Sashe 48
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tun kafin yay parking take kallon daya daga cikin securities din gidan data ganshi kusa da flowers din gidan ya tsugunna ya rike wasu maguna masu kyau farare guda biyu, kana ganinsu kasan yarane ba'a dade da haihuwar suba ya kafa kansu acikin wata yar karaman bowl suna lasan madara daya dama musu, parking yayi a inda ake parking motoci ya kashe motar har lokacin waya yakeyi wacce bamatajin abinda yake fadi sosai bata damuba tabude kofar motar tayi ta sauka, ko rufe kofar batayi ba tana tafiya ahankali tana dan dingisawa ahakanma wai ta saita tafiyan sosai tai wajen magunan yabita da kallo ta madubin mota, tsayawa tayi agaban security dake basu madaran tana kallon fararen magen tana murmushi ahankali tace "naka ne? Sunada kyau" security dasai a lokacin ya lura da ita dan hankalinshi yay nisa akan magunan yace "barka da zuwa madam" ganin magen taketa kallo yasa yay murmushi ya shafa kan daya daga cikinsu yace "kin gansu nan Mamar su itake tayani gadi duk randa nake duty shine fa last week data haifesu ta mutu wlh banji dadi ba" kaman zatai kuka tace "to ka saka musu suna?" girgiza mata kai yayi hankalin shi nakan wacce tadena shan madaran, da sauri tace "ka samusu Sameer da Sameera tunda naga ai mace da namiji ne ko?" dago kai yayi yasake kallon fuskar ta yana murmushi yace "eh" ganin yanda gabaki daya hankalin ta yana kan magunan yasa yace "kozaki dauke sune" da sauri ta gyada mai kai tana murmushi ta mikomai hannu tace "dan Allah kaban daya natafi da ita gida" daidai lokacin shima ya mikomata magen harta daura hannunta tadaura akan magen gyalenta ya sauka daga kanta yakoma kafada sabida iskar dayakada kawai karan saukan mari sukaji, Ayaan ya tallama security wani hadadden Mari wanda yasa shi sakin magen arude da sauri ta rike magen karta fadi kasa ta karye jikinta na rawa ganin tsantsan bala'i a idonshi, kama kwalan rigar shi Ayaan yayi yana jijjigashi "dan ubanka ubanwa yabaka izinin magana da Matata eh" arude security kanshi akasa yace "sorry sir" tureshi Ayaan yayi da karfin tsiya saida yakusa fadi ya nunashi da yatsa da tsanin bacin rai yace "u are fired kabar gidan nan yanzun nan" security nabashi hakuri ko kallonshi baiyiba yajuyo ya kalleta da jajayen idonshi, gabaki daya jikinta rawa yake, fizgota yayi da karfin bala'i yana maida gyalen da sauri ta saki magen tai tsalle ta shige cikin flowers shikuma yay hanyar shashin Mami rike da hanunta, arude tace "dan Allah kayakuri karka koreshi" wani irin mugun kallo yamata zuciyar shi natafasa dan jiyake zai iya kashe koma waye yaga yana kallonta koyi mata murmushi (to fah, mutumin naku wanan kishi haka).
Fashewa tai da kuka sosai ganin yanda yake kallonta kaman zai daketa, dunkule hanunshi yayi ya daki jikin bangon daya jinginata akai kafin ya daka mata tsawa. "shut up and wipe those tears" da sauri ta share hawayen tass sanan yarike mata hannu suna tafiya ahankali ya bude kofar suka shiga ciki ganin kowa na falo zazzaune akasa anata hira, ana ganinsu kowa ya washe baki yana kallonsu yasa tafara kokarin fizge hanunta sabida tsananin kunya da nauyin su Abba datakeji shiko ko ajikinshi saima tafiya daya fara ahankali sabida ita sukai cikin dakin itama tabishi ta daddage iya karfin ta ta saita tafiyar ta sabida kar agane, daidai wajen Mami yasaki hanunta ganin wani irin kallo datake mai da sauri ta tsugunna ta wajen kafan Mami dake kan kujera tana gaida kowa kanta akasa.
Sun jima afalon suna hira itadai tana kusa da Mami kanta akasa shiko yana jikin Abba sai shagwaba yake zubawa, Abba na wani irin riritashi kaman kwai, akai akai yake satan kallonta. Big Mummy ne ta tashi bayan wayarta yay ringing ta kalli Mami tace "Munari ta iso bari naje" murmushi Mami tamata tace "tadan huta tukun anjima na shigo mu gaisa nima" to Big Mummy tace tafice daga dakin sai Mami ta kalli Bilkisu datai shiru ita kadai ganin mazan duk sun natsu kallon news suke yasa Mami tace "tashi muje sama daughter" ahankali ta mike Mami ta kama hanunta da kanta dan tun shigowan su tagane komi sama sukayi yabisu da kallo asace.
Suna shiga dakin Mami tai kasa zata zauna hararan ta Mami tayi tace "kinga zamu batafa in kinamin wanan kunyan niba maman ki bane?" gyada mata kai tayi tana dan murmushi gado Mami ta nuna mata tace "to tashi daga kasa ki zauna akan gado" ahankali ta tashi ta zauna Mami kuma tafita daga dakin tace "ina zuwa" Mama Jummai tabama kudi ta aikata wani wuri cikin minti talatin saiga Mama Jummai tadawo da sakon karba Mami tayi takoma daki ta shiga bayi tahada mata ruwan zafi sosai dawasu magunguna aciki sanan tafito ta kalleta ahankali tace "daughter shiga bayi ki zauna a ruwan dana hada miki ina zuwa" Mami tafita daga dakin dan tabata sarari, kaman zata nutse da kunya haka takeji mikewa tsaye tayi da kyar ta shiga bayin kaman yanda Mami tace ta shiga ruwan bakaramin dadi tajiba ko, tadade aciki sanan tafito daure da alwala ganin ankira la'asar tana fitowa tazo tayi, ta zauna akan gado daidai lokacin Mami ta shigo ta mika mata wayarta tace "ga Baaba" cike da farin ciki ta karbi wayan Mami tajuya tafita, sun dade suna magana da Baaba kafin Baaba ta mikama Raiyana dake kusa da ita dukta dameta, da sauri Raiyana ta karba tai uwar dakan Baaba tace "Anty Baby labari zan baki" dariya Bilkisu tayi sosai tace "ina jinki bani nasha" Raiyana cikin murna tace "Anty Baby kinayin aure nafara samari daban daban amma duk cikin su nafison copper dake koyarwa a school dinmu kuma yazo wajen Baba yace zaima jirani har nagama ss3 kafin nan yagama service dinshi yasamu aiki, wlh Anty Baby ina sonshi" hanun mutum dataji akan cikinta yasa ta daga kai a tsorace wani irin kallo yake mata hakan yasa takasa magana ta sauke idonta kasa Raiyana tace "hello Anty Baby" zama yayi kan gadon ya dauketa yasata ajikinshi tareda daura kanshi ta wajen wayan, Raiyana tace "hello Anty Baby kinji labarin kuwa" da kyar tace "eh" kafin ahankali tace "ke kinji dadi ai kinsami wanda kikeso Baba kuma zai hadaki dashi, niko saidai naji sabon zance ranan bikina" da sauri ta share hawayen daya zubo mata ahankali tace "ki gaidamin da Mama da Umma" ta katse wayar da sauri tana wasa da yatsun ta kama hanunta yayi yana kallon fuskar ta yace "ke" kin dago kai tayi hakan yasa ya daura fuskar shi akan nata yana mata wani irin kallota yace "ke" bude kofar da akayi yasa yadago kai Mami ce ta shigo dakin dauke da tray ahanunta na abinci da sauri ta tashi daga kan jikinshi shima ya mike tsaye ya karbi tray yana kallon fuskar ta ahankali yace "sannu da aiki Mami na" nunamai Bilkisu tai tace "abincin tane" sai a lokacin ma ya kalli plate din tuwo ne da miyan kuka dayasha namomi tabe fuska yayi ya ijiye mata agaban ta, tana ganin abincin batasan lokacin data saki murmushi ba daya lobar da dimple dinta numfashin shi yakusa ya tsaya, ta kalli Mami data bude wardrobe kaman tana neman abu tace "nagode Mami na" yunkura wa tayi zata sakko kasa da sauri ya riketa dauke kai tayi ya saukar da ita kasan, zama tayi akasan ahankali ya dauko tray ya ijiye mata agabanta, shikuma ya kwanta akan gadon Mamin, wanke hanunta tayi da ruwan da Mami tasako mata atray din sanan tafara ci har wani lumshe ido sabida dadi gashi harda man shanu a kukan, juyowa Mami tayi ta kallesu kafin ta mayar da hankalin ta duka kan Ayaan dake kallonta kaman zai cinyeta itako bama tasan yanayi ba, dan gyaran murya Mami tayi tace "bakai da Abban ka zaku kai Baba Sulaiman airport bawai kazo ka kwanta anan?" dan sosa kai yayi yamike tsaye yace "na manta ma" fita yayi yadan saci kallonta sai tuwonta takeci.