← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 90

Sashe 73

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nace."Gwaggo don Allahi kiyi kwanciyarki har yaushe zaki zauna zaman jiran shigowarsa tun dazu kike gyangyadi fa.''

"Aa Sa'ida ki bari dai na zauna na jira shi na riga na saba sai ya shigo nake kwanciya." Nace."To ai shikkenan ni zan kwanta sai da safe." Tace."Allah ya tashe mu lafiya." amsawa nayi da ameeen na gyara kwanciya ta kan gadon k'arfen ta.......
*94*
Hayaniyar sa naji a saman kaina a furgice na bud'e idona ina kallonsa yana tsaye a kaina yana surutai Gwaggo sai magana take masa amma yaki yayi shuru, zaune na mike na dauki hula ta nasa kallonsa nayi da mamaki a tare dani nace."Lafiya kake min hayaniya da masifa a kaina bacci fa nake yi.''

Cikin hayaniyar yace."Ni ina ruwana da baccin ki ina dai fad'a miki cewa ki kama kanki a gidan nan domin ba zan lamunci ki dinga cin mutuncin mahaifiyata ba saboda kawai kina da daurin gindi gurin masu gidan idan abin yayi tsanani zan d'auketa na sauya mata gurin zama tunda zuwan ki gidan ya zama annoba."

Bakina ne ya mutu kawai na dinga kallonsa ina mamakin rashin kunyar da yake min har yaushe yayi girman da zai dinga buga min tsawa ko dan yaga Allah ya rufa masa asiri ya samu duniya.

Gwaggo tace."Khalid ka kyauta abinda kake wato ka shiga can gurin uwarka ta fada maka karya da gaskiya shine kazo zaka d'aga mana hankali ko to shikkenan mun gode ka fice min daga dakina."

Ba tare da ya bata hakuri ba ya buge rigarsa ya fita daga dakin, Gwaggo ta fashe da kuka da fadin."Sa'ida na rasa yanda zanyi da Rabi ta hanani sakat kullum babu kwanciyar hankali to idan Allah ya kaimu gobe zan tafi k'yauye naje na huta da wannan jarabar."

"Gwaggo idan kina so ki zauna lafiya a gidan nan to ki fita daga hurumin Ummatu babu ruwanki da duk abinda za tayi ki zuba mata ido duniya ce tafi bagaruwa jima kullum sai na fada miki hakan amma kin kasa fahimta gashinan ai Yaron da kika k'wallafa ranki a kansa ya shigo yaci miki mutunci saboda ita.''

Hawaye ta share tace." Ki kyale ni dashi ai zan nuna masa fushina zai san wanda yake wa tsawa Allah ya kaimu da safe zamu tafi can k'yauye mu bar musu gidan.

Nace."Eh hakan ma hukunci ne amma ki nemi shawarar Kawu kafin muyi tafiyar.'' Tace."To shikkenan haka za'ayi ki koma ki kwanta ki cigaba da baccin ki."

Saukowa nayi daga gadon na dauki buta na fita domin kama ruwa.

Ina fitowa daga bandakin naji muryar Kawu na tashi sama-sama da alama fada yake mata can naji muryarta tana kuka tana bashi hakuri kafin naji maganar Khalid din yana cewa"Baba don Allah maganar nan ta mutu haka wallahi bana son abinda zai daga muku hankali kuma ni ban fifita Uwata akan Gwaggo ba kowa da matsayinsa a zuciyata sannan Aunty Sa'ida 'yar uwata ce amma bana son irin abinda takeyi a gidan nan mutukar tana nan to Gwaggo da Ummatu sun dinga samun sa'bani kenan shiyasa kawai na yanke shawarar siya mata gida domin a samu zaman lafiya."

Kawu Iro yace."Ban amince da wannan tsarin ba Rabi zata cigaba da zama da Mahaifiyata a cikin gidan nan Sa'ida kuma dole ta zauna a gidan domin bata da inda ya wuce nan din.

Yace."To shikkenan Baba insha Allahu cikin satin nan za a fara aikin gidan idan yaso ita Gwaggon sai a fitar mata da sabuwar kofa ta waje ina ganin kamar hakan shine maslaha.''
Yace."Duk yanda za kayi kayi amma ban amince Rabi taje wani gurin ta zauna ba."

Girgiza kaina nayi na bar gurin ina addua akan Allah yasa hakan shi yafi alkairi watakila idan aka raba musu gidan za'a samu zaman lafiya.

Washe gari da Kawu ya shigo Gwaggo take fada masa cewa zamuje can 'kauye mu kwana biyu.'' Sai ya nuna farin cikinsa sosai harda bada sautun gaisuwa ga abokanan arziki." Sallama yayi mana ya tafi kasuwa.

Khalid yana can yana bacci hayaniyar matasa ta cika kofar gidan wai jiransa suke ya fito su gaisa dashi yayi musu hasafin da ya saba Khalid be watsar da abokanansa ba cikinsu yake zama suyi hira da labarin wassanin k'wallon kafa.

Salim ne ya shigo cikin gidan ya tsaya a bakin kofar dakin Gwaggo suna gaisawa d'an leko da kansa yayi yace."Kamar aunty Sa'ida ko." Gwaggo tace."Eh itace gatanan yau kimanin sati biyar da mutuwar auranta.'' Ji nayi tamkar na kwad'a mata mari saboda takaici wani lokacin idan ta aikata wani abun sai kaji tamkar zuciyarka ta buga.

Yace."Ayya! sannu auntynmu Allah yasa haka shi yafi alkairi Allah kuma ya zaba miki miji nagari." a zuciyata na amsa Yace."Gwaggo Khalid yana nan ko? domin naga motarshi a waje."
Tace."Eh yana nan ka shiga ka duba watakila ko bacci yake dan ban ji motsinsa ba."

Yace."To shikkenan bari na shiga na duba shi." Salim ne ya tashe shi daga baccin da yake Ya kalleshi da fadin."Salim wato ba zaku barni na huta ba ko."?

Yace."Khalid zaka huta idan lokaci yayi yanzu dai dole kayi hakuri tunda ka tara jama'a gasu Rossy Rabs can a waje suna jiran ka da alama ka manta alkawarin da kayi musu nayin wasa tare dasu."

Yace."Wallahi na manta gabad'aya jiya ban kwanta da wuri ba shine dalili bari nayi wanka na karya sai mu fita.'' Salim yace."Okey to bari na fita na fada musu cewa su jiraka ga kanan fitowa."

Yace."Okey nagode abokina." Tare suka fito Salim ya fita shi kuma ya nufi dakin Gwaggo da brush a hannunsa.

Sallama yayi tare da daga labulan dakin Ganinta zaune a bakin gado da rigar bacci a jikinta yasa da sauri ya kauda kansa, Gwaggo kuwa kauda kanta tayi tana 'bata fuska nice na amsa masa sallamar ciki-ciki.

Yace."Gwaggo kun tashi lafiya."? shuru tayi masa yayi jim! yana dan tunani murmushi yayi da ya tuna akan abinda yasa ta juya masa 'keya shi ya manta ma da sun samu sa'bani jiya......."Gwaggo ku bani man goge baki mana."
Da sauri tace."Bani dashi ni bana san ro'ko a rayuwata duk kudi'n ka amma kazo kana ro'kon abu kaje kayi asuwaki mana."

Yace." Sai na fita an jima zan shiga sahad na siya ina da asuwaki ko nayi ina had'awa da brush kawai idan zaki bani ki bani."

Tace."Ni bani dashi sai dai ko Sa'ida." Nace."Nima bani dashi." kallona yayi na minti biyu kafin ya saki labulan dakin ya bar gurin.

Gurin mahaifiyarsa ya samu man goge bakin Ummatu da kanta ta had'a masa ruwan wankan ta kai masa har bandaki sai lalla'bashi takeyi shi kam godiya yake mata yana jin dadin irin kulawar da take masa Gwaggo da Sa'ida na d'aki suna jin duk abinda yake faruwa a tsakaninsu......Gwaggo kishi ya cika mata zuciya sai surutai takeyi nace."Gwaggo don Allah kiyi hakuri ki kai zuciyarki nesa babu ruwanki da duk abinda yake tsakaninta da d'anta Ita uwarsa ce ke kuma kakarsa kowa da akwai matsayinsa." 'Kwafa tayi ta girgiza kanta ba tare da ta sake magana ba ta dauki redio ta kama tashar redio *kano Am* ta ware vollom aikuwa wakar *Aminu Ala* mai taken *Share hawaye uwa ma bada mama share hawaye ki daina kuka Ummi Ummina* ta karad'e gidan da sauri ta sanja tasha ta mayar da ita *Freedom redio* lokacin su kuma sun saka wakar *Zumunci yana kara kusanci* Murmushi tayi ta k'aro murya sosai ta ajiye redion. Na dinga kallonta ina mamakin al'amarinta Gwaggo duk da ta tsufa bata da kyau! irinsu ne suke hana kishiyoyi zama da habaice-habaice babu boka babu malam za'a kori kishiya.

A shirye ya fito da shirin fita sai kawai ya ganta a tsaye a bakin kofar dakin nashi.

Cikin kulawa yace."Umma ina fatan lafiya dai." Tace."Khalid inaso nayi magana da kai." Yace."To ina sauraranki." Tace."Khalid tunda dai Allah yayi maka yanda kake so a duniya kafi karfin komai na rayuwa a yanzu me ya kamata kayi.''?

Shuru yayi yana kallonta ta cigaba da cewa "Tunda ka dawo gida ban ta'ba ji kayi maganar Jamila ba alhalin kasan da akwai alkawarin aure a tsakaninka da ita kada ka watsa min kasa a ido kasa ma'kiya suyi min dariya Khalid."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."Umma bana so kina sa damuwa a ranki idan maganar auran Jamila ne babu damuwa dama ai tuntuni na amince da auranta sai a fara shirye shirye nan da wata uku sai a daura aure insha Allah."

Farin ciki kamar ya kasheta tace."Amma naji dadin wannan al'amarin Khalid Allah yayi maka albarka ya kara d'aukaka darajarka."

Ya amsa da ameeen Umma nagode da addua kwarai." Tace." Naga kayi shirin fita baka karya ba bana so kana zama da yunwa."

Goshinsa ya murza yace."Umma bana sha'awar shan tea kwana biyu kunu nake so wallahi shiyasa ban nemi wani abu a gurin ki ba." Tace."Ayya ai daka fad'a min tunda da akwai gasara sai na dama maka kunun." Yace."Kin san jiya dani dake duka bamu da nutsuwa shiyasa."

Tace."Eh hakane to ko zaka zauna na dama maka kunun." Girgiza kansa yayi yana duba tsadaddan agogon dake daure a hannunsa Yace."Tun dazu mutane ke jira na a waje zan fita na saurari uzirinsu." Tace."To shikkenan me kake bukata na girka maka."?

Yace."Umma duk abinda kika girka min zanci." Tace."To ina maka fatan alkairi yaro na Allah ya baka nasara a rayuwarka." Ya amsa da ameeen ya Allah." Yana fita tayi murmushi tare da girgiza kai tace."Cikin ruwan sanyi zan k'wace yaro na daga hannun ma'kiya na dakinta ta shiga ta dauki wayarta tana so tayiwa Jamila albishir da cewa auranta da Khalid ya kusa zuwa.

Kasa fita yayi sai da ya leqa dakin Gwaggon kamshin turaransa ya cika mana hanci satar kallonsa na dinga yi ta 'kasan idona yayi kyau har ya gaji yana sanye da k'ananun kaya kanshi sanye da f-cap sajensa ya kwanta a fuskarsa ba'ki sosai sai kyalli yake.........Ganinsu suna cin d'umame na towo da jug din kunu da kosai a gabansu yasa ya cire Booth din dake kafarsa ya shiga dakin ya zauna kusa dani lokaci k'ankani na rikice feelings mai zafi ya taso min gabad'aya k'amshin dake tashi a jikinsa ya gigita ni."
Chapter 73 · 0% Book details