← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 90

Sashe 72

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo kuwa gabad'aya gwiwarta ce tayi sanyi kalau ruwan hawaye ya taru a idonta wannan wace irin rayuwa ce Rabi da mahaifiyarta suka jefa kansu Hakikanin gaskiya Ibrahim beyi sa'ar mace ba hannu tasa tana goge hawaye ta juya da niyyar barin gurin shi kuma ya shigo dama lokacin da muka shiga gidan yana bandaki yana wanka.....Ganinta babu kuzari ga hawaye a idonta yasa gabad'aya ya shiga damuwa kafard'arta ya rike yana tambayarta Gwaggo tsabar tausayin kanta yasa ta fashe da kuka tana girgiza kanta, rungumeta yayi a jikinsa suka fito daga gurin.....Ni dai ina daki naji shashshekar kukanta da sauri na fito gabana na faduwa nasan dama ba zasu kwashe lafiya da Ummatu ba, ganinta rungume a jikinsa yasa da sauri na karasa inda suke amma ban kalleshi ba saboda yanayin yanda yake babu kaya a jikinsa sai wando iya gwiwa gashin kirjinsa ya jike jagab da ruwa fatarshi tayi wani irin haske sai kyalli takeyi sosai ya k'ara girma gabadaya jikinsa ya bud'e ya zama k'aton gaske, gabana ya dinga faduwa ina korar shed'an a zuciyata nake tambayarsa abinda yake faruwa.

Shima ba tare da yayi min cikakken kallo ba ya bani amsa da fadin."Ban san dalili ba kawai na fito daga wanka na ganta tana kuka."

Nace."Ya za'ayi kace baka san dalili ba bayan daga 'kofar ku ta fito." 'Bata rai yayi yace."Zanyi miki karya ne."? Nace." Aa ka wuce kayi karya ai tunda ka girma amma tilas kasan abinda ya faru kawai kana 'boyewa ne." Yace."Kina nufin Ummatu tayi mata wani abu kenan."? Nace."Ko Ummatu ba tayi mata ba wasu daga cikin gurin zasu iya yi mata. Kallonta yayi da fadin."Gwaggo me sukayi miki."? Tana numfarfashi tace."Babu komai." Kai ya girgiza da fadin."Akawai dalili Gwaggo ki fad'a min waye ya ta'ba min ke na dauki mataki."

Kallonsa tayi sai kawai zuciyarta ta karye hawaye suka dinga sharara a fuskarta ga jikinta sai karkarwa yake ya dauki zafi sosai.

Hankalina da nashi ya tashi jiki na rawa muka rirri'keta muka shiga da ita dakin muka zaunar da ita kan shimfid'arta......Hawaye na share na kalleta da fadin. "Kinga irin abinda nake gudu ko? shiyasa kafin ki shiga gurin nan sai da na hana ki amma kinqi Khalid dai ba yaro bane ballanatana kice dole sai kin taso shi a gaba yazo yaci abinci gashinan kin shiga sun tayar miki da hankali."

Ya kalleni da bacin rai a fuskarsa yace."Kada ki yanke hukunci sai kinyi binkice tukkuna." Nace."Babu wani binkice da zanyi gaskiya na fad'a matar nan tsohuwa ce ya kamata a dinga yi mata uziri a gidan nan kuma duk abinda take saboda kai takeyi me zai sanya a dinga kokarin kasheta da bakin ciki."

A zafafe yace."To ya isa haka bana bukatar k'ananun magana idan Gwaggo tayi min abu dama can ta saba babu ruwan ki zaman Gwaggo da Ummatu tuntuni haka suke abunsu kowa yana da laifi a cikinsu."

Nace."Ai a matsayin ta na uwar masu gida ya kamata ace ana rangwanta mata da wasu abubuwan me yasa ba'ayi mata adalaci."

Yace."Okey yanzu dai idan na fahimta kina so ki zagi Ummatu ko wani nata ko."? Murmushi nayi nace."Wannan ba halina bane da zan zagi Ummatu da tuntuni na zageta a matsayin uwa take a gurina amma kuma duk inda gaskiya take dole ne a fad'e ta.

"Yace." To kada ki sake sanya bakin ki akan abinda ya shafi zamantakewar Gwaggo da Ummatu mutukar kin dauketa a matsayin uwarki Bana son mu samu sa'bani dake ta wannan dalilin domin ina ganin kima da mutuncin mahaifiyata.......Bude baki nayi zanyi magana ta daga min hannu a sanyaye tace. "Sa'ida kyaleshi tunda ya nuna yafi son uwarsa dani ka tashi kaje ka sallami jama'ar dake jiranka a waje.

Kallonta yayi yana sassauta fuska yace." Gwaggo keda Ummatu babu wacce tafi wata a cikin zuciyata domin kun taka muhimiyyar rawa a rayuwa a yanzu dai babu wata mace a gabana bayan keda mahaifiyata saboda haka kada kiyi wa maganata mummunar fahimta.

Tace."To naji ka tashi kaje kawai Allah yayi mana maganin masifa." Mi'kewa yayi nai saurin kauda kaina daga kallonsa shafefen cikinsa da yayi guru-guru shi yayi masifar daukar hankali tamkar wanda baya cin abinci ciki a shafe sai 'kananun gashin da ya dan kwanta a gurin! Kauda kaina nayi har ya suka gama maganarsu ya fita daga dakin Na juyo na kalleta da fadin." Gwaggo wai don Allah me ya saki kuka ne."? Sai kawai ta shiga girgiza kanta alamun abun na bata mamaki Tace." Sa'ida tun kafin na karasa shiga gurin naji muryoyinsu suna shirya mana mugun abu dani dake Suna cewa kin kashe auranki ne domin ki aureshi saboda kinga yayi kudi sannan ni kuma sai sun raba tsakanina dashi zasuje gurin malamin su yayi mana farraqu domin kada na bashi umarin auranki."
Cikin wani irin mamaki nake kallonta nace."Au Gwaggo abinda suke tunani kenan."? Tace."Eh mana kunnuwa ne suka ji ba karya nayi musu ba.'' Sunkuyar da kaina nayi ina mamakin bindiddigi irin na mutane........."Sa'ida mutukar na isa da Khalid sai ya aure ki sai naga 'karshen kiyayyar da Rabi take nuna miki kuma bayan haka sai na kuntuka mata bakin ciki babu boka babu malam sai nasa Ibrahim yayi mata kishiya zata gane bata da wayo."

"Gwaggo ki kyaleta don Allah duk sharrin ta zai koma kanta ni wallahi bana son 'kananun magana kowa yana fama da kashi a gindinsa amma yana hango na wani mutuwar aure ba akaina aka fara ba kuma ba za'a kare a kaina ba aure tsakanina da Khalid kuma idan Allah ya kaddara babu wanda ya isa ya hana."

Tace."Ki kwantar da hankali insha Allahu wannan karon sai bukatata ta biya akan ku."

Bayan sallar magariba Ummatu ta shigo dakin da abinci a jere akan tire.....Nice na iya amsa sallamar ta Gwaggo kuwa kallon mamaki kawai take mata .

Kallona tayi da fad'in."Sa'ida yaushe kika zo ne.''? Nace." Wajejan la'asar ne." Tace."Ayya lokacin ina tare da baki." shuru nai mata ta Ajiye tire din abincin da fadin."Gwaggo yau dai na gama miki abinci da wuri kuma abinda kike so nayi miki."

Da sauri tace."Rabi ki kwashe kayan abincin ki bana bukata." Cike da mamaki tace."Me yasa Gwaggo ko wani abu ne ya faru."?

Gwaggo kauda kanta tayi ta cigaba da gyara goron ta Tace."Haba Gwaggo lafiya lau fa muke zaune da juna me yasa duk sanda ki kaga Sa'ida sai ki sauya min fuska ko dai zuga ki take yi."
Da sauri na kalleta ina mamakin maganarta Gwaggo tace."Kada ki zarge ta babu ruwanta Rabi ni sharrin ki nake guda insha Allahu Ubangiji Allah zai sanjawa Ibrahim da mata tagari."

Ummatu fashewa tayi da kuka tana kallona tace."Amma Sa'ida kin cika shaid'ainiya wallahi wato daga zuwanki har kin zugata wai me na tsare miki ne."?

Nace."Ummatu dan Allah idan zaki fadi magana ki dinga taunawa ni ina ruwana da zaman ku dama ai kun saba don Allah ki daina zargina babu ruwana."

Tace."Shiyasa ai gashinan duk inda kika je sai an koro ki saboda mugun hali na gado waye zaiyi sha'awar had'a zuria dake." Gwaggo tace."Rabi kin kyauta nagode ki cigaba da zagi na kina aibata zuria ta zan nuna miki ikona idan uban farraqu zakiyi kije kiyi kada ki fasa ni Ramatu naci dubu sai ceto."

Ummatu ta dinga kuka tana fadin."Ni kam na shiga uku a gidan nan nagode Allah tunda Allah ya rufawa yaro na asiri zan umarce shi ya siya min gida na fita daga wannan masifar." Cikin jin rashin dadin maganarta nace."Don Allah Ummatu kada ki dauki al'amarin da zafi ki zauna ku fahimci juna."

A fusace! tace."Rufa min baki munafukar banza da wofi insha Allahu sai Nayi maganinki." Tana gama maganarta ta fice daga dakin a fusace!!!

Gwaggo tace."Rabu da kafura borin kunya takeyi domin tasan naji duk irin makircin da suke shiryawa to duk kaidi da sharrinsu zai koma kansu gafalallu marasa tsoron Allah."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Allah dai ya kyauta." Ta amsa da ameeen tana gyara redion ta.

Koda Kawu ya dawo ya gan ni a gidan sai ya nuna farin cikinsa ya zauna muka jima muna hira yana ta kwantar min da hankalina da addua akan Allah ya musanya min da alkairi."

Yana kokarin mikewa Gwaggo tace ya koma ya zauna tana so tayi magana dashi.

Nace."Don Allah Gwaggo ki kyaleshi yaje ya huta.'' Tace."Aa Sa'ida ai ba zan kwana da maganar nan ba sai na fada masa yasan abinda yake faruwa."

Kawu Iro ya koma ya zauna jikinsa duk yayi sanyi......Gwaggo ta shiga zayyane masa duk abinda ya faru da irin cin mutuncin da matarsa ta shigo har daki tayi mana.

Kawu ransa yayi masifar 'baci gumi kawai yake shi kam ya rasa wane mataki zai dauka akan Matar tashi kwata-kwata bata ganin darajar mahaifiyarsa.....Gwaggo tace."Ibrahim naga hankalin ka ya tashi to ka kwantar da hankalinka a yanzu abu daya za kayi wa Rabi ta shiga hankalinta shine ka 'kara aure ni dana haife ka na baka umarnin ka fara neman aure bazawara ko budurwa duk wacce kake bukata ni zan shige maka gaba.

Yace."Gwaggo naji dadin wannan maganar taki kuma insha Allahu zan fara duba macan da ta dace dani wacce zata kula min dake ita kuma Rabi Allah ya shiryeta.'' Ta amsa da ameeen ya rabbi sannan kuma inaso ka kafa mata takunkumi ma'ana ka hana ta fita zuwa ko'ina saboda idan ta fita din yawace - yawace take na malamai da bokaye.'' Yace."Insha Allahu yau zata ga b'acin raina zan nuna mata cewa ta za'bi daya aure ko zaman gidansu." Gwaggo tace."Yawwa haka za kayi mata jan ido amma ka kula fa kada kayi abinda bai dace ba." Yace."Insha Allahu Gwaggo." Sallama yayi mana ya fita daga dakin.
Gwaggo tace."Haba jama'a Rabi ta zame mana annoba babu abinda zai sanya ta dawo nutsuwarta sai kishiya zata san ni takewa rashin kunya." Nace."Gwaggo ki bar maganar haka tunda dai kin fada masa shikkenan Allah yasa karshen matsalar ce tazo." amsawa tayi da ameeen tana kokarin janyo kwanonin abincin dake gabanta.

Tare muka ci abincin muna hira sai bayan an gama *taskar labarai* na gyara mata shimfid'a tace."Sa'ida ai ba zan kwanta ba sai naga shigowar Yaron nan."
Chapter 72 · 0% Book details