudu ta bige da kujera, ihu tai ta rike kafarta daidai lokacin ya shigo dakin da sauri ya karasa gabanta yana kallon fuskarta dan ya dade bai ganta ba, ahankali ya tsugunna yana duba karfar ganin babu wani ciwo dataji yasa yace "mesa kike gudu" anatse kaman ba shiba, girgiza mai kai tayi tana hawaye gabanta na faduwa gani take kaman idan suka hada ido zai gane itace ta tsorata shi jiya, sakinta yayi ganin yanda jikinta ke rawa kafin ya ijiye ledar daya shigo dashi akan center table ya nuna mata da hannu yace "dauka kitafi dashi" ledan ta kalla kafin ta kalli fuskarshi saiyanzu ma talura yau babu sarkan babu dan kunen akunenshi ya kwanta tareda lumshe ido kaman mai tunani, da sauri tadau ledan tai sama da gudu bude ido yay kadan yabita da kallo kafin ya sauke ajiyar zuciya ahankali.
Tana shiga daki ta rufo kofanta ta zauna akasa ta bude ledan, ice cream ne manya manyan roba gudu uku different flavors, murmushi tayi ta gyara zama ta dauko daya daga cikinsu coconut flavor tahau sha tana lumlumshe ido, kasa shanye wa tayi ta ijiye agefe tana murmushi, ana kiran magrib taji yabude kofa yafita hakan yasa ta sauko ta saka ice cream din a freezer sanan takoma sama tai alwala tai salla ana kiran isha ma tai alwala tai salla tai karatu kafin ta tashi ta shiga bayi tai wankan dare tazo tasaka rigar baccin ta iya gwuiwa ta kwanta abinta tareda saka alarm yau biyu da rabi.
Alarm na tashin ta ta jawo kayan ta saka ta malka uban hoda a fuskarta dayama fi najiya tana dariyan keta dudda yanda kirjinta ke bugawa, fitowa tai Sadaf Sadaf kaman wata mayya ta bude kofar dakinshi bata ganshi ba hakan yasa ta fito tunawa da dazu a falo taga ya kwanta, tana hawa stairs ta ganshi ko akan doguwar kujera yana bacci awahale daga ganinshi kasan bai dade dayin bacci ba, sakkowa tai sadaf sadaf tana tattare rigar dan karya zubar da ita hartazo gabanshi ta tsaya tana kallonshi kafin takira sunashi. "Ayyyy yaaa nuuu" afirgice ya farka dan dama bacci baidade da saceshiba dan kasa bacci yayi tun bayan yadawo daga sallan Isha'i, a tsorace ya mike zaune ya makale jikin kujera yana kallon aljannar mai dogon gashi, ga gashin ta yakusa kai ciki, kara matso wa tai tana mimmikar da hannu kaman zata kamoshi, ihu yayi yana kokarin mikewa daga jikin kujera yace "wlh na riga na tuban ma Allah" wlh takusa dariya amma ta daure kirjinta na dukan uku uku tace "kaaayiii salla yauuuu?" gyada kai yayi yama kasa magana da sauri tace "in har ka kara aikata wani aiki na zunubi bazamu barka ba, rufe idonka lokacin bacewata nakoma duniyar mu tayi" ta dakamai tsawa dawani irin murya, da sauri yarufe ido jikinshi na rawa aiko ta juya da gudun bala'i tai sama batare data bari kafarta yay karaba, ahankali ta bude kofar dakinta ta shiga ta mayar ta rufe ahankali sabida karyay kara, ta cire rigan da sauri tana goge hoda fuskarta da ita kafin ta tunbuke gashin ta dukunkune su tare ta turasu karkashin gado tahau gado da gudu ta ja bargo tarufe tana dariya kasa kasa tana dafe kirji sabida yanda yake beating fast.
Yafi minti goma kankame da idanu ya rirrike lumtsa lumtsan filon kujera kafin ya bude idon ahankali yana kalle kallen falon ganin babu aljanar ta bace yasa ya mike tsaye da sauri yay sama, dakinta ya bude ya shiga arude, abirkice ta yaye bargo tana zazzaro ido da hawaye har yacika su dan tazaci yagano itane ke tsorata shi, shigowa yayi yana kallon dakin ko ina a gyare sai kamshin turaren wuta yake maida kofar yayi yarufe yazo yahayo gadon ya kwanta batare daya cemata kala ba sai ajiyan zuciya yake saukewa, a tsorace ta zabura ganinshi kusada ita zata sauka daga gadon ya riko hanunta yajawota yasata ajikinshi batare dayace mata kalaba ya kankameta yana ijiyan zuciya, tana iyajin yanda kirjinshi ke bugawa fatfat, kankametan dayayi yasama ko kwawkwaran motsi takasa sai hawayen wahala data farayi ahaka bacci yay gaba da ita, kasa bacci yay saima kara kankametan dayayi yanamai jin natsuwa ya sumbaci goshin ta yay istigifari akan kura kurenshi da laifuffukan dayama Allah swt.
Ahaka wahalallen bacci yay gaba da shi ana kiran assalatu ya bude ido tatas ya sauke su akan fuskarta duk ta takure ajikinshi tana bacci yafi minti goma yana kallon fuskar ta kafin ahankali ya ijiyeta agefe kaman yana ijiye Kwai, bayinta ya sauka ya shiga, ko ina kwalkwal ga kamshin dayake bayan yagama abinda zaiyi yafito daure da alwala, da bismilla yafita daga dakin yana Kalle Kalle gani yake kaman witch din zata fito, yay maza yafita daga gidan ya tada mai gadi atare suka tafi masallacin.
Wuraren 9 ya shigo gidan dauke da kayan dazaisa daya dauko daga mota har bayason kallon doguwar kujeran da witch din tazomai yanakai jiya, yay sama da sauri ya bude dakinta ya shiga bata ciki hakan yasa ya ijiye kayan akan gado ya shiga bayi yayo wanka yafito daure da pink towel dinta yafara shiri yana cikin kulle boturin hannu riga ta bude kofa tana ganinshi ta juya da sauri batare datama shigo dakinba zata tafi ahankali kaman ba Ayaan din daba yace "dauko min takalmina adakina" hannu tasa ta taushe bakinta jin dariya yazo mata aranta batare data juyo sun hada ido aranta tace "ashe akwai abinda zai iya chanza ka mugu" dakinshi ta shiga tana kalle kalle dan bataga takalmi ba.
Chapter 39 · 0% Book details