← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 90

Sashe 9

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ihu! na kurma! da karfin gaske! na kai masa duka! " Dan ubanka ba zaka sake ni ba."! nafada ina haurinsa da kafafuna! kamar maye ya ri'ke ni tsam! yana tsotsar kunnena da gefan fuskata sai so yake ya kamo bakina ina kaucewa.

Kuka na shiga yi ina rokonsa ya sake ni na tashi, da kyar yace."Kin amince da maganata."? Da sauri nace"Wace magana."? A shaqe yace."Ta aure mana." naji kamar ya watsa min wuta a jikina, domin ya sake ni nace na amince."

Ajiyar zuciyarsa naji kafin ya sassauta ri'kon da yayi min. nayi saurin fizge jikina na dira daga gadon ina haki da nishi! dakin na shiga bi da kallo! can na hango wayar da gwaggo take chaza redion ta, ita nai saurin daukowa na nannad'e ta a hannuna, a fusace! nayi kansa da duka! dirgowa yayi da sauri yayi hanyar fita yana dariya, hawaye na zubo min na bishi da duka amma ko d'aya ban sameshi ba abinka da d'an ball tsalle ya buga ya tureni ya fita daga dakin yana dariya.

Zubewa nayi a gurin na dinga kukan bakin ciki ina nadamar abinda ya faru a tsakanina dashi.....ya zama dole nayi nesa da yaron nan kada watarana ya haike min ya rabani da budurcina.

Da kyar na iya wanka nayi sallolina kana na d'ora farar shinkafa tunda inada miya dama haka nake sai nayi miya ta kwana uku ko hudu sai dai kawai na dinga amfanin da ita.

Agogo na duba karfe hudu da rabi na yamma babu labarin gwaggo, al'amarin ya dinga bani mamaki yana daure min kai, kasa daurewa nayi naje na samu Ummatu tana hidimar d'ora abincin dare nace"Ummatu dan Allah ko kin san inda Gwaggo taje.''?

Ba tare data dauki maganata da muhimmacin ba tace"Ni kam ban sani ba." a sanyaye na fito daga gurin wanda yayi dai-dai da shigowarta. hannunta ri'ke da leda viva.

Kallo na shiga bin ta dashi , ta wani sha kunu da fad'in "Meye kike kallona ko kin aike ni ne."? Nace." Gwaggo yanzu dan Allah sai da kika je."?

Shareni tayi ta shige daki, bayanta nabi naga tana kokarin d'aga gadon karfenta ina tsaye naga ta tusa ledar ciki ta mayar da zanin gadon ta rufe, nace"Ledar me kike 'boye."?

A fusace! tace."Sa'ida ba zaki daina titsiye ni ba ko."? Girgiza kaina nayi na rabu da ita, taja tsaki tare da daukar buta ta fita.

'Daure da alwala ta shigo dakin, na kalli agogo biyar shaura minti biyar nace."Gwaggo a'ina kika tsaya baki sallah ba duba kiga lokaci fa."

Ci kanki ba tace dani ba ta gyara dadduma ta tayar da sallah! ajiyar zuciya na sauke na fita daga dakin ina tunanin hanyar da zanbi gurin dauko ledar data 'boye a 'kar'kashin gadonta.

"Sa'ida idan kin gama abincin zubo min naci." muryarta naji daga cikin dakin tana magana. nace."Bangama ba tukkuna." Tace ."Salisu mai kanti ya aiko ko."? nace"Ban sani ba dan nima bacci nayi bayan na dawo daga makaranta.

Tace."To koma dai ya aiko to sai dai yayi hakuri dan yanda na gaji d'in nan bazan iya tsinana komai ba." Nace."Wai dan Allah gwaggo ina kikaje kada kice min kinbi Uwale gurin malami."

Shuru tayi bata tanka ba, sai nima nayi shuru na kyaleta, abincin na 'karasa dahuwa na zuba mata da yawa a plate nasa mata miya da kifi na kai mata.

Da sauri tace."Yawwa babbar mace nagode." ruwa na d'ebo mata na ajiye mata a gabanta na fita daga dakin, a nan tsakar gidan na zauna naci nawa abincin na gyara gurin tsaf na koma dakin.

Tace."Haba Jama'a yanzu naji dai-dai." shuru nai mata na cigaba da abinda nake, a nutse ta kira sunana, na juyo ina kallonta tace."Naji kina cewa malami me magani zaki ce dan mu ba gurin malamin zaure mukaje ba."

Nai shuru ina sauraranta ta cigaba da cewa "Na fad'awa mai magani duk abinda yake damunki kuma ya had'o miki magani Sa'ida inaso ki bani had'in kai dan Allah kiyi amfani da maganin nan domin hankalina ya tashi dana ji yace wai 'bakin aljani ne ya aureki shiyasa bakya so ayi miki maganar aure kuma shine yake shiga tsakaninki da Khalid kuyi ta fad'a kuna samun sa'bani wallahi Sa'ida bakiji yanda hankalina ya tashi ba."

Cike da mamaki nake kallonta kafin nace"Gwaggo nice nake da 'bakin aljani."? da sauri tace."Eh mana ko kina kokwanto ne."? nace."Kwarai kuwa Gwaggo ni ban yarda ina da iska ba saboda haka asarar kudin ki kawai kikayi."

Marairaice fuska tayi tace"Haba Sa'ida ya zakice baki yarda kina da iskokai ba yanzu shekarunki nawa a duniya kina zaune babu aure duk sa'onin ki sunyi aure sun haihu yaransu sun wayo amma ke kina zaune duk namijin da ya yun'kuro da niyyar auranki sai ya gudu ko kuma a d'aure masa baki a hanashi magana wannan fa duk sharrin iska ne."

Murmushi takaici nayi nace."Gwaggo ni abinda na kaddarawa rayuwata shine aure lokaci ne duk yanda naso da nayi aure idan lokacin baiyi ba dole na hakura kuma kina maganar cewa na girma nayi shekaru babu aure ai bani kad'ai bace akwai dubban matan da suke zaune babu aure da yawa daga cikinsu ma sunfi ni girma da shekaru saboda haka ki daina wahalar da kanki akan al'amarina duk ranar da Allah ya kawo lokacin aurena babu mahalukin daya isa ya hana."

Tace."Eh duk da haka Sa'ida bakiji bahaushe yana cewa idan kana da kyau ka 'kara da wanka ba ni na yarda da maganar mai maganin nan domin aljani yana da suddabaru iri-iri saboda haka dan Allah kada ki watsa min 'kasa a ido."

Murmushi nayi nace."Gwaggo kenan dan Allah ki bar maganar nan kinga lokacin sallah yayi kije kiyi alwala ki sallah ki roki Allah ya za'ba min abinda yafi alkairi."

Tace."Sallah ko kince nayi ko baki ce nayi ba dole nayi kuma Ubangiji shima ya fad'a cewa bawa ya tashi ya nema shi kuma sai ya taimakeshi." Nace"Gwaggo ba'a irin wannan al'amari Ubangiji yayi magana ba, Allah yace." Ko ro'keni ni kuma zan amsa muku amma bece wani bawan sa yaje gurin malamin duba ba."

A tunzure! tace"Wai Sa'ida waye yace miki gurin malamin duba mukaje."? Nace."Gwaggo dan Allah maganar nan ta mutu haka magani dai idan dan ni kike siyo to kinyi asarar kudin ki dan bazan sha ba."

Ina gama maganata na fita daga dakin na barta tana bina da kallo.

Bayan mun idar da sallar sai ta mike ta fita daga dakin minti biyar ta dawo hannunta dauke da karamin kaskon wuta da garwashi a ciki.......kallo na bita dashi ganin ta d'aga 'karkashin gadonta tana lalube ledar data shigo da ita ta dauko ta saki zanin gadon ta rufe........ta shiga zazzage magungunan dake cikin ledar.....Wani tsumma ta kwance naga ta d'ebo maganin dake ciki ta zuba a wutar a take dakin ya turni'ke da haya'ki! tari ya sar'ke ni! haya'kin maganin ya dinga shiga bakina da hancina! a gigice na mi'ke na fita daga d'akin ina tari da rirri'ke kirji, ko gama dawowa hayyacina banyi ba itama ta fito daga dakin ido jazur! sai tari take hawaye na zuba daga idonta......

*Masoya a taimaka da sharing👏🏼*

*IDAN KINA BUKATAR KI BIYA KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE.....VIP #600 NORMAL#300 .....ACCOUNT..... 0542382124....BINTA UMAR GTBANK....IDAN KATI ZAKI TURO #400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHATSAPP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

*9*
Haka Baba Iro ya fito ya same mu a tsaye muna tari ga haya'ki na fitowa daga cikin dakin. "Gwaggo lafiya me yake faruwa ne."? Miyau ta had'iya ido jawur tace." Haya'ki na kunna sai tari ya sar'ke muka fito muna shan iska." Yace."Gwaggo wane irin haya'ki ne wannan mai cutarwa.''?

Da sauri tace."Na mayu ne kwana biyu kasala tana damuna shine Uwale ta kawo min dama kuma ai sa'i da lokaci ina kunnawa ."

Shuru yayi yana kallonta nima na zuba mata ido ina mamakin 'karyar data shirga. Dakin ya shiga da sauri tabi bayansa tana kallonsa tace."Ibarahim me kake nema."? Yace."Garin haya'kin zan duba nagani." Tace."Aa ba sai ka wahalar da kanka ba ai ragowa ne na barbad'a a wuta shine fa ya turnu'ke gidan da haya'ki."

Yace."Gwaggo dan Allah ki daina yarda da camfi irin na mutane wane maye ne zai kamaki acikin unguwar nan."? Tace."Aa Ibrahim ai shi maye bashi da kama watakila ma ina hurd'a dasu ban sani ba, to dan nayi haya'ki ai ba laifi bane."

Yace."Hakane gaskiya to dan Allah gwaggo kisan irin haya'kin da zaki dinga yi duba dai wannan kinsa gashi gabad'aya ya sar'ke muku numfashi."

Da sauri tace."Ai yau ne kawai hakan ta faru amma lafiya lau nake haya'kina to tunda ma dai maganin ya 'kare ai shikkenan."

Fita yayi daga d'akin ya kalleni cikin taushin murya yace."Sa'ida ki cigaba da hakuri da halin gwaggo ina nan inayi miki addua akan Allah ya kawo miki miji kiyi auranki."

Hawaye naji na kokarin kufce min nace."To Kawu nagode sosai." Yanda na lura dashi shima yana damuwa da halin mahaifiyar tasa dan dai bashi da yanda zaiyi da ita ne.''

Dakin na shiga na sameta tana gyara shimfid'a k'aurin maganin da haya'kinsa ya dinga sanyawa kaina yana juyawa bana tsammanin zan iya kwanciya a dakin domin kuwa zuciyata in banda tashi babu abinda take.

Tabarma da bargo na dauka na fita daga dakin....shimfid'awa nayi a wani dan loko a tsakar gidan na koma dakin na dauki fillo da wayata, kallo ta bini dashi har na fita daga dakin.

Gwara na kwanta a tsakar gidan yafi min alkairi." Waya ta na bude ina dubawa naga text d'in Alhaji Nura wai yana nan fa yana jiran amsa daga gare ni, murmushi kawai nayi ba tare dana bashi amsa ba na shiga WhatsApp ina dubawa.........Gwaggo da buta hannunta ta fito daga dakin ta nufi bandaki tayi uzirinta ta fito, sai da tazo kusa dani naji tana fad'in " 'Dakina ne babu wanda ya isa ya hanani yin abinda naga dama mutum yayi ta kwana a tsakar gida sauro ma ya ishe shi."
Chapter 9 · 0% Book details