Sashe 61
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Juyawa nayi ba tare da nace komai ba ya biyo bayana.
Tea na had'a masa yace kada kisa min madara Nascafe ya isa." Nace."Tom tsaf na hada masa duk abinda yake bukata na tura gabansa.
Yana break din yana amsa waya jamaa sai kiransa suke ni abin har mamaki yake bani. kallonsa nayi nace."Dan Allah ka ajiye wayar nan ka karya a nutse kada ka kware kayi wa kanka uziri mana.
Ajiye wayar yayi yana murmushi yace."Na ajiye gimbiya.'' Shuru kawai nai ina kallonsa wayar nata ringing yaki dauka a nutse nace."Ina so ka bar ni naje gurin Gwaggo mu gaisa."
Jim yayi kafin yace."Okey ai naga a shirye kike ko."?
Nace."Eh a shirye nake." Yace."Okey tom jeki dauko mayafi sai na ajiye ki idan na dawo da yamma sai na shigo na dauke ki amma kuma ko zaki fara zuwa can hotoro ku gaisa dasu."
Nace."Aa so nake na ware rana kowa ne gida naje musu na yini." Yace."Okey hakan yayi." Mikewa yayi hade da daukar key da wayoyinsa na mike da sauri na nufi dakina domin dauko mayafi.
Bakin kofar gidan yayi parking ya kalle ni da fadin."Idan nazo daukar ki zamu gaisa da Gwaggon." Nace."Tom shikkenan Allah ya tsare ya bada sa'a." Ya amsa da ameeen."
Kokarin bude motar nake ya juyo da fuskata ga mamakina sai kawai baga ya dora bakinsa a kan nawa ya manna min kiss akan labbana. tsigar jikina ta tashi ido na tsira masa ina kallonsa yace."Ki kara hakuri kinji ko insha Allah Allah zai mana magani.
Wani irin tausayinsa ya rufe ni nace."Babu komai Yaya Aminu Allah ya baka lafiya." Yana kokarin kunna motar ya amsa da ameeeen matata nagode."
Ajiyar zuciya na sauke bayan wuce warsa daga gurin na tsallaka a nutse nufin gidan.
Yana zaune a bakin rijiya da wando 3qutar a jikinsa ko arzikin vest babu a jikinsa, koda nayi arba da faffad'an kirjinsa mai cike da yalwar gashi sai naji duk rashin kuzari a jikina, cikin sark'ewar murya nai sallama, yayi gaggawar dago kansa muka had'a ido, kauda kaina nayi da sauri gabana na wani irin faduwa....Babu yabo babu fallasa ya amsa da fadin."Sannu Gimbiya." da sauri na kalleshi Yaya Aminu ya kira ni da Gimbiya shima ya kira ni da Gimbiya shin me hakan yake nufi......Muryar Gwaggo ce ta katse min tunani....''Wannan kamshin turaran daga ina yake fitowa." Da sauri na juya muka hada ido da ita a lokacin da take kokarin fitowa daga dakinta.
Ganina a tsaye yasa tace."Haba koda naji ashe matar manya ce Sa'ida ke kike tafe da sanyin safiyar nan."? Ajiyar zuciya na sauke na karasa cikin gidan sosai ina fadin."Gwaggo nice nazo gaishe ki ko bakya maraba da zuwa na."
Tana kokarin gyara tabarma tace."Wace ni ai zuwanki alkairi ne dama jiya sai da nayi mafarkin ki ina cewa zanzo har gidanki na dubaki."
Murmushi nayi nace."Gwaggo ki dauke tabarmar mu shiga daki." Na fadi hakane sabida bana so na zauna a tsakar gidan sabida shi
Tace."Ai dakin ne da zafi kin san fuskar rana ce duk da kasancewa yanzu gari ya waye amma zafi a dakin shiyasa nayi shimfida a waje to amma tunda kin fiso mu shiga dakin to sai mu shiga."
Takalma na na cire na daga labulan dakin na shiga na zauna gefan gadonta ita kuma ta biyo baya na hannunta rike da redion ta.
Zama tayi kan shimfid'arta cike da kulawa tace."Ina fata dai lafiya Sa'ida wannan zuwan naki na sassafiya yasa nasha jinin jikina.
Murmushi nayi a nutse nace."Gwaggo lafiya sumul kawai nazo gaisheki ne." Cike da jin dadi tace."To har naji dadi a raina da kika ce haka me kike so na girka miki wanda zaki ci."
Cike da mamaki nace."Gwaggo daga zuwa kuma sai maganar abinci." Tace."Eh ai gwara ki za'bi abinda kike so sai nasa almajiri yayi cefane.
Nace."To shikkenan kiyi min danwanke." Tace."Keda bakya cin danwake kuma yau shi kike sha'awa ko dai an samu karuwa ne."?
Girgiza kaina nayi ina gyara yanayin fuskata nace."Aa gwaggo ba'a samu ba kawai dai ina sha'awarsa ne."
Tace."To Allah ya kawo mai albarka Danwaken da miyar taushe kike so ko kuma da man gyda da yaji."?
Nace."Gwaggo kiyi min me miyar taushe amma miyar manja.'" Tace."Tom shikkenan bari naje da kaina nayo cefane.'' Nace."Gwaggo ashe har yanzu kina zuwa yawon cefane baki daina ba.
Tana kokarin yafa mayafinta tace."To Sa'ida da raina da lafiya ta mai zai gagare ni ai duk sanda Rabi ta 'bata min rai yafa mayafi nake naje nayi cefane na na dafa duk abinda nake so daga nau'in abincin da kike aiko min dashi.
Nace."Haba shiyasa naga kinyi shar dake kinyi ki'ba." Dariya tasa tana kallona tace.''Eh haka Uwale ke fad'a wai nayi k'iba."
Gyara fuskata nayi nace."Gwaggo ashe har yanzu kina tare da Uwale baki rabu da ita ba.
Taja ta tsaya tana kallona ido da ido tace."Eh ina tare da ita muddun rai jiya ma anan ta wuni muna hira sannan duk alkairin da kike aiko min dashi biyu nake rabawa na dauki daya ta dauki daya."
Mamaki kawai yasa na bita da kallo gabadaya na garara magana.
Takalmanta na danqo tasa a kafarta ta kama hanyar fita tana surutai ni dai bin ta kawai nayi da kallo ina mamakin al'amarinta sai kace ciki guda suka fito da Uwale taki rabuwa da ita.
Maganarta naji ta dawo gidan ta shigo tana fad'in "Kinga Jarumi ma ya huttashe ni yace na dawo gida zai siyo min kayan miyan."
Nace."To babu laifi hakan. shigowa dakin tayi tana fadin."Kinga kuma sai bayan ya tafi na manta bance masa ya siyo d'anyan naman da za'a sa a miyar ba."
Nace."Gwaggo ko ba'a sa naman miya ba babu laifi ai Allah ya hore miki iya girki nasan miyar za tayi dadi ko babu maggi."
Dariya ta kyalkyale da ita tana kallona tace."Yo dama yaushe zaki had'a mutanan da dana yanzu ai dama iya girki sai mutumin da na yanzu sam babu abinda suka iya sai fele'ke da iyayi."
Nace."Hakane kam amma gaskiya Gwaggo ni bani da matsala na dauki darasi a gurinki."
Redio ta dauka tana murd'awa tace"Aikuwa kin taimaki kanki."
Dakin ne yayi shuru ina duba waya ta ita kuma tana aikin murda redio kamar yanda ta saba.....Dagowa nayi na kalleta ina dawurwura akan maganar dake bakina.
"Gwaggo wata muhimmiyar magana nake so na fada miki amma don Allah ki fahimce ni bana so ki d'aga min murya har makota suji sirri na."
Redion hannunta ta ajiye cikin kulawa ta kalle ni da fadin."Haba ai dama nasan akwai wani abu da kike tafe dashi tabbas jikina sai da ya bani hakan to ina sauraranki."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Gwaggo baki yi k'arya ba dalilin daya kawo ni gidan nan mai karfi ne." tayi shuru tana kallona, Nace."Gwaggo ina cikin matsala a gidan aure na babu kwanciyar hankali domin kuwa bana samun biyan bukatata ta aure shine nace bari nazo na sheda miki halin da ake ciki ko zaki taimaka tunda kina da 'yan uwa wanda suke 'kauye watakila zasu taimaka mana da magani."
Tace."Sa'ida magana kike a rufe nifa bangane maganarki ba, bakya samun biyan bukata ta aure shin bukata wace iri."?
Sunkuyar da kaina kasa nayi nace."Gwaggo Yaya Aminu bashi da lafiyar gaba yana fama da rashin karfi da kuzari baya iya ta'buka komai tsayin wata daya da satika wata mu'amula ta aure bata ta'ba shiga tsakanina dashi ba, shine nace ko zaki taimaka min da neman magani.
Ido kawai ta zuba min tana kallona fuskarta gabadaya ta nuna alamun bacin rai.
"Yanzu dama Aminun bashi da lafiya amma akayi rufa-rufa aka daura miki aure dashi? shin wannan wane irin zalinci ne? wato dan an ganki marainiya sai a zalince ki yanzu ina amfanin aure babu wannan mu'amula ai aure bai cika ba saboda haka wannan auran sam bashi da amfani."
Cikin d'aga murya take maganar....Fuska na 'bata nace."Gwaggo tun kafin fa na fada miki matsalata sai da na fada miki abinda bana so me zai sanya ki dinga daga murya ba zaki tsaya ki fahimce ni ba."
Hannu ta daga min a fusace! Tace."Kinga Sa'ida mutukar akan wannan matsalar ce ba zan tsaya na saurare ki ba wannan ai cuta ce da zalinci to bari Ibarahim din yazo yanda sukayi qula-qular su suka daura auran to sai sun warwareshi mutukar ina numfashi.
Kuka nasa ina kallonta nace."Kashe min aure zakiyi akan wannan matsalar."? Tace."To meye amfaninsa tunda babu biyan bukata." Nace."To ai bake kike zaune da mara lafiyar ba nice kuma ni banzo nan domin ki kashe min aure ba taimakona nazo kiyi amma kina nema ki sanja magana.
Tana kokarin magana ya daga labulan dakin hannunsa rike da ledoji da kayan miya masu yawa.
Ganin yanayin da muke ciki yasa ya sha jinin jikinsa a nutse yace."Aunt Sa'ida Allah dai yasa bake kika sata 'bacin rai ba."
Kauda kaina nayi daga barin kallonsa nace."Ni babu ruwana Khalid kamar ka mance halinta na saurin fusata."
Ya kalleta da fadin"Gwaggo ga cefanan kayan miyan nayi miki." Tace."To Jarumi nagode wallahi sai na manta bance ka siyo nama ba.
Yace."Kada ki damu na siyo gashinan a ledar sa daban." Tace."Allah ya kara bud'a maka Jarumi Allah yasa ka zama zakaran gwajin dafi akan dukkanin harkokinka." Ya amsa da ameeen Gwaggo."
Kallona yayi da fadin."Aunty Sa'ida gobe idan Allah ya kaimu zan koma legos bayan sati biyu kuma zamu tafi kasar america da 'Yan uwana inaso kiyi min addua.
A nutse nace."Khalid Allah yasa kaje lafiya ka kuma dawo lafiya Allah ya baka nasara a rayuwarka." Ya amsa da ameeen Ya Allah auntyna." labulan dakin ya saki ya bar bakin kofar.
Ta juyo da hankalinta kaina da fadin."To tunda kince zan kashe miki aure me kike so ayi yanzu."?
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min_*