← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 90

Sashe 39

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kashe wayar nayi na ajiyeta kan mirror na futa falon, shuru babu kowa da alama yaran sun tafi makaranta tunda litinin ce. gurin cin abinci na nufa naja kujera na zauna wato dai nice bare a gidan nice wacce bata da mutunci da galihu ban isa a zauna tare dani a ciki abinci ba tabbas badan kada na cutar da kaina da yunwa ba to da babu abinda zai sanya na zauna naci abincin gidan amma babu komai karshen wata na dauki albashina zan sayi komai nawa na dinga ciyar da kaina wannan shawarar na yanke a cikin raina.

To har na gama breakfast din Aunty Murja bata sauko ba sai kawai na yanke shawarar hawa saman na gaisheta.

Na jima a bakin kofar ina knocking kafin naji motsinta ta bude kofar dakin muka had'a ido da juna.

Fuskarta a sake tace."Aa Sa'ida kece ashe shigo mana." Kasa shiga nayi sabida nauyi tana sanye da wani gajeran wando da riga mai kamar breziya da madauri a wuya nonowanta duk a waje bayan ta ma haka.

Na tsaya daga bakin kofar da fadin"Dama naji shuru baki sauko ba nace bari nazo mu gaisa." Murmushi tayi tace."Kin ga ni wallahi tunda nasha maganin mura ya kashe min jiki nake ta bacci mijinki ma ban san lokacin daya fita ba."

Nace."Ayya sannu Allah ya sawa'ke." ta amsa da "ameeen da fad'in " Ki shigo mana." cikin ya'ke nace"Aa aunty zanje nayi ayyuka a dakina ne anjima idan na gama sai nazo muyi hira."

Tace."Tom shikkenan babu damuwa." sallama nayi mata na sauka ina kokarin shiga dakina naji sallama da sauri na juya domin na dauka Hauwwa ce. wata hamsha'kiyar mata ce taci kwalliya har ta gaji kana kallonta kasan naira ta zauna..

Nace"Sannu da zuwa hajiya." ta amsa fuska a sake tana min wani irin kallo kafin tace."Kece amaryar Murja ko.''? nace."Eh nice amma ke d'in 'yar uwarta ce ko dan naga kuna kama."

'Yar dariya tayi tace"Haka mutane suke fada Aa Murja ba 'yar uwata bace ta jini 'Kawata ce dai." Nace."Ayya sannu da zuwa tana sama sai ki hau ki sameta."

Tace."Okey babu damuwa.'' Juyawa nayi domin bude dakina naga ta bini da kallo tana murmushi, al'amarin ya dinga bani mamaki! irin murmushin da Aunt Murja takeyi min matar ma irinsa take........Gefen gado na zauna abun na cigaba daure min kai.

'Karfe biyu shaura Hauwwa ta karaso gidan, bayan mun gaisa ta dinga bina da kallo tana girgiza kanta kafin tace."Sa'ida kwana biyu kacal naga duk kin sanja kin wani hargitse dan Allah me yake damunki.'?

Ajiyar zuciya na sauke nace."Hauwwa matsala mai girma nake fuskata a gidan nan." Zama ta gyara tana kallona, idanuwa na suka ciko da ruwan hawaye na shiga bata labarin abunda ke faruwa.

Kanta kawai take girgizawa kafin tace." *AI GA IRINTA NAN!* Sa'ida babu irin shawarar da ban baki ba akan mutumin nan kika rufe idonki kika aureshi gashinan kwana biyu kacal ya nuna miki akuyanci me ake da auran irinsu Alhaji Nura kayan ba'kin ciki da takaici ai wallahi gwara na auri 'karamin yaro na raine shi nasan komai rintsi ni zan mora amma duba dan Allah kwana biyu da yin aure kin zama tamkar wata zautacciya."

Nace."Hauwwa dan Allah ki bar wannan maganar Alhaji Nura fa lafiyarsa lau tsabar iskanci ne da wulakanci yasa yake min haka tunda ai na fad'a miki hujjarsa ta 'kin sakin jiki dani saboda kada na haihu bayan sun tsara rayuwarsu shi da matarsa."

Tsaki taja tace."Eh ai na fahimta mayaudarin banza da wofi kawai to ke yanzu wace shawara kika yankewa kanki ko kina nufin a haka zaki cigaba da zama da sha'awa."

Nace."Shine ai na kira ki domin ki bani shawara."

Shuru tayi na minti biyu kafin tace." Sa'ida ki rabu da mutumin nan shine alkairi a gare ki ni dai wannan shawarar ita zan baki."

Gabana na wani irin fad'uwa nace."Hauwwa wace irin magana ce wannan? aure kwana biyu ki fadi irin wannan maganar gaskiya bata dace ba ki bani shawarar arziki mana."

Dariya tayi tace."Duk wata shawarar da zan baki bayan wannan take wallahi idan kika cigaba da zama da mutumin nan zuciyarki sai ta buga irinsu suna nan da yawa masu kashe matansu da bakin cikin su."

Shiru nayi ina kallonta tace."Idan kuma kinga ba zaki rabu dashi ba to sai ki dauki tsatstsauran mataki a duk lokacin daya kusance ki sai ki hana shi tunda zalinci baya barin sa ya biya miki bukatar ki."

Nace."To kinga wannan shawarar ita zan duba a cikin shawarwarin ki amma maganar kashe aure sam bata taso ba."

Tace."Tom shikkenan sai ki kwada ki gani mybe idan kikayi masa butsu ta wannan hanyar zai dinga dogon zango a kanki tunda kin ce lafiyarsa lau ba rashin kuzari bane wulakanci ne irin nasa.

Murmushi nayi nace."Hakane Hauwwa Alhaji Nura ragal yake kawai 'keta ce nima kuwa zan gwada masa tawa." Dariya tasa ta bani hannu muka tafa.

Sai da tayi sallah la'asar muka ci abinci sannan tayi shirin tafiya, tare muka fito falo wanda yayi daidai da saukowarsu daga sama.

Nace."Hauwwa ki tsaya ku gaisa da aunt Murja ko." Tace."Okey babu damuwa.

Muna tsaye suka 'karaso dukkaninsu fuskarsu a sake da walwala aunty Murja tace."Ashe kema bakuwa kikayi.''? Nace."Eh wallahi 'kawata ce Hauwwa gurin aikin mu daya."

Tace."Ayya Sannu.'' Hauwa ta amsa da "yawwa aunty ya gida ya yara."? tace."Alhamdulillahi." Hajiya Aziza na murmushi tace."Ai sai muje na rage miki hanya ko."?

Hauwwa tace."Nagoda hajiya amma nima ina da abin hawa.'' Tace."Okey to babu damuwa sai mu fita tare ko." Tace."Eh hakan yayi.'' Ta kalleni da fad'in "Sa'ida sai munyi waya kenan amma yaushe zaki koma gurin aiki."? Nace." Insha Allahu sati na sama." tace."Tom shikkenan Allah ya bamu alkairi." Nace."Ameeen ya Allah nagode k'awata." Aunt Murja tace."Muje mu taka musu." bayansu muka bi kowacce ta shiga motar ta suka fita daga gidan muna daga musu hannu da fatan alkairi.

Tare muka koma gidan ita ta hau sama ni kuma na bude dakina na shiga ina tunanin shawarar da na yanke akan abinda yake faruwa.

To yau ma dai ban san lokacin da ya dawo ba sai da na fito falo na same shi a zaune suna hira da ita ga yaran su suna wasa, tsabar haushi da takaici ya hana ni kulashi ballantana nai masa sannu da zuwa.

Gurin cin abinci na zauna naci na koshi na bar gurin ita kanta aunty Murjan haushinta nake ji sabida na gane itama fuska biyu gareta.

Sai da bacci ya soma daukata ya shigo dakin, na dinga kallonsa ina daga kwance har ya gama shirye shiryen sa yazo ya tsaya a kaina....."Sa'ida wacece tazo d'azu."? tambayar da yayi min kenan....Na mike zaune ina kallonsa ya sake maimaimata maganarsa." Wacece tazo gurin ki d'azu."? Nace."Kai waye ya fad'a maka wata tazo."? a fusace! ya daga min hannu da fad'in "Wace irin magana ce wannan a maimakon ki bani amsar tambayata sai kuma ki tambaye ni..

*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA GUDA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*

_*Ina kaunar ku iyayena ina kuma alfahari da irin kaunar da kuke nuna min💜🥰*_

*45&46*
Raina ne ya 'baci ganin yanda yake daga murya sama kamar zai doke ni nace."Kayi hakuri dan Allah ni banga abin daukar zafi ba idan kana so kasan wacce tazo guri na sai kaje ka tambayi wacce ta fada maka cewa yau nayi bakuwa."
Wani irin kallo yake min yana girgiza kansa yace."Sa'ida ashe baki da kunya dama? ni kike fadawa wannan maganar?
Hawaye na share nace."Alhaji wace magana na fada maka mai zafi! al'amarin ne ai ya bani mamaki kuma banta'ba tsammanin aunty Murja fuska biyu gare ta ba."
Yace."Okey yanzu mai kike nufi."? kai tsaye nace."Ina nufin abubuwa da yawa." Girgiza kansa yayi kafin yace."Ni ban hana wani naki yazo gidan nan ba kawai dai sintiri ne bana so inace duka-duka yau kwanan ki biyu da tarewa a gidan nan mai zai sanya a fara yi min sallama a gida.

Fuskata na goge nace."Babu wanda zan hana shi zuwa cikin gidan nan tunda dai kasan ina da jama'a bayan haka kuma ina da 'yan uwa da dangi masu yawa saboda haka ni dik wanda yazo gurina ina maraba dashi."

Rai a 'bace yace."Ni kike d'aga wa murya ko."? shuru nayi yace."To bari ki ji abinda baki sani ba Murja da kike gani ta fiki 'yan uwa da dangi da jama'a amma saboda tana bukatar zaman lafiya dani tabi doka ta a kan dauki dogon lokacin kafin kiga wani dan uwanta a cikin gidan nan saboda haka kema yana da kyau ki kiyaye.

Nace." 'Karya take aunt Murjan." cike da mamaki yake kallona.

Na cigaba da cewa" D'azu itama ai tayi bak'uwa mai yasa bata fada maka ba saboda ita ta cika munafukace magulmaciya."

"Murjar kike kira da wannan sunaye." ? a hasale nace."Eh ita din fa ai ta amsa duka sunayen."

Rai a 'bace ya juya ya fita daga dakin. tsaki naja mai karfi da fadin"Mijin tace kawai."

Koda ya fita daga dakin kai tsaye bene ya hau ya sameta a kwance da wayarta a hannunta tana latsawa, ganin shigowarsa yasa tayi saurin kashe wayar ta ajiyeta ta mike zaune tana kallonsa.

Zama yayi kusa da ita rai a dagule! ta dafa kafadarsa da fadin "Abban Yusura ya akayi ne naga ka shigo fuska a 'bace."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Murja na lura yarinyar nan Sa'ida bata shigo gidan nan da sigar son zaman lafiya ba kamar ni zata tsaya tana jayayya dani akan hukuncin dana yanke a gidana saboda na kawo mata misali dake shine take zagin ki."

Murmushi tayi alamun abun bai mata ciwo ba tace."Sai hakuri Abban Yusura kasan ko wace mace da irin halinta wallahi nima yau haka ta yini tana yar min da habaici ban san meye dalili ba amma dai ka cigaba da hakuri da halinta.''

Yace."Ai kuwa zata gane kuskuranta Murja babu wata mace da zan aura ta taka martabarki ban nuna mata kuskuranta ba saboda haka na bar dakinta har sai na koya mata hankali."

Murmushin samun nasara tayi tace."Haba Abban Yusura kayi hakuri dan Allah ka koma dakin kaga amarya ce ka cigaba da rarrashinta.
Chapter 39 · 0% Book details