← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 90

Sashe 53

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Girgiza kanta tayi tace."Sa'ida idan ma tilas akayi masa ai shine ya janyowa kansa me yasa tuntuni baiyi aure ba me ya rasa na rayuwa yana da kudi gida da mota to me yake jira kuma ki daina kiransa saurayi sai dai ki kirashi tuzuru domin ya tashi daga sunan saurayi ya koma matashi kuma baki wuce sa'ar auransa ba ni dai babban burina ki bani had'in kai akan wannan al'amari domin kin san Alhaji ya wuce komai a gurinmu."

Shuru nayi ina girgiza kaina gabadaya kaina ya kulle na rasa wane irin tunani zanyi idan Allah ya kaddara aurena da yaya Aminu wace irin rayuwa za muyi ni dai ba zan iya d'orar da halinsa ba tunda ba zaune nake dashi ba abinda dai zan iya tunawa shine yana da saukin kai da iya mu'amula sai dai halayen mutum basa fitowa sai zama yayi zama ina tsoron abinda zai faru a rayuwar auranmu domin a yanzu gabadaya auran ya fice min daga rai mussaman idan na tuna irin zaman da nayi a gidan Alhaji Nura gabadaya sai naji auran ya fice min daga raina.

Salim sai da ya koma gida cin abincin rana ya samu damar kiran wayar abokin nasa....Khalid yace."Wai wace irin magana zaka fada min ne."?

Salim yace."Khalid wai auran aunty Sa'ida ya mutu ne."? Cike da mamaki yace."Me yasa ka fad'i haka."? Yace."Sau tari ina ganinta a unguwa idan zata wani guri a takaice dai yau ma ni na dauketa a babur dina na kaita hotoro kuma mayafinta a kafad'a gaskiya jikina na bani babu aure a tare da ita.

Khalid ya saki sanyayyar ajiyar zuciya yana murmushi yace."Lallai kace na dawo gida da kwarin gwiwata." Salim yace ."Wai kai don Allah har yanzu baka hakura da ita ba."?

Yace."Salim idan kaga na hakura da aunty Sa'ida to kace bukatata ta biya na aureta amma na rantse maka muddun ina numfashi sai na hanata sunkuni.

Salim yace."Khalid ka ji tsoron Allah ka nemi za'bin Allah kada kace zaka tsananta akan dukkanin hukuncin da Allah ya zartar."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Salim Allah ne ya d'ora min kaunarta kuma kullum idan zan dungura goshina a 'kasa sai na rokeshi da ya za'ba min abinda yafi alkairi tunda naga har yanzu zuciyata ta kasa hakuri da ita na tabbata a gaba ina tare da nasara zan cigaba da bibibyar rayuwarta har sai sanda Allah ya cika min burina ."

Salim ya dinga girgiza kansa yana mamakin al'amarin a sanyaye yace."To ai shikkenan tunda kace haka Allah ya za'ba mata dukkanin abinda yafi alkairi." ya amsa da ameeeen ya Allah.

Suna yin sallama da Salim din ya shiga kiran wayarta lokacin tana tare da mahaifiyarta tana sake kwantar mata da hankali....koda taga kiran nasa daukar wayar tayi ta kashe tana jan tsaki.

Cikin jin ciwon abinda tayi masa ya nemi number Wayar gwaggo ya shiga gurin kira, ta dauki wayar tana dubawa ta gane sunansa da yayi mata serving da *Jarumi* yau dai tayi ra'ayin d'aga wayar domin dama can daurewa take tayi kewarsa.

Tana dagawa ya sauke ajiyar zuciya da fadin."Har naji sanyi a cikin raina.'' Tace."Khalid ka kyauta akan abinda kayi." Da sauri yace."Gwaggo me nayi kuma babu gaisuwa sai ki fara 'korafi.''? a fusace! tace."Ka kashewa Sa'ida aure sai ka zuba ruwa a kasa kasha."

Murmushi yayi had'e da shafa sajensa yace." Gwaggo ni kada ku d'aura min laifi ta yaya zan kashe mata aure bayan bana gari dama can auran matacce ne.''

Tace."Kafin ka tafi ai ka shirya kitumurmurar da ta janyo mutuwar auran ashe bakaji maganar da nayi maka ba sai da ka wanke kafa kaje gidan kuma saboda tsabar rashin mutumci ka shiga har dakin baccinsu."

Yar dariya yayi yace."Gwaggo cewa tayi nayi mata wani abu dana shiga k'uryar dakinta."? Tace."Oh!o ai ko bakayi mata wani abuba tunda mijinta ya shigo ya ganka dole ya zargi wani abu a tsakaninku tunda dama can akwai soyayya.

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin."To ai shikkenan magana ta kare Allah yasa haka shi yafi alkairi."

Tace."Dama ai haka zakace tunda haka kake so to kama daina rawar jiki domin babanka yayi rantsuwa akan ba zaka aureta ba.

'Dif! yayi yana jin wani d'aci a makogwaronsa yace."Gwaggo akan me? zaiyi rantsuwa? akan me zai hana abinda Allah ya halasta." Tace."Ai bani zaka tuhuma ba wayarsa zaka kira ka kai masa k'abali da ba'adi." Tana kare maganar ta kashe wayar tana fad'in "Ja'iri kawai mara zuciya tamkar yarinyar nan ce mace a duniya ya nace dole sai ya aureta

Khalid ka sa'ke yayi da waya a hannunsa gumi sai tsatstsafo masa yake babu shakka dole yaje gida a kurkusa domun yana jin tsoron ayi masa sakiyar da babu ruwa.

Yamma likis na koma gida Gwaggo ta dinga bina da kallo tana so tayi min magana amma tayi shuru da bakinta sai bayan muyi sallar magariba ne na kalleta da fadin."Gwaggo kin san abinda yake faruwa kuwa."?

Girgiza kanta tayi tace."Ina zan sani bayan naga kamar kina 'boye min ai shiyasa nayi shuru da bakina na zuba miki ido."

Ajiyar zuciya na sauke nace."Dama so nake ki samu nutsuwa tukkuna na sheda miki abinda yake faruwa.

Tace."To ina sauraranki Allah yasa alkairi ne." a nutse nace."Alhaji ne ya nemi alfarma akan na auri babban d'ansa Aminu."

Zuba min ido tayi tana kallona kafin tace."Sai kika ce masa me."? a sanyaye nace."Gwaggo na amince domin ba zan iya jayayya dashi ba mutumin bai cancanci haka daga gurina ba.

Tace."Ai dole ki fadi haka mana dama ai abinda yake nufi kenan shiyasa yace kije yana neman ki ashe maganar kenan zai kama ya aura miki yaronsa da yake fama da matsala."

Nace."Gwaggo wace irin matsala kuma don Allah kiyi wa al'amarin kyakykyawar fahinta."

Tace."Sa'ida ni kam bana miki sha'awar auran wannan mutumin sam baku dace ba." Nace."Gwaggo saboda me kike ganin bamu dace ba."

"Haka kawai banyi na'am da al'amarin ba amma tunda har kin amince masa to bani da tacewa sai dai kawai nayi miki fatan alkairi."

Shuru nayi kaina a kasa ina nazarin maganarta to ko dai Gwaggo ta hango wani nak'asu ne a tarrare da Yaya Aminun yasa take fad'ar wannan magana! Ni dai a zahiri ban ga makusa a tare dashi ba cikakken namiji ne wanda ya tara dukkanin abinda ake bukata sai dai hausawa suna cewa abinda babbah ya hango yaro ko ya hau tudu ba zai hangoshi ba.

Kwana nayi da tunani da zullumin al'amarin da safe da Kawu ya shigo nake fada masa yanda mukayi da Alhajin....Yace."Sa'ida ina da masaniyar komai domin kafin kije ku tattauna sai da ya kira ni har gida naje na sameshi ya sanar dani komai tabbas naji dadin al'amarin kuma na taya ki murna samun nagartaccen namiji kamar Aminu ina rokon Allah ya tabbatar muku da alkairi. " A raunane na amsa da "Ameeen ya Allah Kawu." Ya kalli Gwaggo da fadin." Baki ce komai ba Gwaggo.'' Tana cigaba da abinda yake gabanta tace."To me zance Ibrahim ai tunda kun riga kun gama yanke hukunci bani da tacewa.

Yace."Gwaggo kiyi hakuri kiyi wa al'amarin kyakykyawar addua." Tace."Ai tun jiya da ta fada min maganar nayi addua Babu komai ka tafi kasuwarka Allah ya bada sa'a."

Yanda ta fadi maganar zaka gane akwai wani abu a cikin ranta da yake damunta. A sanyaye yace."To shikkenan Gwaggo sai na dawo." Tace."Allah ya tsare ya bada sa'a." Ya amsa da ameeen yana kokarin fita.

Dago kanta tayi ta kalleni da fadin."Yanzu Sa'ida abinda kukayi shine daidai anya ba zaku rage son kai ba."?

Nace."Gwaggo me kuma mukayi."? Tace."Fisabilillahi Sa'ida yaron nan Khalid yana kulafucin ki amma ke sam bakya ta tasa wai shin dan Allah wace irin kiyayya kike masa haka me yasa ba zaki aureshi ba.

Cike da wani irin yanayi nace."Gwaggo wai don Allah me yasa kike dawo da hannun agogo baya na dauka tuntuni maganar Khalid ta wuce tunda zaiyi aurensa to me yasa zaki dinga tayar da abinda ya wuce.

Gefan zaninta tasa ta goge hawayen fuskarta tace."Wallahi tausayinsa nake ji Sa'ida ya kwallafa ransa a kanki sai wahalar dashi kuke hakika da ana sanja zuciya da sai na sanja masa zuciyarsa ya daina wahalar da kansa a kanki Jiya nan sai da ya bugo min waya yana cikin damuwa banda maganarki babu abinda yake mai zai sanya ba zakiyi mana kara ba? me zai sanya ba zaki tausayawa dan uwanki ba? Sa'ida duk fa namijin da Ibrahim yake so ki aura ba kamar d'an cikinsa ba zaifi so ki auri Khalid amma sabida baya so yayi miki dole yake rarrashinki da bin abinda kike so ke kuwa mai zai sanya ba zaki kyautata masa ba.

Cikin kuka nace."Wai shin Gwaggo ya kike so nayi ne? wallahi da mace tana auran maxa biyu a lokaci guda to da na auri Khalid da Yaya Aminu amma yanzu lokaci ya kure dole Khalid ya sake hakuri a karo na biyu tunda na ruga na amince da maganar auran Yaya Aminu duk sai mu barwa Allah abinda ya hukunta."

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*

*66&67*
Gefan zaninta tasa ta share hawaye da fadin."Ai shikkenan Sa'ida tunda haka zaki ce dole nayi hakuri da hukuncin da kika yankewa kanki amma ni sam bana sha'awar ki da wannan mai ba'kar fuskar." Kallonta nayi ina mamakin maganarta Gwaggo idan bata son abu komai kyawun sa ta dinga kushe shi kenan amma in banda haka meye laifin Yaya Aminu kyakykyawa ne sosai Khalid din babu abinda zai nuna masa sai haske fata.

Nace."Gwaggo maganar nan ta wuce don Allah ki daina kuka da damuwa ki cigaba da addua ni da Khalid din Allah ya za'ba mana abunda yafi alkairi Gwaggo duk sonki da na auri Khalid idan Allah bai nufa ba dole ki hakuri kin san komai nufi ne na ubangiji mussaman sha'ani na aure ba'a katsalandan a ciki kawai ki roki Allah alkairi sai kiga ya tabbatar miki.

Tace."To me kika ji na k'ara cewa? ai magana kuma ta wuce wannan yaro Khalid kuma Allah ya sanya masa dangana."
Ameeen na amsa ina kokarin mi'kewa tsaye
Chapter 53 · 0% Book details