← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 90

Sashe 2

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanciya nayi ba tare dana cire hijabin jikina ba kawai na dinga binsu da kallo ina jin tsantsar takaici a cikin zuciyata ni kam ko zan rasa miji a gidan duniya banga abin aure a jikin wannan mara mutuncin yaron ba........Tun sanda na kwanta a gadon yake min wani d'an iskan kallo irin na manufarci a hasale! nace"Wallahi idan baka daina yi min wannan d'an iskan kallon ba sai ranka ya 'baci shashashan yaro mara kunyar banza da wofi."

'Bata fuskarsa yayi dan har sai da fatar saman goshinsa ta tattare haka yake tun yana yaro idan ransa ya 'baci sai goshinsa ya tattare ya watsa min kallon banza had'e da girgiza kansa.......Yana kokarin yin magana ta rigashi da fadin" Ke Sa'ida meye kuma na kiransa shashasha ina laifin wanda zai tallafe ki ni wallahi naji dadin maganar da yazo min da ita duk girmanki da shekarunki ba zaki gagareshi ba dan mace komai girmanta bata fin karfin namiji."

Tsaki! naja ba tare da nace komai ba na juya musu baya....'Kawataccen sajan fuskarsa ya shafa idonsa 'kur! a mazaunanta da yake bala'in 'kwa-'kwa! duk da da hijabi a jikinta hakan bai hanashi ganin tudunsu ba, ya dinga jin wata lafiyayyar sha'awa na taso masa, a sanyaye ya kalli Kakar tasu yace."Gwaggo ga indomee na nan ki dafa min zanje na dawo." da sauri tace"To d'a nagari bari na kunna risho ai ina da kalanzir a ciki." Fita yayi daga dakin yana shafa sumar kansa.

Sama-sama nake jin surutan ta kafin bacci mai nauyi yayi gaba dani......Can cikin baccin naji maganarsa sama-sama! "Haba gwaggo kefe ba'a abin arziki dake yanzu dan Allah haka ake dafa Indomee duba kin zabga mata ruwa sai iyo take a ciki kawai kinsa nai asarar kudina." Zaune na mike nai saurin cire hijabin jikina jin yanda ya jike da gumi! ina kallonsa yasa hannu yana sosa kansa idonsa kur! a kirjina. girgiza kaina kawai nayi na fara yunk'urin mikewa......Tace."Sa'ida duba dan Allah wai duk wannan gwanintar da nayi masa ban birgeshi ba cewa yake banyi daidai ba."

Tukunyar indomee din na kalla da sauri na dauke kaina jin dariya na nema ta sub'ce min indomee guda uku amma ta cika tukunya da ruwa indomeen tayi tsululu duk ta narke a ciki.........Yace." gwaggo bafa zanyi asarar kudina ba ki cinye wannan indomee ki bani dari ukuna ba." da sauri tace ." Wallahi baka isa ba ba zanci kayan atini ba hakan nan zaka daure kaci idan kuma ba hakaba Sa'ida ta baka wata indomee tunda tana da ita in yaso sai ka kaiwa babarka ta dafa maka tunda ni ban iya ba."

Ta'be bakinsa yayi yace."Sai dai na kwana da yunwa akan na kar'bi abunta ni ba shashashan namiji bane kamar yanda take kira na nafi karfin ta ciyar dani sai dai ni na ciyar da ita."

Gwaggo sakin baki tai tana kallonsa sai kuma tayi dariya da Fadin"Khalid jarumi a gida da wajan ya'ki ka burgeni kwarai da gaske yanzu dai kayi hakuri akan 'barnar da nayi maka." Girgiza kansa yayi yace."Bafa zan hakura ba bari ma ki gani." da sauri ya fara lalaben inda take ajiye Pose d'inta....
Da sauri ta ri'ke gefan rigarsa "Aa Khalid kada ka daukar min kudi wallahi zanyi maka rashin mutunci idan ka daukar kwabo a cikin jakata.....Fita nai daga dakin na barsu suna bugawa dama inda sabo sun saba idan 'yan abin arzikin na kusa suyi ta mutunci idan kuma 'yan tsiyar na kusa suyi ta bugawa, Gwaggo san kudin tsiya ne da ita duk neman da take ba zata ci a cikinta ba sai tai ta tara kudin tana 'boyewa a cewarta sai auran Sa'ida ya tashi sai tayi mata kayan daki da kudin......Pose din ya bude yaga kudi dan'kam 'yan dubu dubu duk sunfi yawa, yace." Lallai tsohuwar nan kudi ne dake duba dan Allah Jakarki kamar ta matar alhaji."

Tana kokarin fizge jakar tace"Khalid wannan kudin da kagani ba nawa bane kada ka dauki ko kwabo a ciki." Murmushi yayi yace."Haba gwaggo ina ganin kudi ki hanani kin san Allah sai na dauka." dubu daya ya zara yasa a aljihunsa ya mika mata jakarta, aikuwa ta dinga yi masa mita tana surutai dariya yayi ya kama hanyar fita daga dakin da fadin"Ki cinye indomee da kika dafa ni kuma anjima zanje tevur din mai shayi." Tace."Kaji dai dashi saboda kai zan sanjawa jakata guri haka kawai ba zaka zo kana daukar min kudi ba."

Ni dai Ina alwala ina dariya a cikin raina gwaggo san kudi Khalid son kudi koda yake dole Khalid yaso kudi tunda dan makaranta ne yanzu haka yana daf da kammala karatunsa a jami'ar Bayero dake jahar kano yana zuwa gida duk bayan wata guda yayi hutu na kwana biyu ya koma makarana..

'Dakin na shiga na sameta tana ta surutai uffan bance mata ba dan har yanxu haushinta nake ji akan irin abubuwan da take min, na gyara dadduma a nutse na fara kokarin tayar da sallah, tace"Sa'ida dan Allah ungo wannan jakar tawa ki 'boye min Khalid ya gane inda nake ajiyeta nasan kuma shikkenan kafin ya tafi sai ya tatike ni."

Ba tare dana kalleta ba nace"Ki ajiyeta nan na idar da sallah." tace"To 'yar albarka, tukunyar indomeen da sauke daga kan risho tana fad'in "Waye zai ci wannan ai ko almajiri ba zan bawa ba zubar dashi zanyi dan ni banga abinso a wannan abincin ba.....har na idar da sallah gwaggo bata fasa surutai ba nace" Yau me aka girka a gidan.''

Ta'be bakinta tayi 'kasa-'kasa tace"Kin san halin matar gidan da jarabar son d'anwake shi tayi masifaffiyar mata kawai na haifi d'ana amma tafi ni iko dashi dama nasan Rabi tana bin malamai akan Ibrahim."

Cikin mamaki na kalleta halin gwaggo sai ita surukar ta ma bata kyale ba kullum cikin zaginta take amma ba tayi a gaban idonta sai a bayan idonta dan itama Ummatu bata daukar raini mara mutuncin kanta ce nace"Gwaggo dan Allah ki daina wannan halin ki zauna lafiya da kowa yanzu meye amfanin zagin Ummatu har kina cewa tana asiri."

Baki ta rike tana kallon hanya tace."Ke! Sa'ida maganar ta isa haka kada ki d'aga murya taji amma ni tuntuni Uwale ta tabbatar min da cewa Ummatu ba'a zaune take ba tana yawace-yawacan malamai wai shin bakya ganin ko kara ta ajiye babanku baya iya tsallakawa gashi muma ta daure mana baki dik abinda tayi a gidan shine daidai sannan kice nai mata sharri."

Nace"Gwaggo ki rabu da Uwale munafuka ce wallahi tana so ta had'a ki rigima da surukar ki ita kuma ta zauna lafiya da tata idan ba hakaba meye na cewa Ummatu na bin malam......bakina ta rufe tana zazzare ido irin na rashin gaskiya tace."Haba Sa'ida nace dake ki daina kiran sunanta kada taji haba jama'a yarinya ba'a sirri da ita mtssw maganar a barta haka."

Murmushi kawai nayi na mike tsaye ina ninke dadduma, ta mika min pose din nata da fad'in "Kar'bi ki adana min kada ya shigo ya sake daukar min kudi." karba nayi na bude gurin da nake ajiye tufafina nasa key na kulle..........Da yake idan mun dauki albashi duk abinda nake bukata naci da sha dana d'aurawa ina siyan abina na ajiye duk ranar da akayi abinda bana ra'ayi sai nayi girkina naci na koshi, fita nayi tsakar gida na dauko doya a kicin na zauna tsakar gidan ina feraye wa.

Fitowa tayi daga dakin da buta a hannunta Gwaggo duk rintsi bata bari yara suyi mata wasa da butar alwalarta kullum butar ta cike take da ruwa Macace mai tsafta da kula da ibadah dama dan adam tara yake bai cika goma ba, ganin ina feraye doya yasa ta washe baki da fad'in "A lallai kice yau dadi zamu ci a gidan." Murmushi nai ina kallonta gwaggo akwai kwadayi amma bata yarda ta fitar da kudinta ta siyi abinda take so ba.

Nace"Eh lallai doya da kwai zan soya nayi miyar alayyahu saboda haka ke zaki bayar da kudin 'kwai dan banda kudi." shuru tayi tana kallona dariya ta kusa ta su'bce min.

Tace." Inji dai guda biyu zai isa." Nace"Haba gwaggo a wannan uwar doyar za'a sa 'kwai biyu guda biyar zaki siya." tace"Haba Sa'ida 'kwai biyar nawa kenan."? kai tsaye nace"Dari uku da hamsin." shuru tayi tana nazari kafin ta girgiza kanta tace"Bari dai nai sallah muyi maganar haba Jama'a yanda rayuwa nan tayi wahala kice 'kwai biyar ina laifi biyu ko uku."

Bin ta nayi da kallo ina k'unshe dariya gwaggo kenan mai kwad'ayin tsiya.......Hayaniyarsu naji yo daga waje kafin nayi wani yun'kuri sun shigo gidan su uku, babu walwala na daga kaina ina kallonsu su biyu suna sanye da kayan 'kwallo (ball) mayar da kaina kasa nayi na cigaba da abinda nake naji yace."Salim ku jira ni nasa kayana na fito." Suka ce okey kayi sauri dan Allah." cikin zuciyata nace "Aikin kenan." " Aunty Sa'ida barka da Yamma." a nutse nace" Barka Salim ya kuke." ya d'an sosa kansa yana mirmushi yace "Lafiya aunty muna fatan kina lafiya." " Lafiya Kalau nake." shuru gurin yay na minti biyu na dago kaina kawai sai naga sun zuba min ido! cikin 'bacin rai nace"Salim kaima ka fara zama mara kunya ko."? da sauri yace."Aunty mai ya faru."? girgiza kaina nayi nace"Kuje waje gashinan fitowa daga yau kada ku sake shigowa gidan nan tunda duk kun zama baligai."

Wannan magana da tayi a kunnasa ya karaso gurin yana mata kallon daya saba "Akan me zaki hanasu shigowa gida abokaina ne na 'kuruciya kin sansu kin san iyayensu kuma iyakacinsu nan bakin 'kofa ko wani yayi miki abinda bai kamata ba."

Nace"Khalid na hanasu shigowa gidan nan saboda bai kamata ba su tsaya a waje ka fito ka samesu." Girgiza kansa yayi yace." Keda Gwaggo babu nauyin auran kowa a kanku meye dan abokaina sun shigo kike fita kina yawo a titi gardawa na kallonki a ofis d'inku na malaman makaranta akwai baligan da suka ci uwar abokaina a kuyanci kike mu'amula dasu baki damu ba sai dan kawai abokaina sun shigo gida kice su daina shigowa ba zai yiwu ba."
Chapter 2 · 0% Book details