Sashe 1
Sangartattce Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Compiled By Umar Dalha Funtua.
♦♦♦
*SANGARTATTCE*♦♦♦
Maman Abd Shakur
1...
Free page
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinkai.
"wayyo Allah na Baba mutuwa zanyi, wayyo Mama huramin cikin" mata biyune suka zagayeta akan tabarman dawasu yara mata guda biyu dake tsakar gidan dayasha simenti kal kal dashi duk sunyi zuru zuru, kana ganinsu kaga tashin hankali kwance akan fuskarsu, chan ta gefen tabarman kuma wajajen inda kafanta yake wani dan tsohone haka dake sanye da babbar riga dakuma yar hula daya zagayeta da rawani irin na malamai dinan ya rike kofin silver yakara abaki yanata addu'o'i aciki anatse, ihu takara yi ta dage rigarta sama tabude daidai cikinta dake nan kaman bata tabacin abinci ba, ta gefen haggun cikin ya dan kumbura idan kaga wajen saika rantse wani irin babban kurjine yafito ya kumbura haka yay ruwa zai fashe, ihu tasake yi tariko hannayen matan dake kanta tace "wayyo Allah Mamammu na shiga uku, azaba Mama wayyo, azaba yakemin" tasaki hanunsu tana ihu "Baba Baba baba kiranka nakefa, wayyyo Allah na ba banu ni" wani irin ihu take ta rirrike hannayansu gam tana nishi, wajen ciwon cikin kuwa sai balbal yake yanda kasan halita mai rai ne acikin wurin, duk ihun ta yacika gidan, tsabagen takaici ma daya daga cikin matayen wacce itace mahaifiyarta taja tsaki, hakan yasa dayar ta goge zufan datake yi agoshi, takamo fuskarta da hanunta tarike tace "haba Balkisu, iye mai gadon zinare, ki daure mana baga baban kinan namiki addu'a aruwaba, kefa mai dauriya ce, jaruma, kinga Layla da Raiyana zasuce ke raguwa cefa gashima sai kallonki suke" girgiza kai tayi tawani irin kece da kuka da ihu harda shesheka tace "ni kukiramin Baaba wlh, Baaba tazo, Baaba kizo ki taimakeni" tafara shure kafa idanun nan sunyi jajir tace "Baba, Baba, Muji, wayyo Allah na Mujittapa kuzo kutaimake ni, Shato kuzu dan Allah na shiga uku, wayyo Mama dubamin kiga kodai barkewa cikin yakeyi ne?" tawani irin buga ihu hakan yasa mahaifiyarta dake kanta ta buge bakinta da karfi tace "kewai baki iya kiran sunan Allah bane banziya kawai" daidai lokacin Baba ya cire cup daga bakinshi ya kalli Uwargidan yace "dagomin ita Zainaba" dagota tayi ahankali sai wani uban nishi take tana cije baki tace "tsaya tsaya uhmm" tsayawa tayi tana kallonta cike da tausayi, hannu budurwan tasa akan kafadar matar tareda runtse ido da karfi tana nishi tace "tona shirya" har Mama saida tasa hannu suka dagota zaune ahankali wani irin ihu tayi kaman zata mutu "ya isa, ya isa, yayi" suka jinginar da ita ajikin bango, kafamata kofin Baba yay abaki ta kurbi ruwan sosai tasha tana kara dage rigar atampan jikin ta sama, ragowan ruwan Baba ya debo yay addu'a zai shafamata akan kullutun da sauri tarike hanunshi tana ihu tana kuka tace "Baba wlh azaba yakemin, in kanama Allah karka tabamin, kaji dan yarasulullahi" hanunta Mama dake kanta ta buge tana wurga mata wani mugun kallo, hakan yasa Baba ya girgiza kai ya shafamata ruwan awajen tana wani irin shegen ihu da duk yacika musu kunne, tashi Baba yay ya kalli mahaifiyarta ya mika mata cup din yace "bayan awa daya kikara bata Amina, bari nakoma zaure wajen dalibai" jiki asanyaye ta karba tace "to malam" juyawa yayi yay hanyar zaure bude kofa yayi sanan ya daga asabari dazai sadashi da zauren yafita, almajirai ne cike a zauren sunata karatu da alo, ga wasu manya akansu dake rike da bulala suna lura dasu, bangon zauren duk jakunkunan almajiran ne dakuma taburmai dasuke kwana akai dan zauren nada girma sosai, daliban na ganinshi suka kara karfin karatun dasuke, fita yayi daga zauren zuwa kofar gida nan ma wasu almajiran ne akan simentin kofar gidan dayawa sunata karatu da alo, anyi babbar runfa daya kare kofar gidan sabida koda ana ruwan sama dan wasu almajiran anan waje suke kwana, ga robobin almajiran cike akan dankali dan dazaran karfe biyu tayi zasu tsaya sai ayi salla kowa yatafi bara, daga chan gefen kofar gidan kuma lungu ne dayasa suka gineshi dajar kasa aka zagaye suka maida bayi, anan almajiran suke wanka suke dai komi nasu sanan a kofar gidan akwai rijiya da guga dasuke diban ruwa, zama yayi akan tabarma da aka wareshi musamman tashi ce dan akwai yar dadduma mai taushi akai ya zauna tareda yin bismilla yanajan chasbaha, yana bin kowani dalibin dake wurin yana karatu da kallo, wani dalibi babba dan yana daga cikin wayanda ke kula da sauran almajiran ne yazo kusa da malam ya zauna tareda tankawshe kafa yadan dukar dakai yace "Allah taimaki Malam, Allah gafarta ma Malam, Allah kare mana Malam" ahankali Baba ya ijiye charbin ya kalli yaron yace "sun biya karatun da kyau Isyaka?" "i sunbiya Malam, na muhammadu ne kawai bai kawo da kyau ba amma nakara maimaita mai" murmushi Malam yayi tareda kishingida da bango yace "masha Allah to, daukomin Al Qur'ani na nabarshi a zaure saika biyamin naka inji" dan kallonshi matashin yayi saikuma ya sunkuyar da kai yace "Malam ya jikin Balkisun?" ajiyar zuciya Malam ya sauke yace "da sauki namata addu'a zata sami lpy nan bada jimawaba" cike da damuwa Isyaka yatashi yabar wajen zuwa zauren dan dauko abinda Malam ya aikeshi.
Gyangyadi tafara yi anan wajen a zaune, hakan yasa duk suka sauke ijiyar zuciya, Uwargidan dasuke kira da Umma tamike ta kalli Maman Bilkisun tace "sha biyu tayi bari na daura girki Amina" kallon yaran daduk sai kallon Bilkisu dake nan zaune tana gyangyadi suke tace "ai sai atashi aje ataya Umma aiki ko" hijabi Raiyana ta cire wacce ita kebin Bilkisu shekaran ta 15 tamikama Layla hijabin wacce take auta shekaran ta 8 tace "ungo kaimin daki" karba Layla tayi ta wuce dakin su ta ijiye tafito suka karasa kitchen din jajjage Umma tasa Raiyana itakuma Layla Umma tace "tahura mata wutar ta kama" tafice daga kitchen din zuwa tsakar gida dan tankaden tuwo.
Layla dake fifita wuta ne ta juyo ta kalli Raiyana dake jajjage, ajiye maficin tayi tazo kusa da Raiyana ta tsaya kaman zatai kuka tace "Anty Raiyana maisa Baba bazai kai Anty Baby asibiti ba, kinga ko koyau a makarantar mu anmana primary science fa, ance idan abu yafito acikin ka yay babba har yana motsi operation akeyi, Allah kuwa, Baba kuma yanata mata karatu tanasha da dafa mata ganye maisa bazaice aje asibiti ba" tunda take maganan Raiyana ta tsayar da jajjagen tana kallonta, Umma ne ta shigo kitchen din ta kallesu tace "surutun me kukeyi ba aiki nasaku ba?" baki Layla tabude zatai magana Raiyana ta girgiza mata kai hakan yasa tai shiru takoma gaban murhun tacigaba da fifita, abinda Umma ta shigo dauka ta dauka tafice daga kitchen din, hakan yasa Raiyana tadawo wajen murhun ta tsugunna tace "karki kara fadin maganan nan, Baba bai yarda da maganin asibiti ba kuma idan yajiki kinsan sauran, karki karayin maganan kinji" ahankali Layla ta gyada mata kai kowaccen su tacigaba da aikin da aka sakata.
Wuraren sha biyu da rabi ta farka azabure ta mike Mama dake zaune gefenta tana dama ma malam fura ta kalleta tace "ya cikin" hanyar dakinsu tayi ta daga labule ta kalli agogo sanan ta kalli Mama tace "Mama nakusa lattin makaranta shine baku tasheni ba" turo baki tayi tai gaban rijiya tadau botiki zataja ruwa, tabe baki Mama tayi tacigaba da dama furan ta, agurguje taje tayo wanka tafito daure da zani a kirji tashiga daki da gudu, uwar dakan su ta shiga dake nan agyare ko ina dan gado ne madaidaici sai ledan daki da aka shimfide, tsugunnawa tayi tajawo ganamasgo daga karkashin gado ta bude taciro kayan makarantar ta dake nan agoge, purple dogon wandon tafara sawa sanan tasaka rigar dayakai har gwuiwa fara tana dan bata fuska sabida yanda cikin ke mata ciwo kadan kadan yanzu ba kaman dazu ga, gaban madubi taje ta shafa farar hoda tasaka kwali, basilin ta lakato ta shafa akan pink and black lips dinta, dan lips dinta daga tsakiyar su pink ne sosai sai kasan kuma baki kaman ta shafa janbaki haka suke gashi sunwani irin tattare gwanin kyau and sexy, idan ka kalla kaman nama, komawa gadon tayi tasanya farin hijabin daya wuce gwuiwa, ta maida ganamasgo karkashin gadon tadau yar jakarta da litattafan ta keciki tafito ta zauna adakalin bakin kofa tana kokarin saka safa da takalmin makaranta Umma da fitowar ta daga kitchen kenan tace "Baby yaushe kika warke dahar zaki tafi makarantar allazi boko?" dan murmushi tayi daya bayyanar da beauty point dinta tace "Umma yafa dena fa wlh, kuma kinga nice monitor aji chalk natare dani dole nakai" baki Umma ta kama tace "su manito manya" dariya Balkisu tasaki harda fadawa jikin Mama dake kan tabarma tace "ana monito kina manito Umma" tacigaba da dariya kaman ba ita ke ihu dazuba, rankwashi Mama tasakin mata akai tace "tashi min akan jiki kafin na juye miki furan nan akan kayan makarantar nan" ahankali ta tashi kaman zatai kuka ta zauna kusa da ita Umma ta bude kullin zani taciro naira hamsin ta mikamata tace "gashi kihau mota, daga fillin mallawa zuwa dogon bauchi da shegen nisa keda baki da lpy" karba tayi cike da murna tace "nagode Umma na Allah barmin ke" komawa tayi kusa da Mama tana kallon furan, kaman zatai kuka tace "Mama dan sammin kinga ba'a gama abincin rana ba karnaje makaranta haka da yunwa" hararan ta Mama tayi tace "kwadayayya" dariya tayi tace "eh naji Mama kidan ban" da sauri ta shiga daki ta dauko karamin kofin roba Maman ta tsiya mata dan daidai ta shanye harda saka yatsa tana kakkale kofin ta lashe tass sanan ta ijiye kofin tana goge baki tace "nagode Mama natafi" da sauri tadau jakarta ta leka kitchen taga su Raiyana na kwasan tuwo tace "natafi" atare suka mata addu'a, Mama tace "salla fa?" "a school zanyi Mama" tabude kofa sanan ta daga asabari tafita.
[7/15, 12:17 PM] Ummi Tandama: ♦♦♦ *SANGARTATTCE*♦♦♦
Maman Abd Shakur
2 - 3