← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 90

Sashe 13

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse nayi sallama cikin dakin nasa......Ya amsa min tare da kiran sunana." Na karasa cikin dakin sosai ina amsawa har 'kasa na tsuguna na gaishe shi. Ya amsa cikin sakin fuska da kulawa ya d'ora da fad'in "Sa'ida jiya mahaifiyarki duk tayi min bayanin abinda ke faruwa da rayuwarki naji rashin dad'i sosai kuma raina ya 'baci dalilin da yasa ma kenan na yanke hukuncin kan cewa ko zaki koma can gidan to ba yanzu ba sai kin samu nutsuwa saboda haka ina so ki kwantar da hankalinki ki cire duk wata damuwa dake ranki insha Allahu Allah zai kawo miki miji nagari ki aure."

Cikin rauni gami da tausayin kaina nace"Nagode Alhaji insha Allahu kuma zan cire al'amarin daga cikin raina."

Yace."To Alhamdulillahi ya aikin ki ina fatan komai lafiya."? nace."Alhamdulillahi komai lafiya Alhaji."' Yace."To masha Allah Allah ya taimaka." Na amsa da ameeen tare da kokarin mikewa yace."Kyace ina kiran mahaifiyar taki." Nace."Tom zan fada mata yanzu.

Ina fita na nufi kicin din na sheda mata kiran da yake mata, cikin sakin fuska muka gaisa da mai aikinsu Asabe har tana tambayata yaushe nazo. nace "Shigowar dare nayi shiyasa ba kowane yasan da zuwana ba."

Sai bayan mun kammala aikin ne na samu nutsuwar shiga d'akunan abokan zaman nata muka gaisa dasu cikin mutunci da girmamawa Famliy d'in Alhaji Shamsu suna da kirki sosai Mussaman Babban d'ansa Mai suna Aminu mun saba dashi sosai yana da kirki da saukin kai kud'in sa sam bai rufe masa ido ba babbar matsalar Yaya Aminu rashin aure anyi anyi dashi yayi aure ya'ki ga uban kudi da yake samu dan kasuwa ta nayi dashi sosai yake fita 'kasashe ya shigo da kaya amma duk kudinsa da tsayin shekarunsa bashi da mace... mahaifiyarsa har magunguna take 'karbo masa cikin dubara take bashi a ganinta ko bashi da lafiya shiyasa baya sha'awar auran shi kuwa ba tare da yasan maganin menene ba zai kar'ba yasha tunda yasan mahaifiyarsa ce ba zata cutar dashi ba.

To Alhaji Shamsu na fita da kamar minti ashirin su Khalid suka isa gidan.....su gaisa da maigadi cikin mutunci Baba Iro yace "Munzo gurin maigidan ne." Maigadi yace."Ayya wallahi kun doki gurbi Alhajin bai jima da fita ba sai dai idan kasuwa zaku bishi."

Gabad'ayansu jikinsu yayi sanyi....Baba Iro yace."Babu damuwa insha Allahu zamu dawo da daddare ko kuma gobe da safe idan yaso idan ya dawo sai ka sheda masa zuwanmu."

Maigadi yace."To shikkenan babu damuwa wane suna za'a fad'a masa."? Yace."Kace masa Ibrahim ne Kawun Sa'ida daga Mandawari."

Yace."To shikkenan za'a fada masa insha Allah."

Sallama sukayi da juna Maigadin ya rufe gate din....Khalid a sanyaye yace."Baba mai zai hana mu bishi kasuwar.''? Baba Iro ya girgiza kansa da Fad'in "Khalid al'amarin yana bukatar sirri bai kamata mu bishi gurin sana'arsa ba tunda dai maigadinsa yasan da zuwanmu nasan idan ya dawo zai fada masa."

Jiki a mace yace."Hakane." Adaidaita sahu suka shiga Baba iro yace."Ni Kasuwa zan wuce yanzu yana da kyau kazo muje ." Jim! yayi yana nazari kafin yace."Baba kasan gobe zan koma skull so inaso na koma gida nayi shirye-shirye." Yace."To shikkenan Khalid idan ka koma gida ka taushi zuciyar Gwaggo nasan dai yau akwai rigima a gidan amma kai tunda taku tazo da d'aya ka rarrasheta kafin na dawo."

Yace."To shikkenan Baba." Direban yace." Ina zan kaiku ne naga kamar tafiyar taku ta bambamta." Khalid yace." Kasuwar sabon gari zaka kaishi ni kuma Mandawari." Direban yace."Ai hanyar ta baud'e ni yanzu kai tsaye Sabon gari na nufa."

Yace."Okey to sauke ni na samu wata." ya tsayar da babur din ya fito hannu yasa a aljihu ya dauko kudi ya mik'a masa......Baba Iro yace."Kana da kudi wadatacce a jikinka ne."?

Yace."Eh baba kada ka damu Kuje kawai Allah ya kiyaye." Direban yayi saurin sa kudin cikin d'an bankin dake gaban babur din yaja da sauri suka bar gurin.

Ajiyar zuciya ya sauke bayan barin su a gurin ya tari wani babur din gidan Alhaji Shamsun zai koma.

Maigadi ya bude karamar kofa yana tambayar waye ganin Khalid yasa yace ''Ka dawo kenan."? Khalid yace."Inaso zanyi magana ne da Auntyna Sa'ida."

Jim! yayi kafin yace."Khalid kayi hakuri da abinda zan fada maka Alhaji ya hana kowane namiji shiga cikin gidansa ko masu yi musu hidima iyakar su bakin gate saboda haka nake baka shawarar kiranta a waya ita sai ta fito ku gaisa."

Yace."Okey to bude min na zauna a gurin zamanka sai na kira wayar tata." Maigadin ya bude masa ya shiga ya zauna kan kujerarsa shi kuma ya mayar da gate din ya rufe...

*Masoya a taimaka da Sharing🥰👏🏼*

*IDAN KINA BUKATAR BIYAN KUDIN LITTAFIN GA YANDA ABIN YAKE......VIP GRUOP#600....NORMAL GRUOP#300.....ACCOUNT.....0542382124.....BINTA UMAR GTBANK.....IDAN KATI ZAKI TURO...#400 NE SAI KIYI MIN MAGANA TA WHASAP DA WANNAN NUMBER*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
[3/6, 2:04 PM] Umm Muhammad: *GA IRINTA NAN!!!🙆🏼‍♀️*
_(LOVE STORY🌺)_
*NA*
_BINTU UMAR ABBALE🍒_
*MANAZARTA WRITES ASSO🖊️📚*

*12*
Cikin ikon Allah ina tsayuwa a bakin titin wani adaidaita sahu ya tsaya a gabana. "Hajiya ina zakije."? Ya fad'a yana dan le'ko da kansa. Da sauri nace."Hotoro zaka kai ni." Jim yayi kafin yace."Okey to nawa zaki biya."? 'Kugin da naji a bayana yasa nai saurin juyawa Khalid ne da Salim cikin a daidaita sahu suna kokarin shiga layin....Da sauri na dauki jakata na fad'a babur da fad'in "Muje ko nawa ne zan baka." babur din ya buga da sauri muka bar gurin....Sai da naga munyi nisa sosai hankalina ya kwanta a nutse na fito da wayata daga cikin jaka number ta na shiga nema inaso na sanar da ita cewa gani nan a kan hanya.

A tsanake muka gaisa nace."Umma gani nan a kan hanyar zuwa." Tace."Da daddare nan Sa'ida ina fata dai lafiya."? Cikin rauni nace."Lafiya Umma." Ta amsa da to "Alhamdulillahi sai kin 'karaso." Kashe wayar nayi nasa a jaka kana nayi saurin sa gefan hijabina na goge hawayen da ya fara zuba a fuskata.

Cikin magagin bacci ta tashi tana lalu'ben torchlight d'inta ta kunna tana haske d'akin da fad'in "Sa'ida Ibrahim din be shigo bane."? Shurun da taji yasa tayi saurin kallon inda take kwanciya taga wayam! sai tai zargin ko tana bandaki redion ta ta dauka ta fara kokarin kunnawa wasu tashoshin sun rufe da kyar ta lalubi freedom redio lokacin suma daf suke da rufewa. kimanin minti goma tana zaune ba taji motsinta ba sai ta mike ta fito bakin band'akin ta tsaya tana kiran sunanta. shurun da taji yasa gabanta fad'uwa tana kokarin barin gurin ya shigo gidan ganinta a tsaye a bakin bandaki yasa yace." Gwaggo lafiya me kike anan gurin."?

Murya na rawa tace."Khalid Sa'ida bata gidan nan.'' gabansa ya fad'i da sauri yace."Gwaggo bangane bata gidan nan ba." ? Ajiyar zuciya ta sauke tana kokarin barin gurin tace."Jeka kira min babanka idan ma yayi bacci ka taso shi.''

Khalid da sauri ya nufi gurin nasu itama ta nufi dakinta tana haske haske da torchlight nan taga babu jakar kayanta sai ta sake karaya a sanyaye ta zauna kan shimfid'arta tana fad'in "Wannan yarinya bata da hankali ashe."

Baba Iro da Khalid suka shiga dakin a tare......Tace."Ibrahim matarka ta tunzura Sa'ida ta had'a kayanta ta gudu."

Kawu Iro yace."Gwaggo wace irin magana ce wannan."? Fashewa tayi da kuka tace."Iro d'azu Rabi ta zauna ta 'karewa Sa'ida cin mutunci tana kiranta da Karuwa tsohuwar guzuma saboda kawai ina maganar auransu da Khalid shine fa ta fito tayi mata wannan cin mutuncin a cewarta wai d'anta ba zai auri lalatacciya ba wannan dalilin ya fusata zuciyarta ta had'a kayanta ta gudu."

Baba Iro yayi shuru yana jimanta al'amarin! tace."Yanzu ni babban tashin hankalina da damuwa ta inda ta nufa a cikin daran nan."

Yace."Gwaggo hakika raina ya 'baci da wannan al'amarin kuma duk irin hukuncin dana dauka akan Rabi kada kice don me ta riga ta gama fusata ni ace wai 'yar d'an uwana na jini take kira da Karuwa."

Gwaggo tace."Ibrahim ba zan hana ka ka dauki mataki akan Rabi ba domin ko baka dauka ba ni zan dauka ba zata dinga la'antar zuria ta ba."

Yana kokarin fita daga d'akin Khalid ya dafa kafad'arsa a tausashe yace."Baba kada ka yanke hukunci cikin fushi Annabi ya hana."

Rai a 'bace! yace."Saboda mahaifiyarka ce ko? yanzu kai a tunaninka abinda ta aikata tayi daidai."?

Kansa ya girgiza a sanyaye yace."Nima banji dadin al'amarin ba amma dan Allah kayi hakuri." Ba tare da yace masa komai ba ya bar gurun.

Khalid dakin ya shiga jikinsa duk a mace babu shakka yasan wannan hargitsin dake faruwa shine sila da baya shiga sabgar auntyn nasa da mahaifiyartasa ba zata samu hanyar zaginta ba.

Number ya nemo a wayarsa ya fara kira, Gwaggo tace."Yawwa dama yanzu zance ka kira ta a waya mu ta fad'a mana inda ta nufa duk da dai nasan watakila tana can gurin uwarta mai hure mata kunne."

Jin wayar tana shiga yasa da sauri ya d'aga mata hannu. shuru tayi tana kallonsa, wayar ta 'karaci ringing ta katse bata dauka ba.

Hannu na rawa ya sake kira nan ma babu amsa Khalid ya dinga kiran wayar tana katsewa ya kai sai goma, jiki a sanyaye ya kalleta da fad'in "Gwaggo aunty Sa'ida tayi zuciya taki daukar wayar."

A sanyaye tace."Khalid dole tayi fushi! bayan fitarka Uwarka sata tayi a gaba taci mutuncinta ta dinga zaginta tana kiranta karuwa." Tana share hawaye take maganar ta cigaba da cewa"Wai yau zuria ta Rabi takewa wannan cin mutuncin."

Yace."Gwaggo idan Ummatu tana da laifi kema kina dashi kada fa ki manta irin takura mata da kikeyi Gwaggo keda Ummatu kune kuka kori auntyna Sa'ida daga gidan nan."

Shuru tayi tana share hawaye tace."Dan Allah sake kiran wayar ko zata dauka idan kuma bata daga ba ka kira wayar uwartata idan kana da number ta."

Yace."Ni bani da Number Ummah Habiba amma bari na sake kira naji ko zata dauka...sake kiran wayar yayi har sau biyu babu amsa, ya sauke nannauyan ajiyar zuciya yana tunanin yanda za'ayi......."Khalid ka fito kaje gidansu abokinka ka kar'bo mukkulin adaidaita sahunsa ka kai ni babban gida.'' Muryar mahaifiyarsa ta katse masa tunani.
Chapter 13 · 0% Book details