← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 90

Sashe 63

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwale tayi murmushi tare da fadin."Yo ai Sa'ida wannan matsalar ba sabuwa bace mu da muke yawo gidajen masu magani mu muke ganin abubuwa wannan matsalar itace ke damun wasu mazan kuma idan anyi katari da magani mai kyau sai kiga an dace saboda haka ki kwantar da hankalinki yanzu ki bada sadaka sai nayi sauri na tashi na tafi insha Allahu kafin la'asar na dawo.

Shuru nayi ina nazarin maganarta.....Gwaggo ta fusata! da fadin."Ke duk wanda zai taimaka miki sai kin zarge shi ki saki zuciyarki ki bada sadakar magani tunda dai ke kikaji kika gani sai ki daura d'amarar neman magani."

"Uwale dan Allah kada naji maganar nan a wani guri." hankalina a kanta nayi maganar .

Gabad'ayansu suka rike baki Uwale cikin jin haushi tace"Sa'ida munafuka kika mayar dani kome."?

Da sauri nace"Aa ni ba haka nake nufi ba halinki na sani idan labari yayi miki dadi sai ki manta ki fadi abinda bai kamata kowa yaji ba."

Cikin takaici Gwaggo tace."Uwale tashi kiyi tafiyarki ina dalilin wannan abu yarinya ta dinga kokarin cin fuskarki a banza a wofi."

Da sauri nace."Gwaggo kinga don Allah ki tsame kanki daga cikin maganar nan tunda dai ke kinqi taimakawa ai sai kija bakin ki kiyi shuru ki kyale wanda zasuyi.

Tsaki taja ta bar gurin.

Handbag d'ina na bude na dauko kudi dubu dubu guda biyar na bata da fadin "Uwale ga sadaka Allah ubangiji yasa a dace." Hannu tasa ta 'karba da fadin."ameeen ameeen." Na mika mata dubu daya da fadin."Ga wannan sai ki kara kudin mota." tasa hannu ta kar'ba da fadin."To nagode a na tashi na tafi kada naje na samu layi a gurin.''

Nace."To shikkenan Allah yasa a dace."Takalmanta tasa tana amsawa ta leqa kicin a gurguje tayi sallama da Gwaggo ta fita daga gidan.

Mikewa nayi jiki a sanyaye naje na kwanta gadon gwaggo ina tunanin wautar dana tafka sai yanzu da na zauna nayi tunani da nazari na gane manufar Khalid wato ya bugi cikina yaji dukkanin sirri na yana min dariya idan banda tsabar iskanci a ina zai samo maganin da yake magana gabadaya kaina ya daure tunani na ya ta'allaqa gurin ganin na samu mafita akan abinda yake damuna shiyasa na saki jikina dashi na fada masa abinda ke damuna dariyar da yake itace ta tabbatar min da cewa kawai tsabar iskanci ne babu wani taimako da zaiyi mana.

Kwanciya na gyara a kan gadon ina addua akan Allah yasa dai a dace da magani idan hakan ta faru itama Uwale dole a samu kyauta ta mussaman ayi mata mutukar ta kasance wacce tayi sanadiyar samuwar abinda muke bukata.

Motsin shigowarta naji dakin nayi saurin rufe idona "Sa'ida kinyi bacci ne."? Shuru nayi mata sai naji tana cewa" Allah sarki watakila tayi bacci oh! ko wane bawa dai da irin jarrabawarsa a rayuwa." Fita tayi daga dakin na bude idona ina kallon bakin kofar da tunanin maganarta ashe tasan kaddara ce amma idan rigimar ta tashi sai ta mayar da laifin kaina.

Jin ana kiran sallah yasa na sauko daga gadon fita nayi domin daura alwala lokacin har ta kammala aikinta tana kashe wuta.

Kallonta banyi ba na shiga bandaki na fito ina daura alwala tace."Ai na shiga dakin naga kina bacci."

"Umm." abinda nace kenan na cigaba da abinda nake tace."Idan kinyi sallar ai sai kici abinci ko gashinan na kammala." Ina kokarin mikewa nace."Nifa Gwaggo ba cin abinci ne ya kawo ni gidan nan ba zaman da kika ga nayi ina jiran Uwale ta dawo na kar'bi magani nayi tafiyata." Ina gama maganata na bar gurin ba tare dana saurari abinda za tace ba.

Ina zaune akan dadduma ta shigo dakin, na kauda da kaina da fadin."Gwaggo na tashi a hannunki nayi wayo a hannunki kiyi min aure amma ace ba zaki rufe sirri na ba shin wannan wace irin rayuwa ce Shikkenan tunda abin naki ya zama haka dukkanin matsala ta zan dinga tunkarar mahaifiyata da ita nasan tunda ita ta haife ni zata rufa min asiri kuma ta taimake ni."

Uffan ba tace dani ba ta hau kan dadduma ta tayar da sallah, koda ta idar da sallar sai da taja carbi kafin ta ajiye ta mike ta fita.

Kwanonin abincin ta shigo dasu dakin ta ajiye daidai lokacin Ya shigo dakin ya tsaya daga bakin kofa da fadin."Gwaggo Ummatu bata dawo bane."?

Tace."Khalid yaushe Rabi zata dawo gidan nan ka manta 'Yar gidan yayarta ce ta haihu ko bata fada maka ba."?

Kansa ya sosa yace."Wallahi ranar da akayi haihuwar ma ta fada min na manta ne gabad'aya okey ina tsammanin yanzu idan naci abinci zanje can Dalan nayi sallama dasu."

Tace."To hakan yayi daidai sai ka shigo kaci abincin." Yace."Bari tukkuna na watsa ruwa zafi akeyi wallahi." Tace."Ai dama kai ko babu zafi a gari baka gajiya da kuzawa kanka ruwa.

Dariya kawai yayi ya bar gurin.

Kallona tayi da fadin."Sa'ida kin gama cin mutuncin.''? A hasale nace."Gwaggo wane irin cin mutumci gaskiya ce na fada miki tunda dai kin kasa rufa min asiri zan koma gurin uwar data haife ni."

Kuka ta fashe dashi tana nuna kirjinta tace."Ni kike fadawa wannan maganar."? dauke kaina nayi na 'bata rai sosai! ta cigaba da share hawaye tana fadin."Ai shikkenan tunda fahimtar da kikayi min kenan babu komai akwai Allah."

"Gwaggo laifin me nayi miki da zaki had'a ni da Allah nifa wallahi Uwale nake jira ta dawo na bar muku gidanku."!

Baki ta rike tana kallona a tsorace! nace." Eh ba zan zauna a gidan da ake nuna min wariya ba a zahiri kina nunawa kin fi son Khalid dani."

Hawaye ta share ta saisaita kanta a nutse tace."Sa'ida maganar nan ta wuce kada kisa jinina ya hau dake da Khalid duk daya kuke a gurina saboda haka kiyi hakuri ki daina wannan maganar dazu ma raina ne ya 'baci shiyasa kikaji ina surutai amma tunda bakya so na daina Allah yasa a dace da magani mai kyau."

Uffan bance mata ba ta cigaba da maganganunta nace."Gwaggo bafa zanci abincin nan ba ki daina wani damuwa a koshe nake."

Ta dinga kallona tana girgiza kanta dauke kaina nayi dan ko kadan bata bani tausayi ba saboda halinta.

Shigowa yayi ya ganta cikin damuwa....."Gwaggo menene naga kamar kinyi kuka idonki yayi jawur."
Kallonsa nayi na ganshi daga shi sai short Neckar ko arzikin singlet babu a jikinsa, gabadaya hankalina ya tashi na sunkuyar da kaina kasa gabana na bugawa.

Dakin ya shigo sosai ya zauna kusa dani ina jin kamshin sabulun da yayi wanka wani masifaffen feeling's ya dinga taso min.

"Aunty Sa'ida me ya faru.''? ba tare dana kalleshi ba nace." Gaka gata ka tambaye ta mana." Murmushi yayi yace."Gwaggo menene."?

Ajiyar zuciya ta sauke tace."Khalid wai ba za taci abincin nan ba shine nake mamaki." Ya kalle ni da fadin."Akan wane dalili."? Tsaki naja na mike na fita na bar musu dakin. ita dashi gabadaya suka bini da kallo.

Tsakar gida na zauna ina duba waya ta ina jinsu suna magana 'kasa-'kasa sam bai dame ni ba babban burina naji sallamar Uwale da magani a hannunta.

To sai daf da magariba Uwale ta dawo a jigace hannunta rike da wani katon buhu cike da itacen magani da saiwowi.

Gwaggo ta gyara mata tabarma tana mata sannu.....Tace."Gwaggo bani ruwa nasha yau nasha bakar wuya kafin na samu ganin mai daburau."

Gwaggo da sauri ta mike ta ciko kofi da ruwan randa ta bata tasha sosai ta ajiye kofin tana sauke numfashi.....Sai da hankalinta ya dawo tukkuna nayi mata sannu ta amsa da yawwa Sa'ida ai tafiya tayi kyau sosai tunda anyi dace an samo magani gashinan cikun buhu.

Nace."To Alhamdulillahi Nagode sosai sai kiyi min bayanin maganin." Tana kwance buhun tace."Ai dama yanzu zanyi miki bayanin yanda zakuyi amfani dashi."

Tsaf ta zazzage itacen maganin da wasu gari a daure a leda da saiwa ta shiga yi min bayani nace."To insha Allahu zanyi kokarin bin ka'ida. Tace."Kuma mai maganin yace."Bayan sati biyu a koma masa da bayanin yanda mara lafiyar yaji a jikinsa." Nace."To shikkenan Uwale insha Allah zanzo har gidanki da bayanin." Ta shiga mayar da maganin cikin buhu tana cigaba da magana da 'kawar ta.

Gwaggo ta mike da fadin."Bari na kawo miki abinci nasan dai kinsha yunwa acan." Tace."Aikuwa dai dama kin san babu masu siyar da abinci da kyar na samu mai awara na siya na toshe wata kafar."

Tace."Ai dama dubara akeyi idan mutum zashi irin wannan guri sai yayi abincinsa ya zuba a fulas ya tafi dashi maganin yunwa." Tace."Wallahi kuwa ai na dauka ba zan dade ba shiyasa ban tafi da abinci ba sai kuma naje na tarar da layi jamaa kowa lalura ta ishe shi."
Gwaggo dake kicin tace."Ai fa abinda ake ta fama dashi kenan Ubangiji Allah yayi mana magani." Gabadaya muka amsa da ''Ameeen Ya Allah."
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*

*81&82*
Gwaggo abinci mai yawa ta had'awa Uwale tasa mata miya da nama sosai ta ajiye mata a gabanta ta dauki kofin silban gabanta ta debo mata ruwa a randa ta ajiye mata tare da zama kusa da ita. Uwale tace."Sannu da aiki Gwaggo nagode sosai da hidima." Gwaggo tace."Haba Uwale ai babu komai an riga an zama d'aya muma mun gode sosai da taimakon ki muna rokon Allah yasa kwaliya ta biya kudin sabulu." Uwale na kokarin kai lomar abinci bakinta tace."Insha Allahu za'a dace domin mutane da yawa sun sheda kyawun maganin mai daburau shiyasa jama'a keta rububin zuwa gurinsa kar'bar magani."
Chapter 63 · 0% Book details