← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 90

Sashe 31

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da sauri tace."Ibrahim ai gidan yafi karfin mu le'ka kaga abinda yake fitowa daga cikin gidan.

Le'ka kansa yayi soron ya hango haya'ki da sauri yace."Subahanallahi Gwaggo ba dai wuta ce ta tashi a gidan ba.'' Yana kokarin kutsa kansa gidan yake magana.

Gwaggo ta hana shi shiga da fadin"Oh o! ko d'aya Rabi ce take haya'ki a gidan ko na barkono ne oho! dan a jigace muka fito daga gidan.

Kawu ransa ya 'baci sosai shi kam Allah ya jarrabeshi da fitinanniyar mata kafin Gwaggo tayi aune ya fad'a cikin gidan.

Lokacin da ya shiga gidan Ummatu ta gama aikin tana sunkuye gaban kaskon wutar tana karkad'eshi duk tayi wujiga wujiga fuskarta tayi jawur! d'ago kan da za tayi sai taga mijin nata a tsaye a kanta shima hawayen haya'kin na zuba a fuskarsa Kawu Iro bai damu ba saboda yasan dole yayi hawaye saboda zafin maganin da yake fitar da haya'kin.

A sanyaye take kallonsa tana share fuska yace."Rabi wane irin haya'ki ne wannan kika turni'ke gida dashi saboda tsabar iskanci da wulakanci na dawo na tarar da mahaifiyata a waje a tsaye Rabi wai me yasa bakya ganin girman Gwaggo ne me tayi miki kika raina ta."

Ummatu kuka ta fashe dashi tace."Wallahi ni bance su fita daga gida ba da kansu suka fita dama nasan dole a k'ulla min sharri a gurinka.

Mari ya kwada mata yace."Rabi kina nufin mahaifiyata ce za tayi miki sharri.'' hannu da dafe da kumatu tace "Aa ni ba haka nake nufi ba. Yace." To wannan azababben haya'kin na magani da menene.'' ?

Tana kuka tace."Kiranye Malam ya sani nayi wa Khalid saboda d'azu da Rana Ya kira ni a waya yake sheda min cewa shida gida har abadah. shine Baito tace na tashi muje ayi mana taimako akan al'amarin shine wani malami ya had'a min wannan maganin yace nasa a wuta na tsaya a kai na kira sunan Khalid in sau dari ba d'aya."

Fuskarsa ta sanja da yanayi na 'bacin rai yace."Rabi yanzu akan yaron nan Khalid kike nema ki kauce hanya wane irin mushirikin malami ne wannan kikeje gurinsa da ya baki irin wannan hayakin."?

Tana hawaye tace." Kandala 'Kawar Baito ce ta kaimu gurinsa a can cikin k'yauyen Janguza."

A karaf a kunne gwaggo a lokacin da suke kokarin shiga gidan ita da Sa'ida.

Tace."Umhum! kaji maganar Uwale ta fito ko Ibrahim."? da sauri ya juya yana kallonta ta cigaba da cewa." Ibrahim ba zan ta'ba mantawa ba kafin ka auri Rabi babu irin abinda ba a fada maka ba a kanta da mahaifiyarta amma ka rufe ido to yanzu ai sai ka gazgata maganar mutane tunda gashinan da bakinta tana fada maka cewa ita da mahaifiyarta sukeje Janguza gurin malami.

Kawu Iro jikinsa yayi sanyi tabbas hakane babu irin shawarwarin da ba'a bashi ba akan ya hakura da Rabi ya nemi wata ya rufe idonsa a lokacin saboda masifar son da yake mata ya aureta gashinan tana azbatar masa da mahaifiyarsa.

Yace."Gwaggo dan Allah kiyi hakuri wallahi tuntuni na gazgata maganar mutane akan Rabi ba mutuniyar kirki bace."

Tace."Ai ni tuntuni magana ta wuce a gurina amma inaso na sanar da kai cewa Yau tsayin kwana biyar kenan Kullum matarka bata yini a gida haka take fita tana barin mu da yunwa ga kayan abincin Sa'ida ya kare muyi ta kame-kame! to sabida haka nake umartaka cewa ka hana ta zuwa ko'ina idan kuma ta'ki to ka gindaya mata sharadi cewa duk sanda ta sake fita a bakin auranta.

Ido jawur yake kallon Ummatu da tayi muzu-muzu a tsaye sabida tsabar zurga-zurga har ta rame yace."Rabi ina kike zuwa babu izini na sannan kuma ina kike kai kudin cefanan da nake baki a kullum."

Murya na rawa tace."Wai shin ya za'ayi na zauna a gida na kwantar da hankalina rayuwar yaro na na cikin garari ai dole naje inda za'a taimaka min."

Gwaggo tace."Shiyasa kika dauki katifar dake shimfid'e a gadon ki kika siyar saboda kiyi yawon malamai."

Da sauri Kawu Iro ya kalleta dan shi bai da labarin siyar da katifa tunda a dakinsa yake kwana sai da Ummatun ta kai kanta gurinsa.

Gwaggo tace."Eh Ibrahim maganata gaskiya ce Kwana hudu da suka wuce Rabi ta siyarwa da Lantana katifar ta.....Kawu Iro kamar yayi kuka yace."Rabi me na gaza dayi a gidana yunwa ko ishirwa."? shuru tayi tana dauke kanta

Yace." To bari kiji Rabi bani kika tozarta ba kanki kika tozarta kuma shi yaron da kike kashe kudi a kansa ko ya dawo ba zai zauna mana a gida ba sai dai ya nemi gurin zama yawon bin malamai kuma kada ki fasa kece a wahale sannan maganata ta karshe dake ita wallahi tallahi duk sanda kika sake fita daga gidan nan bada sani na ba a bakin auranki dan na gaji da wannan munanan d'abi'un naki."

Ummatu tana kuka na fitar hankali ta shige gurin....Ya juyo cikin tausasawa yake rarrashin mahaifiyartasa Gwaggo tace."Ibrahim kada ka damu kaji ko kaje kayi sallah nayi abinci kazo kaci mu tattauna muhimmiyar magana."

Yace."To shikkenan Gwaggo bari na shiga na daura alwala." tace"To babu laifi." Kawu Iro ya bude kofar gurinsu ya shiga ita kuma ta shigo dakin ta sameni a zaune a bakin tabarmar ta.

Zama tayi tana fad'in "Haba jama'a mata duk ta zame mana annoba a gida wallahi Sa'ida da Ibrahim yana da iko aure zan sa shi yayi domin kuwa sam bai dace da mace ta gari ba."

Nace."Gwaggo kema fa da laifinki kina shiga abin da babu ruwanki a gaskiyar magana Ummatu tana hakuri dake da halin ki shiyasa wani lokacin idan tana mayar miki da magana bana jin haushi sabida nasan ke kika janyo."

Tace."Sa'ida nifa ba zan ga ba daidai ba nayi shuru haka halina yake tunda can bana shuru kawai na zuba ido akan mutum yana abinda yake so ban gyara masa kuskuransa ba."

Nace."To Gwaggo kada dai kisa Kawu yayi wani aure a yanzu dan Allah ki kyaleshi yaji da d'aya idan ya 'karo aure gidan nan sansanin ya'ki zai zama gaki ke kuma a gefe kina 'kara ruru wutar al'amarin sabida haka ki kyautata zamanki da surukar ki shima Kawu Ibrahim sai yaji dadin tafiya neman sa."

Tace."To ai shikkenan Sa'ida tunda laifi na kike gani a kan na Rabi." Nace."Aa Gwaggo bance ke kadai kike da laifi kowa yana dashi."

Shuru tayi bata tanka ba ta dauki redio tana murdawa. Kawu ya shigo dakin na gaisheshi a nutse ya amsa Gwaggo ta ajiye redion a kusa da ita bayan ta kama tashar da take so.

Abincin ta zuba masa tasa masa da yawa, yaci ya koshi yasha ruwa. tace."Ka gani sai Rabi taci kayanta idan ta dafa dan Allah Ibrahim ko tayi maka tayi kada kaci ka nuna mata kuskuranta.".......kallonta nayi ina mamakin 'karfin halinta ko waye ya fad'a mata ana shiga tsakanin miji da mata oho.

Zamansa ya gyara da fad'in"Gwaggo kada ki damu ai sai na sake nuna mata kuskuranta idan na shiga gurin." Tace."Yauwa to ka tauna mata tsakuwa sosai." yace."Insha Allah Gwaggo ke nake saurare akan maganar da zamu tattauna.

Gyara zama tayi ta fuskance shi sosai tace."Ibrahim akwai wani bayani dana saurara daga Malam Aminu Daurawa inda yake cewa................Bayani tayi masa sosai kamar a gabanta malam din yayi tambihin...Kawu Iro ya dago kansa a hankali yace."Gwaggo wallahi ni kaina na sha'afa da wannan al'amari nasan tabbas hakane gaskiya malam ya fad'a akan wannan al'amarin kuma dole ne a dakata da daurin aure tukkuna aga abinda ubangiji ya lullube amma ni yanzu tunanin ta inda zan tunkari Alhaji Nura da maganar nake."

Gwaggo tace."Muma dai tun dazu muke wannan nazarin mutumin nan fa ya riga ya gama duk wani shirye-shiyen sa lokaci kawai yake jira idan anje masa da wata magana dole yayi zargin wani abu.

Kafin Kawu yace wani abu kira ya shigo waya ta Alhajin ne da sauri na fita daga dakin da wayar a kunnena.

Soro na tsaya muka gaisa kamar ko da yaushe kafin yace."Sa'ida wasu harkoki ne na kasuwanci suka taso min a yanzu dama kuma tun watanni uku da suka wuce nake tsammanin gudanar da harkokin sai yanzu Allah ya bani iko sabida haka nake baki hakuri akan abinda zakiji na fada miki a yanzu." a sanyaye nace."Haba Alhaji ai babu komai ina sauraranka.''

Yace."Yauwa 'yar albarka inaso za'a d'aga daurin auran mu sai nan da wata uku ko hudu saboda a cikin satin nan nake so na tafi chana domin company da muke harkokin mu a tare suna bukatata a kusa wannan dalilin yasa nace bari na kira ki a waya na fada miki kafin nazo.'' Ajiyar zuciya na sauke ina godewa Allah a raina babu shakka dukkanin abinda yake faruwa da ikon Allah ne.

Nace."To babu komai Alhaji kada ka damu ai kamar yau ne kaje ka dawo insha Allahu ina zaman jiranka kuma inayi maka fatan alkairi da nasara a rayuwarka."

cikin jin dadi ya amsa da ameeen Sa'ida insha Allahu a satin dana dawo za'a daura auran ki tare a dakin ki.'' mirmushi nayi nace"To Alhaji Allah ya nuna mana lafiya." Ya amsa da ameeen Gimbiya bari na barki ki huta ko insha Allahu gobe zan shigo da wuri muyi sallama."

Nace."To shikkenan sai kazo din a gaishe min da yarana." ya amsa da fadin"Zasuji da kyau insha Allah." sallama mukayi da juna na kashe wayar na koma cikin gidan.

Cikin nutsuwa na nemi guri na zauna ina kallonsu duk sun shiga yanayi na damuwa nace."Gwaggo ku kwantar da hankalin ku Allah ya kawo mana mafita domin kuwa yanzu muka gama waya da Alhaji Nuran yake sheda min cewa tafiya ta taso masa zuwa chana sabida haka za'a daga daurin aure sai bayan ya dawo wata uku zaiyi a can ko hud'u insha Allahu yace cikin satin da ya dawo sai a daura auran.

Gwaggo tace."Kai alhamdulilahi amma naji dadin wannan magana wallahi dama bayan fitar ki muna ta tararrabin yanda za'ayi a tunkareshi da maganar sai gashi cikin sauki Allah ya kawo mana mafita."

Kawu yace."amma kuma kamata yayi yazo ya same ni mu tattauna maganar a tsakaninmu.
Chapter 31 · 0% Book details