← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 89

Sashe 62

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tsaki tayi tasa rigan tana maganganun ita kadai, tazo gaban madubi man data gani ta shafa sanan takoma wurin abincin kunun tasha sosai taci ships da egg sanan ta tashi tana kalle kalle dakin zama tayi akasa tunawa da sweetheart tafashe da kuka sosai. "sweetheart ina kake? Inane nan daka kawoni wurin mutanen nan da mutumin nan, please come back, wayyo Allah na Anty Ummy" kuka tasha sosai dan kanta tagaji ta share fuska saikuma tafara tsalle tsalle har falo, wurin TV tai dan kunna ta kalli cartoon amma tayi tayi tayi ta kunna TV takasa hakan yasa ta cigaba da tsalle tsalle tahau wanan kujeran ta dirko tahau wanan saikuma tai hanyar kofa dazai fitar da ita daga dakin dayar fingilar rigar jikinta mara hannu gashi iya guiwa ta tsaya mata kanta babu dan kwali sai kitson nan guda biyu bude kofa tayi tafita tana tsalle tsalle, workers biyu ne kawai maza a part dinshi dake watering flowers daya kuma na rage tsawon su da almakashi. Sai guje guje take abinta tana on ur mat get set ready go, taje ta taba wanan bangon sanan tadawo wanan bangon, gashi tasa over size slippers dinshi a kafarta daya mata yawa sosai. Workers din kuwa hankalin su nakan aikin su sunayi suna hira sama sama.
Tana cikin gudun ta timm tafadi guiwan ta daya ya gurje wani irin ihu datayi yasa ma'aikatan suka fito da gudu sukayo kanta ta baje akasa ta dago kafarta daya tana duba guiwar tana kuka tana yarfe hannu dan gurjewa ma tayi kadan amma take uban ihun nan, daya daga cikin sune yace "sannu tashi ki shiga ciki" hararan su tayi ta make musu kafada, dayan kuma yabita da wani irin kallon maita ga rigarta tadanja kasa dan kana ganin cleavage dinta, wanda yay maganan ya kalli dayan dayake kallonta yace "wuce mutafi Musa" da sauri Musan ya tsugunna ya mika hannu zai taba kafar yace "mugan kafar" daidai lokacin Ayaan yashigo part din hanunshi daya rike da babban teddy bear red me gashi dayan hanun kuma white leda ne dake dauke da different snacks, tsayawa yay chak yana kallonsu yanda suke kallon mai mata barinma na tsugunnen. Washe baki Musa yayi yace "haba mana kibari naduba miki ciwon kefa me kyau ce" make mai kafada tayi tana kuka ta matsawa baya tana hararan shi, dayan yace "Allah baka sa'a nidai kaga tafiya ta" yajuya zai koma wajen plant Ayaan daya gani a tsaye yana musu wani irin kallo da idanunshi dayay jajur yasa bakinshi yafara rawa yanason yakira sunan Musa amma yakasa, wani irin watsar da kayan hanunshi dayayi sukai kara shi yasa daga Musa har ita suka dago kai, arude Musa ya mike tsaye ya kalli dayan da shima jikinshi ke rawa yake yace "kai nafasa aikin, nabar aikin, natafi" da sauri yajuya yazo ta gefen Ayaan zai wuce da gudunshi, wani irin fizgo shi da Ayaan yayi saida rigar jikinshi ta yage, bugashi yayi da bango bamm, yawani irin shake shi, dayan na ganin haka da mugun gudu yazo yabi tabayan su yafice, yanda taga Ayaan ya shake shi mutumin na neman mutuwa yasa ta mike tsaye tana zazzaro ido jikinta ko ina na rawa, wani irin duka Ayaan yarufe shi dashi a zuciye yana buga bayan shi da bango. "uban wayace ka kallan min matata? Uban wayace ka kalla min mata ta har kasan ita mai kyau ce ko dan ubanka, yausaina tsiya yar da idon daka kalleta dasu" kamo wuyar shi yayi yana neman kai hanunshi cikin idanunshi, idan kaga Ayaan zaka rantse mahaukaci ne, fashewa tayi da kuka sosai tsabagen yanda ta tsorata tazo wurin ganin kokarin budemai ido da mutumin ya runtse gam yake, tabaya ta rungume shi sosai jikinta na wani irin rawa tafashe da kuka tace "please stop am scared" yanda ta daura hanunta akan kirjinshi yasa wani irin shocking ya shiga jikinshi, da sauri jikinshi ya saki hakan yabama Musa dayaji jiki a hanunshi ya fizge kanshi ya gudu da kyar, yunkurin binshi yayi tai baya zata fadi da sauri ya fizgota azuciye, kankame idanunta tayi a tsorace, ya tsugunna yadau teddy ta da ledan ya fizgo hanunta yabude daki ya shiga da ita.

Wani irin jefata yay akan kujera da idanunshi dasukai kaman banashi ba yace "uban wayace kifita ahaka, kinja wasu maza sun kallan min ke eh, bakisan da aurena akan kiba, u are my wife, my property, am ur husband" make mai kafada tayi tana kallon dan gurjewan datayi tace "ni banda husband, kuma ni sweetheart zan aura dankaji, nasan yau zaizo ya dauke ni mubar muku gidan ku, ni banason nan gidan ma nafison gidan sweetheart dina, farm house dankaji infad..." wani irin tari dataji yanayi yasa ta daga kai ta kalleshi, dafe kirjinshi yayi numfashin shi na neman barin kirjinshi yana kokarin saita kanshi yana tari kaman mai asma, arude ta mike tsaye tana kalle kalle, ruwan data hango kan fridge ta dauka da sauri ta juyo kafin ta karaso ta bashi har ya zube a wurin asume".
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

73...

*dake nake, kedai wanan rubabbiyar me hanun tantabara dazata marking ta fitar dashi waje, da idanun kaman na agwagwa, maicin amana dai yay asara, yar air mekama da macen bera, yama sunan macen bera ?? Beratu kawai*

Tsugunnawa tayi ta kwalalo ido waje tana kallonshi ganin ko numfashi bayayi, arude ta daura hannayen ta akan kirjinshi tana dukanshi. "kai, kai, wai bazaka tashi ba, bude idanun ka" girgiza shi take sosai amma ko motsi bayayi, fashewa tayi da kuka ta mike tsaye tana kalle kallen dakin tarasa abinyi, bottle water data dauko ta ijiye kusa dashi ne tagani hakan yasa ta tsugunna da gudu tana kuka tadau ruwan ta bude takai bakinshi cikin kuka tace "dan Allah kasha to katashi kaji, to bazan kara fitan ba, amsa" jijigashi takeyi ruwan akan bakinshi amma baiko motsa, mistakenly garin jijigashi yasa ruwan ya bare mai a fuska daga hanunta, wani irin ajiyan zuciya ya sauke batare daya bude idanunshi ba hakan yasa tafashe da mugun kuka tace "kai kabude ido nace, yakuri to" labban shi dataga yabude yanason yay magana yasa takai kunenta saitin bakinshi da sauri, murya chan chan ciki yace "press my heart" da sauri ta daga kanta ta daura hannuwanta ata saitin zuciyan shi wanda baya bugu da kyau ta daura ta danne da duka karfin ta tana kallon fuskarshi, ganin har lokacin babu wani chanji yasa tasake danne zuciyar, jin still batajin bugun zuciyan sosai yasa ta daddage tai nai uku tana kallonshi, ajiyar zuciya ya sauke sosai tareda bude idanunshi kadan ya kalleta, fadawa tayi kanshi tafashe da kuka tace "kai bazan karaba" saikuma ta dago kanta ta kallai Ita yake kallo asanyaye da idanunshi dasuka kankance tace "u are sick ina maganin ka na dauko ma" shiru yayi yana kallonta, share kwallan daya zubo mata tayi tace "ina maganin ka" shiru yayi yana kallonta da idanun nan dasuka kankance suka chanza kala, matsawa tayi ta jingina da kujeran ta cusa kanta akan guiwowinta tafashe da kuka sosai tace "ni nagaji da gidan nan, anata dukana, anata dambe da mutane har ana kwakule ido ma, tunda nazo tashin hankali nake gani, am tired, Sweetheart kazo ka tafi dani, where are you sweethea..." kasa karashe maganan datake yi tayi sabida yanda Ayaan yataso ya daura kanshi shima akan guiwanta duk yanda yaso ya daure yakasa wani irin nishi yake bakinshi na rawa yace "dan Allah, dan Allah Baby, I know you are not well but pl..." saikuma yay shiru jin yana neman yakara sumewa sabida yanda zuciyarshi ke wani irin gudu, arude ta dafa kanshi tace "kai wai me haka mutuwa zakayi? Na shiga uku Sweet..." fadawa yayi jikinta ya kankame ta sosai yanason yay magana amma yakasa ajiyan zuciya kawai yakeyi, yanda taji zuciyarshi na wani irin beating ba kakkautawa yasa tace "u heart is sick" saikuma tai shiru tana sauraron yanda jikinshi ma yadau rawa kodai ba mutum bane dama gashi fari kaman aljanin zabiya da Anty Ummy tabata labari, ahankali ta shiga tureshi daga jikinta muryan ta narawa tace "sas..sa..sakeni inje induba ko sweetheart yazo mutafi" wani irin matseta yayi ajikinshi yanajan numfashi ya chusa kanshi awuyan ta kirjinshi nawani irin bugu yafashe da kuka sosai yama kasa maganan, itama arude tafashe da kuka so kawai take ta kwaci kanta daga wanan kwakumetan dayayi, cikin kuka tace "sakeni inje in duba swe..." kara fashewa da kukan da yana ganin rabonshi da yin irinshi tun yana yaro, shi karan kanshi baze iya explaining yanda yakeji aranshi inda takira katon nanba, zata sake magana ya daga hanunshi ya kyar ya daura akan bakinta ya shiga rera mata wani irin kuka mai tsinkar da zuciyar mutum, da kyar ya iya controlling yanda zuciyarshi ke bugawa ya bude baki cikin kuka yace "p..pl...lz..stop calling dat name wlh zan iya mutuwa, am begging yhu baby dan Allah ki tausaya min, am suf...fering" shi kanshi baisan meke damun shi ba, yanda yake reramata wani irin kuka irin na sangartattun yaran nan mara kara awuya, hawayenshi har gangarawa suke yi daga wuyanta zuwa kirjinta, da sauri ta hadiye nata kukan taji yawani irin mugun bata tausayi duddu bata gane takamai men meke sakashi kukan ba, amma saitaji tana wani irin jin tausayin shi ahankali tace "to nadena amma nadinga cemai uncle to" runtse idonshi yya da mugun karfi wasu hawayen sharr nazubo wa shi gabaki daya bama yaso yaji tana maganan wani namiji ne aduniyan nan, shiru itama tayi jin yanda hawaye ke gangarawa jikinta, ahankali ta sakala hannayen ta ta daura asaman kanshi ta shafa mai alamun lallashi, wani irin ajiyan zuciya ya sauke yakara kankame ta da kyau ya lumshe ido, tun tana sauraron yanda heart dinshi ke beating da mugun fast har tazo tajishi yasoma komawa dai dai ahaka itama wani wahalallen bacci yay gaba da ita.
♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

74 - 75
Chapter 62 · 0% Book details