← Book details Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 89

Sashe 24

Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*kano*
Cikin bacci yaji Abba na bugamai kafa bude ido yayi yaga Abba ya shirya cikin hadaddiyar gizna shadda ga uban malum malum yace "jekai wanka harda kai zamu zaria bikin Bilkisu, kawani kwanta kana bacci kasan karfe nawa?" turo baki yayi Abba ya tallabemai keya ahankali yamike ya shiga bathroom.
Fridge harda su washing machine Abba yasai ma Bilkisu zai bada as gift su Mami dakuma big Mummy dasuma zasu zaria suka hada mata atampopin da lace harda turarurruka duk sunci gayu sunyi kyau. kusan 20 minute sanan yafito fuskar nan adaure, ya sanya sky blue shadda dake kyalli tsabagen kyau ya kafa wata hadaddiyar hula aka yana tafiya daidai sai uban kamshi yake. gaban mota ya shiga driver yajasu sai zaria, matayen suka fara kaiwa gida Malam ya kira Mama tamusu jagora ciki sanan Malam yama mazan jagora zuwa massallacin jumma'an dake anguwan su, bayan anyi sallan jummu'a duk aka natsu a massallaci wanda malamai da dama abokanen malam sun halarta, saikuma Isyakan dayay kyau yasha yar farar shaddar shi ta daidai kudi da mutanen shi danhar baban shi yazo daga sokoto, gakuma daliban malam gasu Abba agefe kusa da malam sai murmushi yake dudda har cikin ranshi yaso ace Bilkisu rabon danshine. 🎤 limami ya rike ya kalli Baba yace "ina angon da iyayen shi ku matso sabida adaura" tashi Isyaka dake sahu nabiyu yayi yazo gaba shidai Ayaan sai binshi yake da kallo yana wani irin tabe baki, microphone din Isyaka ya karba daga hannun limamin yay murmushi yace "inada wata yar sanarwa ne" mikamai limamu yayi ya e bismilla, karba Isyaka yayi sanan ya gyara tsayuwa ya kalli Malam da yayan shi dama duka mutanen dasuka cika masallacin makil, yay gyaran murya sanan yasake kallon malam da murmushi kekan fuskar shi yace "Allah gafarta malam gaskiya nidai nafasa auren, banison yarka Bilkisu, kayakuri bawai cin mutunci bane amma bani sonta ko kadan nafasa auren, na fasa" ya ijiye microphone din yafita daga masallacin ta kofar inda liman kejan sahu, nan fa masallaci ya kacame da surutu baban isyaka yatashi yabi yaron da sauri amma harya hau mashin yabar wajen.
Wani irin matsiyacin murmushi Ayaan yayi ya kalli fuskar malam dahar wani zufa ke ketomai, dawowa yay kaman mara lpy ma su Abba se baki suke bashi, hanun Baba Suleman yaja hakan yasa Baba Suleman dake magana dago kai ya kallai, kara janshi yayi hakan yasa yamike ya bishi abaya suka fita waje Baba Suleman yace "wai wani irin iskanci ne wanan kana ganin babanta baida lpy ne kake jawoni waje, ba yanzu zamu tafi ba leave me" Baba Suleman yay maganan cikin fushi, kaman zai mutu dan bakin ciki yadai saita kanshi yace "Baffa nizan aureta kafada ma Pops adaura auren dani dama saisa nakira ka waje nafada ma" da mugun mamaki Baba sule ke kallonshi yace "kace me?" murmushin yake yay yace "adaura dani" da gudu Baba sule ya juya yay cikin masallacin shikuma ya dunkule hannu ya daki iska. "f*ck wlh zakici ubanki ne ahannuna" azuciye ya shiga masallacin ya hango Baba sule nama Abba magana akunne tashi Abba yay tsaye yazo inda yake tsaye yace "son are u serious?" murmushi yama Abban ya gyada kai, kamashi Abba yayi yamai peck a goshi tsabagen farin ciki, kafin yajuya da sauri yakoma gaban masallacin yadau mike ya tsaya yace "asaurara jama'a, asaurara" shiru akayi duk aka maida hankali kan Abba, yay murmushi ya kalli Baba yace "dama muntaba zuwa neman ma dana auren Bilkisu amma munyi latti lokacin, to gashi dannawa har yanzu yace yana ciki fa, alfarma muke nema ataimaka mana abamu malam" "Allahu Akbar" kawai aketayi a masallacin malamai nata kabbara suna cema malam "Allah ya fitar dakai kunya" wan Baba ya kalli Malam dayay shiru yace "kabasu Bilkisu tunda danshi na sonta kaga munfita kunya" murmushi Baba yay ka kalli Abba yace "na amince kuma nabaku ubangiji Allah ya sanya albarka" zokaga murna wajen Abba da Baba Suleman kamoshi Abba yayi ya zaunar dashi kusa dashi nan fa aka gyara zama liman ya daura aure tsakanin AYAAN ABDULRASHEED DA BILKISU ABDULBASY akan sadaki dubu dari da hamsin.
[7/15, 12:21 PM] Ummi Tandama: ♦♦ *SANGARTATTCE* ♦♦

Maman Abd Shakur

29 - 30

Bayan Mama ta kaisu dakin Umma dan nanne ba jama'a sosai sai gaishe gaishe suke sanan Umma ta kwalama Layla kira yarinyar ta shigo da gudunta ta sanya yar atampa ta mai kyau ja ta anko, Umma tace "yi maza jeki kira Bilkisu tazo ta gaishe da baki ai kinsan inda take paty ko?" yarinyar ta gyada kai tana washe baki tana kallon su Mami dasukai shigan alfarma sunyi kyau da sauri ta juya tafita daga dakin, wani gida dake nan kusa da gidansu ta shiga gidan Mrs Alkaleey matar amarya ce badai kirki ba tanason Bilkisu saisa ma tace "tazo itada kawayen ta suyi party anan" da gudu ta shiga babban falon inda kawayen Bilkisu yan dogon Bauchi suka cika ko ina su Fa'iza, Fateema, Walawa, Aisha Shehu, Maryam Umar, Fadila, Bass, Maymuna, Hajjaju, Zainab, Reemar, Hajaea gasunan rututu dai ancika falon Mrs Alkaleey sai hira ake anacin shinkafa da salad ana hiran samari da first night, ganin bata falo yasa tai hanyar bedroom din Mrs Alkaleey kwankwasa kofar tayi akace ta shiga, turawa tayi ta shiga ciki, baki tabude tana kallon Yayar tata da Dr Binta ke kokarin zage mata zip din jan lace dakeda ratsin baki din jikinta, ga Maryam Gafai agefe tana kokarin nada dankwalin da za'a daura mata, takowa tayi tazagayo ta gaban ta ta tsaya tsabagen mamaki hannu tasa ta kama bakinta, Mrs Alkaleey tace "rufe mana bakin ke" washe gibi tayi tace "wlh Anty Baby kinyi mugun kyau" murmushi Bilkisu tayi daya lobar da dimple dinta takara kallon fuskarta ajikin madubi dudda kayan data saka na daidai karfi ne, dan wanan lace din ma Baba ya saimata bai hana kyawunta yafito ba, Maryam Gafai ta rangada mata ubansun dauri, an mata riga na sket da ja da bakin lace din da akama aiki awuyan rigan, tasaka bakin takalmi hill da kuma bakin jakarta mai kyau, an saka mata wani hadadden sarka barawon zinare da dan kunen shi da warwaro harda ma zobe, gashi Dr Binta ta chanchara mata makeup da tunda take bata tabayi ba, anyi parking gashinta anmata donut a tsakiya sanan akai daurin dan kwali mai step aka fito da gashin ta tsakiyan daurin. Tsarki ya tabbata ga ubangijin dayay wanan hallitar! abinda su Reemar keta fadi kenan lokacin data fito falo, Walawa tace "gaskiya Isyaka yau zai sha dadi, anya xai sarara miki kuwa yau idan ankaiki? Kinyi romo romo da yawa yar malam" tai maganan tana wani irin shu'umin murmushi, Fadila tace "koma kakide kakide ne tayi mudai gobe da sassafe zamu faso gidan muzo mu ga yanda take tafiya" dukansu suka fashe da dariya, zama tai akan kujera hawaye ya taru a idanunta sosai zatai kuka dan haka nan taji wani irin kuka takeji duk hankalin ta atashe yake, dafata Mrs Alkaleey tayi tace "karki biye musu kinji ki bata kwalliyar ki, inhar kikai musu kuka haka zasuyi ta zolayar ki" Laylah data kasa dena kallon yar tata tace "Anty Baby Mama ce tace nazo nakira ki wai kinyi baki" ihu dakin ya dauka Bass tace "an daura, an daura su Isyaka ne, tashi kije yar malam amuku wa'azi tare" kaman bazata tashi ba saikuma ta mike tsaye, Raiyana ta dauko bakin gyale mai kyau ta daura mata akai share dan kwallan dataji ya zubo mata tayi ta kalli Reema tace "muje ki rakani" tashi Reema tayi tadau gyalen ta saba akafada suka fita bayan ta kara jan gyalen ta tarufe fuskar ta.

Tunda suka fito daga gidan kanta ke kasa sabida yanda taga maza sun cika layin alamun andaura auren kenen, ahaka har suka shiga cikin gidansu aiko ana ganin ta matan dasuka cika tsakar gidan suka hau guda ayyiririri ga amarya ga amarya, kara lullube fuskar ta tayi har suka shiga dakin Umma da Layla ta nuna musu, Umma ce dake daga bakin kofa ta yaye mata gyalen data rufe fuska dashi tace "ai sai abude fuskar ko tunda kin shigo amarya, ga baki kinyi daga kano iyayen Ayaan ne" dukda bata gane waye Ayaan din da Umma ke fadi ba hakan bai hanata dago kai ta kalli manyan mata biyu dake zaune akan doguwar kujeran ran Umma da aka wadata su da abincin biki agaban suba suma ita suke kallo a kunyace ta dukar dakai ta tsugunna tana wasa da hannayenta dasuka sha lallin amare ahankali tace "ina yinin ku Mumy kunzo lpy" atare Big Mummy da Mami suka amsa mata da lpy lau tareda yima ta godiya akan abinda tama Ayaan, sai a lokacin ma tagane ashe iyayen mara mutuncin mahaukacin nanne, suka mata fatan alheri tareda addu'a zama lpy duk kanta nakasa dan bata yarda sun sake hada ido ba dan kunyan su takeji sosai, Mami ma takasa daina kallonta har kasan ranta takeji kam inama ace Ayaan ya sameta din ya aura da tai farin ciki sosai yarinya mai natsuwa haka da kunya. Ganin takasa tashi yasa Umma tace "to tashi kuje ku koma wajen kawayen ku" ahankali ta mike tsaye tadan kallesu kafin tasake dukar dakai tace "mungode Mummy Allah kiyaye hanya" tajuya da sauri tafita Reema tabiyota abaya tana murmushi suka fito zaure zasu fita waje, tsayawa tayi tana kara lullube fuskar ta da gyale sanan suka fita suka koma gidan party.
Chapter 24 · 0% Book details