← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 89

Sashe 16

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Parking Muji yafara yi kafin babbar jeep dinsu kirar range rover tai parking, Muji ne yafara fitowa kafin Abba da Baba Sulaiman, gaban motar Abba yabude ganin baida niyyar fitowa ya kalleshi yace "fito mah boy" fitowa yay sai wani cin magani yake, Abba yasa hannu yacire shegen bakin gilashin dake idonshi tareda turawa a aljihu, Muji ya kalli Abba yace "bari nagaya mai" shiga zauren yayi almajiran dai sunata karatu sai kallon su Abba suke, karasa wa zauren Muji yayi ya tsugunna agefen malam dake biyama wani karatu saida yagama sanan ya dago kai yace "Mujittapa ba'aje sana'a bane yau" dariya yay yace "Baba baki nakawo ma, kai ake nema suna kofar gida" Baba ya mike tsaye yace "muje" fita sukayi daga xauren shida Muji, Abba na ganinshi ya washe baki dudda zai girmi Baba bai hanashi dukawa ba lokacin daya mikomai hannu, shima Baba kunya yaji ya duka ya karbi hanun nashi suka gaisa, sanan ya mikama Baba Suleman hannu suka gaisa, bugeshi Abba yay tabayan shi hakan yasa yamikama Baba hannu yanadan murmushin dabaikai ciki ba yace "barka da warhaka" karba Baba yay cike da fara'a dudda dai bai sansuba amma yaga kaman daga gani dan tsohon nanne, ya kalli Muji yace "shiga gida kace su gyara zan shigo da baki" da sauri Muji yajuya yay cikin gidan yayinda Malam yajuya aka cigaba da gaishe gaishe kaman ansan juna, Muji yafito yace "Baba zaku iya shiga" Malam ya kallesu yace "to Bismillan ku" Muji ne yafara gaba Baba biye dashi abaya sai Abba daya fizgo hannun Ayaan da baida niyyar zuwa sai kallon almajiran yake kaman baitaba ganiba, daure fuska yay yabi Abba suka shiga zaure ya nunama Abba allo yana wani yatsine fuska yace "wats dat Pops" gaba Abba yay abinshi ya barshi tsaye yanata kallon bangon da yaran daketa kallonshi suna washemai wani harda lashe majinan daya fito daga hancin shi da sauri yajuya ya tabe baki kafin yabi bayan Abban nashi dayaga ya bude kofa suka shiga cikin gidan dake a gyare tsaf dashi, simintin sai kyalli yake, babu kowa a tsakar gidan sai kamshin turaren wuta mai dadin kamshi dake tashi, iso Malam yamusu afaddadden falonshi dake gyare tsaf an shimfida babbar tabarma a tsakiya duk suka zazzauna sai bin dakin yake da kallo yanda yaga littatafai kala kala sun cika bangon dakin an jerasu kaman mesuim, Baba ya kalli Muji tareda ciro kudi a aljihu yace "jeka sawo ruwan gora" ganin yanayin su na yan gayu ne, da sauri Abba yace "ina ga randa nan ina gani kawani ce ruwan gora malam, ban yarda ba gaskiya" yay maganan yana nuna randar dakin yana dariya, tashi Muji yay yadebo ruwa ya cika babbar jug din malam mai tsafta yadaura akan tray dinshi sanan ya sanya kopuna biyun a kai yakawo musu Abba ya karba yana washe baki diba yay yasha Baba Sulaiman ma yasha ruwan dadi ga sanyi, tsiyayawa Abba yay ya mikama Ayaan dake gefenshi duk atakure, murmushin dole yay yace "ina azumi kamanta ne Popsy" shanye ruwan Abba yay sanan ya ijiye cup din, Baba yay murmushi yace "Masha Allah sassannun ku da zuwa saidai ban ganekuba wlh" Muji ne yadawo kusa da Baba yace "Baba uhm dama" saikuma yakasa magana Baba yace "ina jinka" ahankali Muji yace "Baba dan Allah kayakuri daga ni har Bilkisu bamu fada muku komi akaiba, dama akwai wani.. ...." nan Muji yafadi ma Baba komi, Abba ya chabe da. "Malam babu abinda zamu iya ce muku sai ubangiji Allah ya saka da alheri yakuma biya bukata yakara daukaka ka, ai da Ayaan yafada mini shine muka shirya tundaga kano mukazo neman ku, munsha wuya kafin mu gano nan, Allah ubangiji ya biya muku bukatun ku duniya da lahira, yanda kuka taimaki dana kuka sani farin ciki ubangiji Allah yasaku ku farin ciki ranan gobe kiyama, watana daya da kwana goma sha biyu banga Ayaan ba rana daya kawai yadawo ta sanadin ku, nagode nagode malam" murmushi Malam yay yace "Ameen Alaji mugode ma Allah, a'aa ikon Allah kaji magana fa, shine kuma yaran nan sukamin karya, inda ace Bilkisu tafadamin ai danasa ma har gida anje an dauko shi namai addu'a nabashi magun guna anan, to ubangiji Allah ya kara mana katanga da makiyan mu, ko lokacin dana bata addu'an nace mata inhar sihiri ne dazaran yasha zai karya ashe kam sihirin ne" Abba ya girgiza kai cike da damuwa yace "bamusan waye ke neman shi da shairi hakaba, amma muna kan rokon Allah daya bayyana mana gaskiya" Baba yace "ai wanan ba matsala bace zan bashi addu'o'i dazai dingayi kullum safe da maraice in sha Allah babu abinda zasuyi dazai kara kamashi da izinin Allah kuwa dan kariya ce" Abba da kaman yazuba ruwa akasa yasha yace "mun gode, mun gode akaramakallahu, Allah ya biya bukata" sukadan yi shiru shidai Ayaan kanshi akasa Allah Allah kawai yake Pops yagama surutun shi sutafi, gashi yakasa daddana waya hakanan yaji malam ya cikamai ido, maganan Abba ne yadawo dashi daga zancen zucin dayake yi. "Malam ina diyar naka Bilkisu zanzo mu ganta mu kara yimata godiya idan ba damuwa" murmushi Baba yay yace "tana makaranta chan dogon bauchi, dayake na rana takeyi sai biyar da rabi zata dawo" Abba yay shiru chan yace "inba damuwa zamu jirata tadawo Malam" Malam yace "babu komi ai tama kusa tunda gashi yanzu hudu saura" nan fa hira yakachame tsakanin Abba da Malam da Baba Suleman kaman sunsan juna ataba nan ataba chan, suna yin la'asar Muji yamusu sallama yatafi nan Umma ta gabatar musu da abincin da aka dafa musu farar shinkafa da jar miya bayan ta gaisa dasu ta fita, abincin su Abba sukaci sosai abinsu dan wlh yay dadi.
Chapter 16 · 0% Book details