← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 90

Sashe 37

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sa'ida mai yasa kika yaudare ni kika sa na aure ki a matsayin budurwa." ? tambayar da yayi min kenan wacce ta kusa sa zuciyata ta faso kirjina ta fito waje.
jarumta na aro nace."Alhaji wace irin magana ce wannan."? Ido ya zuba min fuskarsa a had'e yace." Kada ki mayar dani shashasha mana ba'a kanki na fara auran budurwa ba matata Murja da budurci na aureta kuma akanta nasan ya yake saboda haka jiya na tabbatar da cewa ke ba cikakkiya bace dan duk wasu gyare-gyare da kikayi a gurin sai da na gane budurci ya bambamta da komai."

Zafafan hawaye suka kwace min murya na rawa nace."Haba Alhaji shedar da za kayi min kenan? ashe shiyasa naga kana ta 'kunci ka tashi ka fita tun asubah baka shigo ba sai yanzu to inaso ka sani ni ba 'yar iska bace ballanatana kayi zargin ko gurin yawon ta zubar na sarayar da mutunci na. Sabida haka ni ban san wata magana ba budurci na kai ne ka kar'ba ba wani ba." Cikin kame-kame nake magana gabana kuma na cigaba da faduwa

Yace."Ki saurare ni da kyau kiji abinda zan fada miki." Na kalleshi ina goge hawaye ya cigaba da cewa"Tun kafin na aureki jama'a suke kawo min suka akan ki cewa babu abinda kikeyi a gurin aiki sai lalata da maza wannan dalilin yasa na sake gazgata maganar mutane tunda naga zahiri kada ki mayar dani yaro nasan komai kin cuce ni kin yaudare ni ashe kin san baki da kamun kai kika sa na tsaya na 'batawa kaina lokaci gurin auranki."!

Ina wani irin kuka na zube gabansa hannunsa na rike nace."Wallahi Alhaji duk k'arya ce kada ka gazgata maganar mutane akaina sharri sukai min amma ni bana bin maza zan iya rantse maka da al'kur'ani ni ba karuwa bace budurci kuma da kake magana akansa watakila ya fita ne saboda tsayin lokacin dana dauka banyi aure ba bayan haka kuma kaga kullum bana zama ina zurga zurga zuwa gurin aiki hawa babur da Napep hakan zai iya janyowa na rasa budurcina.

Shuru yayi yana kallona da akwai alamun sassauci a tare dashi a sanyaye nace."Dan Allah ka yarda da maganata Alhaji ban yaudare ka ba kada ka amince da maganganun mutane a kaina sharri sukayi min."

Hannu yasa ya d'ago ni na zauna kusa dashi yace."Naji maganarki kuma na gamsu tabbas zaki iya rasa budurcin ki ta wad'annan hanyoyin da kike fad'a sabida haka ki share hawayen ki na amince da maganarki.

Ajiyar zuciya na sauke nace."Nagode sosai mijina ina rokon Allah ya kauda idanun makiya akanmu." ya amsa da ameeen yana kokarin miqewa yace."Ni zan tafi kasuwa saboda kin san bamu jima da shigo da kaya ba bana zama a gida sosai dan haka kina iya zuwa kiyi breakfast d'in ki."

A sanyaye nace"To shikkenan sai ka dawo Allah ya bada sa'a.'' ya amsa da ameeen ya kama hanya ya fice daga dakin.

Ajiyar zuciya na dinga saukewa ina godewa Allah da yasa ya yarda da maganata yanzu dama ashe kallon karuwa mutane keyi min? shin me nakeyi a makaranta da har mutane zasu sanya min ido su dinga zargi na da aikata fasikanci." hawaye na share a fili nace."Ya Allah kabi min hakkina akan dukkanin wanda ya d'ora min kazafi na zina.

Fuskata na wanke na d'an shafa hoda nasa kwalli a idanuwana kana na fita falon......a hakimce akan kujera na sameta tayi ado sosai kamar itace amaryar tafkekiyar wayarta ce a hannunta tana dubawa.

Gani na yasa ta saki fuskarta tana murmushi ta nuna min kusa da ita na zauna a nutse muna gaisawa.

Yaran na tambaya tace."Sun tafi makaranta sai biyar da rabi zasu dawo ai da har sun zauna suna jiran fitowarki sai kuma direbansu yazo daukarsu da kyar na lallabasu suka tafi.

Murmushi nayi nace."Ai idan sun dawo zamu gaisa da kyau." Tana tauna cingum! din bakinta tace." Kwarai hakane.

Falon ya sake daukar shuru na 'yan mintina kafin tayi magana "Sa'ida kije kiyi breakfast mana." Murmushi nayi ba tare da nace komai ba. tace."Dan Allah ki saki jikin ki dani ni bana kishi irin na jahilci kanwata na dauke ki.''

Nace."Nagode kwarai auntyn Murja. " tace."Nima nagode da kika fahimce ni saboda haka sai ki tashi kije ki karya ko." ba tare da nayi mata musu ba na mike a nutse na nufi gurin cin abincin.

A ranar haka muka yini da Aunty Murja muna hira na dinga mamakin saukin halinta kamar bata da damuwa akaina domin daidai da 'kwayar zarrah banga ta nuna wani kishi a kaina ba wannan dalilin yasa na saki jikina da ita sosai muka shiga kicin a tare mukayi aiki tsaf muka kammala komai muna hira cikin fahimtar juna

Koda yaran suka dawo daga makaranta a daki suka sameni ina shiryawa suka gaisheni suna nuna farin cikin su da zuwana cikinsu nima na dinga jansu a jikina ina duba litattafansu na makaranta.

Sai da mukayi sallar isha'i tukkuna suka fita suka barni ni kadai a dakin.....sai kawai na yanke shawarar fita falon. abin mamaki da al'ajabi maigidan na samu zaune a gurin cin abinci iyalin nasa suna zaune ko wanne da kujerarsa suna cin abinci....sosai na shiga mamakin al'amarin yaushe ya shigo gidan babu labari kuma me yasa basu nemi ni gurin cin abincin ba.?

Gwiwa a sanyaye na juya zan koma daki muryar Yusura ta daki kunnena...."Aunty kizo muci abinci." a sanyaye na juyo ina kallonsu naga shi gogan ko kallona ma beyi ba sai abincinsa yake ci itama aunty Murjar haka.... hakan da sukayi sai ya nuna min cewa basa bukatata a gurin.....jiki a mace na bude kofar dakina na shiga na rufe tare da jingina jikina jikin kofar gabana sai wani irin faduwa yake....wace irin rayuwa ce wannan? shin wai me Alhaji Nura yake nufi dani ne? ganin bani da mai bani amsa yasa na sulale nayi zaman durshan a gurin hawayen bakin ciki ya shiga karakaina a fuskata.

Na jima a zaune a bakin kofar dakin ina kuka kafin na bawa kaina hakuri na mike a sanyaye na shiga bandaki na wanke fuskata na fito ina kallon agogo goma har ta gota bai shigo dakin ba ga yunwa na kokarin cinye min 'ya'yan hanji a sanyaye na mike na fita falon sai na gansu a zaune yaran suna kasan kafet suna duba littafansu na makaranta su kuma suna zaune a kan kujera a tare yana nane da jikinta sai soyayya sukeyi. fitowa ta bai hana su abinda sukeyi ba, ta kalle ni na kalleta ina mamakin iya sharrin ta wai ni za tayi wa dariya na tsaya kawai ina kallonta da jin abinda take fad'a...."Sa'ida kina ji Yusura nayi miki maganar abinci kika share ta.''

Kai tsaye nace."Aunt Murja naga kamar bakwa bukatata a gurin ne."

'Yar dariya tayi tana kallonsa tace."Abban Yusura kaji amaryar ka da wata magana ko."?

Murmushi yayi irin na dole yace." Ina jinta ai na fahimci neman fitina take."

Kallon banza na watsa masa a zuciyata nace"Lusari mijin tace kawai."
Daga ita har shi sunga abinda nayi kuma na lura sunyi mamaki. nace."Ai idan an damu da naci abincin kira na Za'ayi ba kawai sai na fito na tarar daku kuna ci ba.''

Fuskarta ce ta sanja da yanayi na 'bacin rai kafin tayi magana ya rigata da fad'in "Ke wace irin banzar magana ce wannan? kina so ki rusa min tsarin gidana ne."? shuru nayi masa ya cigaba da fuffuka yana kumfar baki.

Nace." Dan Allah kayi hakuri naga kamar maganata ta fusata ka kasan ita gaskiya d'aci gareta."

Da sauri tace."Sa'ida kiyi hakuri anyi miki ba daidai ba kai kuma ka daina wannan kumfar bakin haka.'' Kamar anyi ruwa an dauke yayi shuru sai wani muzurai yake.....naja tsaki cikin raina na bar gurun

Gurin cin abincin na zauna na zuba daidai cikina naci na tashi na bar gurin......nesa dasu na tsaya da fad'in "Aunt Murja sai da safe." Fuskarta kamar gonar audiga ta amsa da fad'in "Allah ya tashe mu lafiya.

Dakina na bude na shiga takaici kamar ya kashe ni cikakken mutum a zahiri mai haiba da kamala uwa uba kudi amma saboda lusaranci mace na juya shi a gida wani irin tsanarsa naji a cikin raina.

Wanka nayi na shirya jikina na kwanta kan gado da waya ta a hannuna.......Misscall din Khalid na gani gabana ya fadi da sauri na mike zaune hannuna sai rawa yake.

Wani kiran ne ya sake shigowa, kamar kada na daga sai wata zuciyar tace " ki daga kiji abinda zai ce."

A hankali nayi sallama naji sanyayar muryarsa yana amsa wa. kafin yace."Aunty ya kike ina fatan kin wuni lafiya." ?

Nace."Lafiya khalid fadi abinda yake bakin ka inada uzuri.'' murmushi yayi wanda yasa tsigar jikina tashi. na lumshe idona ina sauraransa.

Yace."Wato aunty Sa'ida idan bani na kira wayarki ba ban isa ki kira ni kiji lafiya ta ba ko."?

Shuru nai masa yace."Yau so nake nayi hira dake inaso na rage feeling's ne auntyna ina nan sha'awar ki duk ta addabe ni kiyi min wani taimako mana." yakarasa maganar a sanyaye.

Wani irin yanayi na shiga na tsantsar tashin hankali da fargaba nace."Khalid yaushe zaka dawo gida." Ajiyar zuciya ya sauke yace."Na fada miki cikin satin nan zan zo kuma da sadaki na domin ba zan koma ba sai an daura mana aure.

Shuru nayi kaina yana wani irin sarawa nace."To kayi kokari ka dawo kaji ko." Yace."Insha Allahu ki bani Gwaggo mu gaisa.'' da sauri nace."Ta riga tayi bacci." yace."Okey da safe zamu gaisa insha Allahu yanzu meye labari auntyna ki fad'a min kinyi kewa ta ko."?

Ina kokarin magana ya shigo dakin, da sauri na datse wayar na ajiyeta, ya karaso kusa dani a daida lokacin da ya 'kara kira, sai kawai na dauki wayar na kashe ta gabadaya na ajiye saman bedside.

Jallabiyar jikinsa ya cire na dauke kaina daga kansa toilet naga ya nufa da gashi sai gajeran wando naja tsaki da fadin"Shashashan namiji kawai.

Minti biyar ya fito daga toilet din ya kashe wutar dakin, kusa dani ya zauna na sunkuyar da kaina ina jin wani irin haushin sa.
Chapter 37 · 0% Book details