Sashe 44
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Hannu na mika na dauki wayar ina dubawa Alhaji Nura ne sai naji wani sanyi a cikin raina text d'inshi na gani da sauri na shiga ina dubawa......Hakuri yake bani akan abinda ya faru wai nayi hakuri insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma idan anjima zai zo ya daukeni.
Zuciyata tayi sanyi kad'an amma dai duk da haka idan na koma sai na nuna masa 'bacin raina.
A nutse nace."Gwaggo Alhaji Nura ne yake baku hakuri akan abinda ya faru yace insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba kuma anjima da daddare zai zo mu tafi."
Ta'be bakinta tayi tace."Ai sai ki zuba ruwa a 'kasa kisha saboda murna."
Kallonta nayi ta gyda min kai da fad'in "Eh mana ai kinga kuka da damuwa ya 'kare zaki koma d'akin ki tunda anan akan qaya kike."
Takaici ya hanani ce mata komai kawai na d'auki kofin kunu na fara kur'ba ina duba wayata.
Katsaham! naji maganarsa a kunnena" Aunty Sa'ida idan kin koma gidan mutumin nan waye zai dauke miki bukatunki na yau da kullum.
Babu walwala a tare dani nake kallonsa, shima ya 'bata rai da fad'in ''Kin kawo 'kararsa akan baya biya miki bukatarki ta aure sannan baya so ya haihu dake amma sabida rashin sanin ciwon kai zaki koma gidanshi meye amfanin zama dashi a haka kodai kwad'ayin kud'insa kike."?
Na dinga jin wani irin gumi mai zafi na tsatstsafo min a jikina shin ko dama maganar da sukeyi kenan a lokacin da na tashi na ga sun nuna alamun rashin gaskiya! "Yanzu Gwaggo meye amfanin yin wannan maganar da Khalid? me ya shafe shi a ciki da har zaki zauna kina fada masa halin da nake ciki a gidan aurena."
Shuru tayi bata tanka min ba, naji wasu hawaye masu zafi suna kokarin zubo min na kalleshi raina a 'bace nace."Wato dai ba kaji gargadin da mahaifinka yayi maka ba ko."
Cikin rashin tsoro yace."Ai magana ta wuce aunty Sa'ida na rabu dake kije kiyi rayuwar auranki wannan magana kuma da ki kaga nayi miki ba wai da wata manufa nayi miki ba ina jin tausayin halin da zaki shiga anan gaba."
Nace."To ina ruwan ka da dukkanin halin da zan shiga a gidan aurena bana so ka nasa bakin ka akan al'amuran da suka shafe ni ka tsaya a matsayin ka."
ta'be bakinsa yayi yace." To shikkenan aunty Babbah na daina saka bakina akan abinda ya shafe ki tunda bakya bukata."
Nace."Hakan shi zai fi maka alkairi." Shuru dakin yayi kowa yana sabgar gabansa.....Yace."Gwaggo kin san wata yarinya Jamila 'yar Kawu Garba 'kanin Ummatu."
Da sauri tace."Eh kwarai kuwa nasan yarinyar ko ba wata 'yar fara siririya ba."
Yace."Eh ita ce Ummatu take fada wai na nemi auranta."
Gwaggo ta rangwad'a buda tana washe baki da fad'in "Kai Alhamdulillahi amma naji dadin wannan al'amari tabbas wani hanin ga Allah baiwa ne Khalid nima na goyi da bayan ka auri Jamila domin ta cancanta.
Murmushi yayi yace." To shikkenan Gwaggo ku cigaba dayi min addua akan Allah ya tabbatar mana da alkairi.'' ta amsa da ameeeen ya rabbi.
Gabad'aya ji nayi na kasa nutsuwa a gurin jikina yayi bala'in sanyi jin maganar da sukeyi fita nayi na bar musu dakin na zauna baki soro ina dube-dube a wayata gabadaya na rasa abinda yake min dadi.
To koda Kawu ya dawo da yamma na fada masa sa'kon Alhaji Nura sai yace."To Alhamdulillhi dama jiya na fada miki cewa yau ne karshe idan baiyi magana ba zamu tattauna da Alhaji Shamsu to tunda yace zai zo ya daukeki zan zauna zaman jiran zuwan nasa.
Nace."To shikkenan Kawu........Bayan sallar isha'i Alhaji Nura yayi parking din motarsa a kofar gidan ya fito daga motar cikin lafiyayyar shadda sai maiko take yana baza 'kamshin turarensa Khalid dake zaune cikin abokinsa ya dauke kansa dan koda Alhaji Nuran ya 'karaso gurin yana musu sallama bai amsa ba su Salim ne suka amsa Ya kalli Khalid da fad'in ''Ko zaka kira min Sa'ida ne." Kai tsaye yace."Alhaji ka kirata a waya mana."
Ya duba wayar hannunsa da fad'in "Tun kafin na karaso nake kiran wayarta bata daga ba mybe tana wani uziri ne."
Jim yayi na minti biyu kafin ya miqe ya shiga gidan.....Lokacin na fito daga wanka ya tsaya yana kallona tsaki naja zan wuce shi yace." Sai kiyi maza ki kimtsa wancan lusarin mijin naki yazo yana jiran ki a waje."
Uffan bance masa ba na wuce shi na barshi a gurin a tsaye. dakin na shiga a gurguje na soma shirya jikina...
*52&53*
"Mijin naki ne yazo ne."? Gwaggo ce ke magana tana zaune akan dadduma da carbi a hannunta. A nutse nace." Eh shine yazo yanzu." shuru tayi ba ta sake tankawa ba har na gama abinda nake na fita daga dakin.
Yana tsaye a soro kamshin turaransa duk ya game gurun. babu walwala a tare dani na gaishe shi. sai naga ya saki fuskarsa yana amsawa sai kallona yake yana murmushi.
Shuru gurin yayi na 'yan mintina kafin yace."Sa'ida ina fatan kinyi hakuri akan abinda ya faru tsakanina dake sharrin shed'an ne kuma bana fatan wani sa'bani mai muni ya sake had'a mu."
Murmushin takaici nayi nace." To naji dadin maganarka kuma ina fata har cikin zuciyarka kake maganar domin ni tuntuni na dawo daga rakiyar ka."
D'an murmushi yayi yana kallona yace."Kada ki damu Sa'ida wannan magana har cikin raina nakeyi miki insha Allahu zan gyara kuskure na."
Ajiyar zuciya na sauke ina jin sassauci a cikin zuciyata nace."To ya maganar aikin nawa."
Shuru yayi kansa a kasa yace."Sa'ida ki ajiye batun aiki a gefe kwata-kwata bana ra'ayin matata ta dinga yawo a gari inada kishi mai tsanani."
Na bude baki kenan zanyi magana Kawu ya shigo soron ganinmu a tsaye yasa ya tsaya babu yabo babu fallasa suka gaisa a tsakaninsu.
Kawu yace."Alhaji ai tun shekaran jiya muke tsammanin zuwanka shuru babu kai babu labarinka."
Cikin jin nauyi yace."Malam Ibrahim a gafarce ni wallahi uzirurru ne sukayi yawa."
Kawu yace."To babu laifi ai Allah ya taimaka." ya amsa da ameeen ya Allah"
Kawu yace." Sa'ida tazo mana da magana tana kuka wannan dalilin yasa nace tayi hakuri a saurari zuwanka domin kaima muji ta bakinka.
Yace."Malam Ibrahim d'an sa'bani ne muka samu ni da ita wanda ya sanya ta yanke hukuncin zuwa gida a gaskiya al'amarin beyi min dadi ba ko kadan."
Kawu yace."Yanzu kana nufin dama ba kai kace tazo gida ba." ? Ko kunyata beji ba yace."Kwarai kuwa ni dai bance tazo gida ba nayi mata fada da nasiha akan abinda tayi min na rashin kyautawa."
Kawu ya juyo da sauri yana kallona a lokacin da nake mamakin 'karyar da mutumin nan ya shirga da girmansa da komai amma baya jin kunyar karya.
Kawu yace "Sa'ida ina gargadi akan duk irin sa'banin da zaki samu da mijinki kada ki sake cewa zaki dawo gida ki zauna ki bashi hakuri ku fuskanci juna aiki kuma tunda yace baya so sai ki hakura."A sanyaye nace." To shikkenan Kawu duk abinda kace haka za'ayi.
Ya juya yana kallonsa da fadin"Alhaji a kara hakuri da lamarin mata dan Allah ku zauna lafiya da iyalanka."
Ya amsa da ameen insha Allahu zanyi kokarin ganin na kawo daidaito da zaman lafiya a gidana.
Cikin farin ciki Kawu yace."Yanzu zaku tafi kenan.
Yace."Eh kwarai kuwa." ya kalleni da fadin "Kiyi maza kije kuyi sallama da mutan gidan yana tsaye yana jiranki."
Amsawa nayi da to Kawu da sauri na shiga gidan domin dauko jakar kayana
Yana dogare a bakin kofar dakin Gwaggo suna magana na shiga gidan har na karasa bakin kofar bai kauce min hanya ba sai da nayi masa magana tukkuna ya dan matsa hanyar na duba naga ba tada da spece gurin wuce wa jikinmu zai iya had'uwa.
Kallonsa nayi yana duba wayarsa ya wani murtuke fuska nace."Khalid ko ba kaji ne ka matsa ka bani hanya na wuce." Gwaggo da sauri tace."Ke kam Sa'ida kin fiye neman fituna wace hanya zai baki bayan wacce ya matsa miki.
Nace."Gwaggo duba da kyau ki gani a bakin kofa ya tsaya hanyar ba zata isheni ba.
Gurin take kalla kafin tace."Jarumi bata guri ta wuce kada tayi maka wani sharrin.'' Ba tare da yace uffan ba ya shiga dakin ya zauna a kusa da ita suka cigaba da magana.
Kallonta nayi da jakar kayana a hannuna nace."Gwaggo ni zan koma." baki a bude tace."Ke kadai zaki koma dakin naki babu dan rakiya kuma saboda ke ki ke iko da kanki ba zaki tsaya Kawunki ya dawo su tattauna magana ba.
Nace."Gwaggo yanzu haka Kawu da Alhaji suna tare kuma sun tattauna dik maganar data cancanta."
Shuru tayi tana kallona kafin tace."Ashe ni ban isa ya shigo ya gaishe ni ba kenan.'' Tunda tafadi wannan maganar nasan neman magana take sai kawai na kama hanyar fita ba tare da nace mata komai ba.
Tace."Ai shikkenan Allah ya sa'ba halaye sai ki cigaba da hakuri tunda ke ki kaga zaki iya." shuru nayi mata nasa takalmana gurin Ummatu na nufa nayi mata sallama na fito.
Khalid kuwa kasa sukuni yayi ya rasa abinda ke damunsa kishi mai zafi ya dinga taso masa Gwaggo data fuskanci yana cikin damuwa sai ta dinga rarrashinsa tana tausar zuciyarsa jinta kawai yake da kunnensa amma sam baya fahimtar abinda take fada.
Tun a mota yake jana da hira ni dai jinsa kawai nake da kunne dan na kasa sakin jikina dashi kafin mu shiga gidan sai da ya tsaya ya sayi kaji da yoghot masu sanyin gaske.
Aunty Murja ita da yaran suna zaune a falo suna kallo muka shiga muka samesu.
Babu yabo babu fallasa ta amsa gaisuwata gabadaya ta rage walwala komeye dalili oho.
Nima ban wani zauna a falon ba na mike da jakar kayana na bude dakina na shiga......to har nayi shirin kwanciya bai shigo ba raina ya 'baci sosai dan koda ya shigo dakin sai da ya fahimci hakan sai ya shiga bani hakuri yana inda-inda nace."Alhaji wallahi idan ba kayi da gaske ba aunty Murja zata kai ka wuta gabadaya na lura tsoronta kake ji shin wai itace take auranka ko kaine kake auranta."?