← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 90

Sashe 16

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

lokacin ni kadaice zaune a falon Ummah ina karyawa, jin kira ya shigo wayata dake gefena a ajiye yasa da sauri na kai hannuna kan wayar kwata-kwata ban kawo shi bane sai da na duba naga number sa akan wayar. tsaki naja na mayar da ita na ajiye a nutse na cigaba da abinda nake.

Ya kira kusan sau hudu bata dauka ba jikinsa yayi sanyi sosai kuma ransa ya 'baci da abinda tai masa yanke shawarar tura mata text yayi kamar haka."

_*Aunty Sa'ida ina fatan kin tashi lafiya na kira wayarki babu adadi sabida wulakanci kin'ki dauka kin tafi kin bar baya da kura a gida saboda ke Baba ya kori Ummatu gidansu bayan haka kuma Gwaggo tana nan cikin damuwa ko abinci ta kasa ci kiyi hakuri ki dawo gida idan ni nake takura miki to ina mai tabbatar miki da cewa gobe i yanzu ina skull saboda haka ki dawo gida saboda farin cikin masu kaunarki.*_

Text din na duba jikina yayi sanyi jin cewar Ummatu na gidansu me yayi zafi da Kawu Iro zai yanke irin wannan hukuncin sai duk naji banji dadin al'amarin ba.

Dakin ta shigo ta sameni a zaune ga kayan break din a gabana na kasa ci tace."Lafiya kika zabga tagumi haka."?

A sanyaye nace."Umma wai kinji Ummatu tana gidansu saboda abinda tayi min Kawu Iro ya yanke mata wannan hukuncin."

Cikin rashin jin dadi tace."Ikon Allah me yayi zafi shi kuwa da zai yanke irin wannan hukuncin a gaskiya ban Ji dadi ba wallahi."

Nace."Nima gabadaya jikina ya mutu wallahi a cewarsa wai ba zata dawo ba har sai na koma gidan.''

Umma shuru tayi tana girgiza kanta kafin tace."A gaskiya Ibrahim ya yanke hukuncin da bai da dace ba ai bai kamata da girmanta da komai yayi mata haka ba."A sanyaye nace." Nima dai haka na gani." tana kokarin bud'e wardrobe d'inta tace."To Allah ya shiga cikin al'amarin ya sasanta tsakaninsu." na amsa da "ameeen ya Allah."

Khalid kai tsaye can babban gida ya nufa gidansu mahaifiyar tasa dake unguwar dala gidan yawa ne irin na gado duk wanda ya tashi a gidan yake aure ya zauna kafin Allah yayi masa nasa shiyasa gidan kullum yake a cike da yara kowanne da nasa .

Kai tsaye bangaran su Mahaifiyarsa ya nufa ya same su suna karyawa da koko da awara zama yayi kusa da kakarsa mai suna Baito yana tsokanarta ganin yanda ta tasa bokitin koko a gabanta tana sha. Tace."Kai ma idan kana sha sai na zuba maka badan halin Ubanka ba."

Yace."Aa bana shan koko kashe min jiki yake." shuru tayi ta cigaba da kur'bar kokonta yace."Baito naga kamar haushina kike ji."

A fusace! tace" Ba dole naji haushi ba Khalid jiya da bakin cikin kakarka da babanka na kwana saboda tsabar rashin mutunci su koro min yarinya cikin dare mai tayi musu da zafi da har zasu yanke mata wannan hukuncin."?

Yace."Baito dan Allah ki samu nutsuwa muyi magana ta fahimta yanzu ina Ummatu take."?

Tace."Tana Bandaki." shuru yayi na minti biyu kafin yace." Baito Ummatu bata fad'a miki laifinta ba ko."?

Tace."Ta fad'a min akan wannan lalatacciyar yarinyar ubanka ya koro ta.''

Khalid yaji kamar ta soka masa wu'ka a ma'koshi yace."Baito bai kamata ba abinda kukeyi kuma fa kun haifa kina da 'ya'ya da jikoki bai kamata ki dinga aibata d'an wani ba yau ko gaskiya ne zargin da kukewa auntyn Sa'ida bai kamata ku dinga zaginta kuna la'antar ta ba kamata yayi kuyi mata adduar shiriya.''

"Allahu akbar! Khalid ka gama nasihar ko baka gama ba."? Tafad'a tana masa wani kallo. yace." Da alama maganata bata gamsar dake ba."

Da sauri tace."Ta ina kuwa zata gamsar dani bayan nasan karya kake kana fada ne kawai dan ka kareta nan Jamila take sheda mana irin lalatar da takeyi da maza a makarantarsu saboda haka maganar Jamila ba karya bace Sa'ida bata da kintsi da kamun kai."

Jamila 'yar yayan Ummatu ce da suke zaune a cikin gidan Jamila budurwace 'yar kimanin shekara goma sha takwas tana zuwa makarantar da Sa'ida take koyarwa ta *Hajara Buhari* dake goran dutse.

Khalid yace."Jamilan ce tazo tana fad'in wannan maganar."? Baito na kokarin yin magana Ummatu ta karaso gurin da sauri tace."Rabi kinga Khalid daga zuwansa ya soma kalubalantata akan na fadi gaskiya ashe har Sa'ida ta fiki kima da mutumci a gurinsa."

Ummatu ta ajiye butar dake hannunta rai a 'bace tace."Baito aini tuntuni na gama magana wallahi tallahi duk ranar da yaron nan ya sake shiga sabgar Sa'ida to sai yaga abinda zai faru dashi."

Khalid yace."Ummatu dan Allah ki daina wannan maganar aunty Sa'ida 'yar uwata ce bai kamata ki raba zumuncin dake tsakanina da ita ba."

Tace."Ai nima dama ba zumuncin ku nace zan raba ba abinda nake nufi shine ka raba kanka da ita tunda duk wasu alamu ka nuna kana sonta in banda rashin hankali irin naka Khalid me zakayi da wannan yarinyar tsohuwa gata mara daraja da kamun kai kai yanzu ba zakaji kunyar auranta ba."

Yace."Ummatu babu kunya a cikin abinda ya zamanto halas dan aunty Sa'ida ta girme ni hakan ba zai hanani na aureta ba tunda ba haramun bane.''

Baito tace."To ba zaka aureta ba d'in Khalid ba zaka lalata mana zuria ba kaje ka nemo wata ka aura idan baka samu ba kazo gida ka duba gamu nan da 'yan mata kyawawa masu da kyau da duk abinda ake bukata."

Shuru yayi ransa duk a 'bace ya tsani yaga suna nuna k'yamarsu akan auntynsa a ganinsa sam bata cancanci haka a gurinsu ba.

A cunkushe yace."Dama ni nazo ne domin nayi muku sallama idan Allah ya kaimu gobe zan koma makaranta''

Baito tace."Wace makaranta kuma? dama baka gama karatun ba."?

Yace." Akwai sauran kad'an." Tace."To Ubangiji Allah yasa daga ka gama ka samu aiki kaga sai kayi auranka da hujja ni nafi so ma kazo gida ka duba wallahi ina yi maka sha'awar Jamila." tana 'yar dariya ta 'karasa maganar.

Hararar gefan ido yayi mata yana kokarin mi'kewa yace."Baito ni dai Namiji ne babu wanda zai yi min auran dole."

Ummatu tace."Khalid magana kake so ka fad'a mata saboda baka da kunya."?

Girgiza kansa yayi yace."Aa Ummatu kiyi hakuri dan Allah abar maganar amma ni kada a 'kara yi min maganar wata Jamila bana ra'ayinta."

Ummatu ta fusata sosai tace." 'Yar d'an uwan nawa kake k'yamata? meye aibun Jamila yarinya kyakykyawa fara mai kuruciya a jika."

Shuru yayi bai tanka ba yasa takalmansa Baito tace."Ai ni mamaki ma ya hana ni magana 'kiri-'kiri yaron nan yana nuna yafi kaunar dangin Ubansa akan na uwarsa."

Khalid dai baice komai ba ya kama hanya ya fita daga gidan gabad'ayansu suka bishi da kallon mamaki!! bayan fitarsa Baito tace."Rabi hak'ika zama bai ganki ba tilas ki fara neman taimako akan yaron nan idan ba hakaba anan gaba cewa zaiyi ba ke kika haifeshi ba."

Ummatu ta sunkuyar da kanta ranta idan yayi dubu ya 'baci tace."Baito maganarki gaskiya ce Khalid kwata-kwata baya ganina da mutunci baya jin maganata sai ta kakarsa duk abinda Gwaggo tace shine daidai a gurinsa ni ya raina ni alhalin ni na haifeshi kuma mutukar za'a zagi Sa'ida a gabansa sai ya nuna 'bacin ransa saboda haka dole na nemi taimako a gurin malamai su karkarto da hankalinsa kaina dan na rantse ba zai auri Yarinyar nan ba."

Baito tace."Abinda ya kamata kiyi kenan kada kiyi sanya idan anjima ki shirya sai muje gurin Malam Saminu zai taimaka miki akan lamarin."

_Allah kasa mu dace jama'a wai uwa ce take d'ora 'yarta a hanyar zuwa gurin malami a maimakon tayi wa d'anta kyakykyawar addua sai mugun baki take masa 'karshe ma zata kaishi gurin malami Allah ya kyauta yasa mu gane_

Khalid na daf da fita sukayi karo da Jamila zata shiga gidan washe baki tayi da fadin"Laa Yaya Khalid ina wuni."? Kallon banza yayi mata kafin ya ratseta ya wuce ba tare da ya amsa gaisuwarta ba, haushinta yake ji sosai akan k'azafin da tayi wa auntynsa.....Jamila a sanyaye tabi bayansa da kallo gabanta na faduwa itakam ya zatayi ne Allah ya d'ora mata kaunarsa a cikin ranta...jiki a mace ta shiga cikin gidan.

Gwaggo na zaune a tsakar gida ita kad'ai tayi suguri abin duniya duk ya isheta Sa'ida kawai take tunani idonta akan kofar shigowa gidan daga taji motsi zata zabura ta kalli kofa.....Uwale ta rangad'a sallama cikin gidan.

Gwaggo ta amsa mata tare da gyara mata gefanta ta zauna suka shiga gaisawa....Uwale tace."Dama nazo ne naji inda aka kwana shin ina fatan kuna ganin kyawun maganin nan."?

Gwaggo ta sauke ajiyar zuciya rai a 'bace! tace." Ai Uwale Yarinyar nan ta'ki bani had'in kai wallahi da 'kyar ma ta bari aka turara maganin sau biyu daga nasa turaran a wuta zata dinga masifa ta fita daga dakin ta barni a ciki ina shakar haya'kin ke a takaice ma ta gudu daga gidan tun jiya."

Uwale ta rike ha'ba cikin mamaki tace."Kinji ko ai alamun da akwai iska a tare da ita kenan tunda gashi sun hanata zama a gidan saboda turaran da kikeyi musu."

Gwaggo tace."To hakan zata iya kasancewa amma ni ina tunanin abinda Rabi tai mata ne yasa ta tattara kayanta ta gudu."

Cikin son jin gulma Uwale tace."Oh! me kuma Rabin take mata."? Gwaggo ta shiga bata labarin abinda ya faru...Uwale tace."Ai kinga Rabi ko gado tayi dan mahaifiyarta Baito mara mutunci ce babu irin sharri da kazafin da ba tayi wa kishiyoyinta ba ni dama tuntuni nasan Baito ba mutuniyar kirki bace."

Gwaggo tace.''Kice dai Rabi gadon mugun hali tayi."? Uwale ta 'bantari gora ta mi'ke kafarta a kan tabarmar tace"Wallahi kuwa Sau nawa muna had'uwa da ita a zauran malam ai shiyasa kullum nake fad'a miki cewar sai kin tashi a tsaye akan Rabi domin ita da mahaifiyarta biye-biyen malamai suke."

Gwaggo tayi shuru tana jimanta al'marin.....Uwale ta yunkura da fad'in "Gwaggo ni zan tafi dama unguwa zani nace bari na shigo mu gaisa na kuma tambayeki halin da ake ciki."

Gwaggo tace."To Uwale nagode sosai sai kin dawo nazo gidan naki domin mu yanke shawarar yanda za'ayi domi gaskiya maganar Rabi da mahaifiyarta ya tsaya min a rai."
Chapter 16 · 0% Book details