Sashe 54
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Ko minti talatin baiyi ba ya dawo ya paka motar shi a tsakar gidan, tun daga waje yakejin kukan ta girgiza kai kawai yayi ya bude bayan motan ya dauko katoton babban leda daya siyo mata kayan sawa na mata, sai kuma ledan take away ya dauko yay hanyar cikin gida dashi da sallama ya bude kofan ya shigo falon da gudun ta tafito daga uwardakan tana sanye da doguwar rigar atampa ja daga gani zainab ce ta bata kayanta, tazo da sauri tana kuka ganin shirin fadawa jikinshi take yasa ya juya da sauri yay facing kujera yana daura ledokin akan kujera hakan yasa ta tsaya abayanshi tana goge kwalla, ahankali ya juyo ya sauke idanunshi akan fuskarta yanda hawaye ke gangarowa yanabin kuncinta, anatse yace "mesa kike kuka" hanyar uwardaka ta nunamai daidai lokacin Zainab tafito tana kokarin saka hijabi kayan jikinta duk sun jike, yace "ita ta jikaki haka zainab?" dariya zainab tayi tazo wajen tace "ihu tadinga yi wai bazata yi wankan ba dana hada mata ruwa shine ta dinga zubamin da kyar dai tayi, Uncle wlh tanada kyau bakuwar nan naka ya sunanta?" da sauri itama Bilkisu ta kallai tanuna kanta tace "ya sunana uncle?" dauke kai yayi dan idanunta namai wani irin ya zauna akan kujeran yadau leda daya na take away ya mikama zainab a kunyace ta karba tana godiya, da sauri ta zauna kusa dashi harda leka fuskarshi dago kai yayi ya kalleta hakan yasa ta washemai fararen hakoran ta, dan murmushi yamata yana mamakin ta, tuntsirewa tayi da dariya takara matsowa kusa dashi tace "ya sunana?" Ahankali yace "kinaso na baki suna?" da sauri ta gyadamai kai tana washe baki lumshe ido yayi kafin ya budesu yakara daurasu akanta yace "okay dagayau sunanki Ameerah" da gudu ta mike tsaye tana tsalle "yeeeee Ameerah, Ameerah" ta kalli Zainab data tsaya tana kallon ta tana yaba kyanta aranta ta murguda mata baki tare da hararan ta turo baki tace "sunana Ameerah ko Uncle" daga mata kai yayi Zainab tace "Uncle natafi" kudi yabata taki karba tafita da sauri.
Ahankali yabude dayan ledan dayan take away yaciro jellof rice ya kalleta inda take tsaye tanata kiran kanta da Ameerah tana juyi ahankali yace "Ameerah" da sauri ta dago kai ta kalleshi tareda washemai baki abincin ya nuna mata hakan yasa tazo ta zauna kusa dashi yasa mata spoon yabata tafara ci saida taci kusan rabi ta ture tana yatsine fuska, maganin ta yabata da ruwa tasha da kyar tasha sanan tadau abincin tanaci tana wasa dashi shikuma chatting yake a watsapp da Dr Ameenu, kanta dayaji ya kwanto akan kafadar shi yasa ya dago kai ya kalleta tai bacci ga takeaway akan cinyarta shinkafan dukya zuzzuba akan rigarta yakai kusan 5 minutes yana kallon fuskarta kafin ahankali ya janye kafadar shi ya gyara mata kwanciya akan kujeran tareda karbe take away ya kakkabe shinkafar jikinta acikin roban yawuce yakai kitchen sanan yadawo ya zauna kujeran nesa da ita yana kallon fuskar ta, addu'a kawai yake ko ina iyayen ta suke Allah ya bayyana su.
*kano*
Ahankali Abba yay sallama ya turo kofar dakin Bilkisu wanda Ayaan ya mayar nashi, abu dayane ke fitar dashi daga dakin shine salla ko wani irin zazzabi yake saiya tashi yana dafe bango yatafi masallaci. Mami itama ta tare gidan dan kula dashi, Big Mummy kuma takoma gida sabida bakuwar ta Munari wacce yanzu take neman kusan sati hudu da zuwa kenan amma dai kullum saitazo ta duba Ayaan. Shigowar Abba kenan bayan ya raka Dr Ibrahim dayazo dubashi dan anyi anyi dashi yaje asibiti yaki.
Ahankali Abba ya zauna kusa dashi akan gadon hanunshi rike da tray na abinci dan yau throughout yakicin komi, dafa goshin shi Abba yayi hakan yasa yadan bude idanunshi da sukai jajir, gashin shi da gemunshi sunyi busu busu, hannu Abba yasa ya taimaka mai ya tashi zaune ya jingina da gado, Abba yace "zoka ci abinci Boy so kake ka kashe kanka wai, dare da rana police nakan case dinan, nasa amana rokon Allah, in sha Allah, Allah zai bayyana mana gaskiya, da kansu zasu dawo da ita" Abba yay maganan yana mika mishi bowl din pepper soup, ture bowl din yayi da hannu ya dau pillow ya rike muryan na rawa yace "bazan iyaci ba, tana chan hala ma basu bata abinci ba halama sunata dukan tane yanzu haka, kullum da tunanin ta nake wuni na tashi Pops..." yanda muryan shi ke rawa yasa Abba ya jawoshi jikinshi yana bubbuga bayanshi kafin ahankali ya ciroshu yama forehead dinshi peck yace "za'a ganta da izinin Allah yanzu dai ko 3 spoon ne kasha kaga zaria zani inaso naje nasami mahaifin Bilkisu, yakamata susan wats going on, idan bamu fada musu ba bamuyi adalci ba" dafe kanshi dayakeji kaman zai fashemai yayi Abba kaman zaimai kuka yace "sannu Boy oya sha sha saika sha magani" da kyar ya bude ido ya karbi coffee da Mami tasamai madara, saida yasha sanan Abba ya lullube shi da bargo yafita baitaba sanin haka Boy keson Bilkisu ba, driver yajashi sai zaria.
Kiran sallan la'asar ya farkar dashi daga baccin wahalar daya dauke shi da kyar ya sauko daga gado ya shiga bayi yaje ya dauro alwala yafita daga dakin a stairs ya hadu da Mami ta hado abinci a tray zata kawo mai da sauri ta ijiye tray akasa ta rikeshi ganin kaman zai fadi, kaman zatai kuka tace "ina zaka ahaka Ayaan kana layi?" da kyar ya ware idonshi ya kalleta yace "masallaci zani Mami" girgiza mai kai tayi tace "Ayaan no mukoma daki kayi achan u don't look good, baxaka iya zuwa masallaci ba" ahankali yace "zan iya Mami please ki barni nasan nama Allah laifuffuka da yawa, cikinsu harda rashin sonyin salla, amma yanzu in sha Allah ba ciwo ba koma me saina je masallaci" ahankali ya zame hanun daga nata yana tattaba karfen stairs ya sauka kasa Mami tabishi da kallo da sauri ta share hawayen daya zubomata suna ganin jarabawa.