Sashe 66
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kansa ya dafe yana cijar lips d'inshi. jikinsa na matsa na dora hannuna a cinyarsa da sauri ya ture ni yana hararata yace."Kada ki janyo wa kanki 'bacin rai Sa'ida ni ba zan iya aikata miki komai ba a yanzu ki rabu dani nayi bacci."
Raina ne ya soma 'baci nace."Haba Yaya Aminu ya kake wannan maganar kamar ba namiji ba kayi min dabaru dan Allah na samu satisfaction ko yaya ne."
"Sa'ida idan nayi miki dabaru kin samu gamsuwa ni kuma fa? zaki barni cikin halin damuwa kiyi hakuri nima ina bukatar naji dadi amma babu hali shiyasa gabadaya na ajiye maganar aure a gabana saboda lalura ta ina ganin zan iya kare rayuwata a haka saboda haka ki cigaba da hakuri insha Allahu komai yana da karshe."
Yana gama maganarsa ya mike ya shiga toilet ya barni da baki a sake ina binsa da kallo.
Ya jima a ciki kafin ya fito ya kalle ni da fadin."Ashe baki je kin kwanta ba kina zaune."? Ba tare da nace masa komai ba na sauko daga gadon na kama hanya na fita daga dakin zuciyata tamkar zata fashe sabida tsabar takaici da bakin ciki.
Ruf da ciki nayi kan gado na dinga rizgar kuka ina rokon Allah ya kawo min dauki!! jaraba sai k'ara nunnukuwa takeyi al'amarin da ya gigita ni mutuka ba tare da nayi tunanin abinda ka iya zuwa ya dawo ba na dauki waya ta na kunna number Khalid na lalabo na shiga gurin kira.............Muryar wani naji ta doki kunnena da sauri na cire wayar ina dubawa tabbas number sa ce to ya akayi wayarsa taje hannun wani.
"Da wa nake magana ne."? Mutumin yayi magana. a sanyaye nace." Sunana Sa'ida daga kano inaso nayi magana da Khalid.
Yace."Eh naga sunanki akan wayar sai dai kiyi hakuri fa Domin Khalid baya kasar nan sun tafi wasa kasar america."
Jiki a mace nace."Dan Allah babu yanda za'ayi ka bani number da yake amfani da ita a can din.........Yace."Zan iya baki mana sai dai ko na baki number be zama lallai ki samu amsa akan lokaci ba saboda kullum yana busy. " Nace."Babu matsala ka bani number."
Yace."Okey bari na miki text. " ajiyar zuciya na sauke da fadin."Nagode sosai. wayar na kashe ina dan jin sauki a cikin zuciyata.
Number ya tura min nayi sauri nayi serving agogo na duba karfe goma sha biyu da minti arba'in inaso na kira shi amma kuma ban san me zan ce dashi ba.
Gwada kiran wayar nayi cikin ikon Allah ta shiga sai dai har ta karaci ringing ta katse bai dauka ba, text na tura masa na sheda masa cewa nice nake kira ya dauka.
Lokacin suna dakin hutu shida abokansa domun basu jima da fitowa daga filin wasa ba, koda ya duba text din sai kawai ya share yaki kiran ta akan wane dalili zata kirasa da daddare ta tayar masa da hankali ta hanashi gudanar da abinda ke gabansa wayar ya ajiye kan drowar ya shiga toilet daidai lokacin dana sake kiran wayar tayi ta ringing babu wanda ya daga a cikin jama'ar dake dakin kowa harkar gabansa yake.....sai bayan ya fito daga toilet din yana tsane jikinsa da towel Salmanu yace."Khalid an kira wayarka kana wanka kuma da alama daga gida Najeria ne."
Yace."Salmanu rabu da ita don Allah aunty Sa'ida ce me za tayi min da daddare salon ta jaza min masifa ta kuma hanani gabadatar da uzurina."
Salmanu yace."Amma nayi mamaki fa to me zata ce maka bayan tana gidan auranta." Yace."Nima abinda na gani kenan."
Salmanu yayi jim yana nazari yace."Baka kuma tunanin ko wata matsalar ce ta faru a gida ka kira ta kaji ko menene."? Girgiza kansa yayi yace."Aa ba zan kira ta ba Salmanu idan wata matsalar ce Babana zai kira ni ya fad'a min tunda yana da number ta." Salmanu yace."To shikkenan Allah yasa alkairi ne." Yana kokari sanya short nickar a jikinsa ya amsa da "Ameeen Ya Allah."
Jikina a mace na ajiye wayar na kwanta rigingine idona na kallon rufin dakin hawaye kawai yake zuba a fuskata duk yanda naso da na samu bacci a daran abin ya gagara yanda naga rana haka naga dare na tashi da wata irin kasala da mutuwar jiki! da kyar na shirya break fast na samu nayi wanka na kimtsa jikina na fito falo na zauna ina jiran fitowarsa.
A shirye ya fito da shirin fita kamar yanda ya saba babu yabo babu fallasa muka gaisa da juna na mike na nufi gurin cin abincin ya biyo bayana.
Haka mukayi zaman kurame a gurin babu wanda yayi magana da dan uwansa tun bayan gaisuwar data shiga tsakanin mu.
Kallonsa nayi yana goge bakinsa da tissue nace."Yaya Aminu ina so ka ajiye ni a hotoro mu gaisa da mutan gida."
Jim yayi na minti biyu kafin yace."Ina fatan a kimtse kike."? nace."Eh mayafi na kawai zan dauko." ya mike da fadin."Okey to kiyi sauri ki fito ki same ni a bakin mota."
Da sauri na mike da fadin."To shikkenan." hanyar fita ya kama ni kuma da sauri na shiga dakina domin dauko mayafi na.
Ko a motar ma haka mukayi zaman kurame sai jefi-jefi muke magana da juna waya kuwa ban san iya adadin nawa ya amsa ba duk wayoyinsa a lokaci guda sai a kira sai ya gama da wannan sai ya dauki wannan.
A tsaitsaye ya shiga gidan suka gaisa da mutanan gidan ya wuce ya tafi kasuwa, ni kuwa ko wane daki sai da nabi daya bayan daya muka gaisa sai dai na jima a dakin mahaifiyarsa muna hira sama-sama kafin na fito.
Ummu Habiba ta kalle ni da fadin."Ina fatan dai kuna zaune lafiya babu wata matsala." ?
Shuru nayi ina wasa sa hannuwana. tace."Sa'ida idan da akwai matsala ki fada min baki da wacce ta kaini a duniya.
A raunane nace."Hakane Umma sanin hakan ne ma yasa nazo gurin ki domin na sheda miki abinda yake faruwa."
Zama ta gyara tana kallona a nutse tace."To ina sauraranki." Na jima kaina a sunkuye kafin nace."Ummu ashe Yaya Aminu bashi da lafiya."?
Tace."Bangane ba idan Aminu bashi da lafiya ai zaki fi kowa sani ya za'ayi kuma ni da nake gefe guda ki tambaye ni."
Ajiyar zuciya na sauke nace."Ummu ki fahimci maganata mana Yaya Aminu a zahiri lafiyayye ne amma a bad'ini nakasashshe ne."!
Ta dinga kallona tana neman karin baya ni. Murya na rawa nace."Ummu ranar wanka ba'a boyan cibi kamar yanda kika fada hakane bani da wanda zan kaiwa matsalata ya saurare ni sai ke da kika haife ni To inaso na sanar miki da cewa tsayin watannin aurena da Yaya Aminu wata mu'amular aure bata ta'ba shiga tsakani na dashi ba gabadaya bashi da kuzari bashi da girma irin na maza haka nake zaman hakuri har aka kawo wannan lokacin da na kasa hakuri nazo na sheda muku koda taimakon da zakuyi a matsayin ku na iyayenmu tunda nima nayi iyakacin bakin kokari na akan matsalar."
Ido ta tsira min tana girgiza kanta daka ganin yanayin ta al'amarin ya bata mamaki! "Sa'ida yanzu tsayin wata hudu da kwanakin auranku babu wata mu'amula ashe."?
Kaina na daga mata hawaye na kokarin kwace min." Tace."Amma al'amarin ya bani mamaki mutuka kuma babu kama ko kad'an to shin me yake damun wannan yaron haka."?
Nace."Wallahi nima ban sani ba gashi baya son shan magani dan har zuwa nayi gidan Gwaggo Uwale taje can kauyen daburau ta samo masa magani amma sau uku kacal yasha yace a zubar dashi ba zai kara amfani dashi ba."
Ummu Habiba tace."Ai to hakan ba zata yiwu ba dole ya nemi magani domun rayuwa ba zata ta'ba tafiya a hakaba wace macace zata zauna dashi a haka babu shakka dole yau mahaifinsa yasan halin da ake ciki domin yasan matakin da zai dauka.
Nace."Ummu ni wallahi da Ya bani hadin kai a gida babu wanda zaiji ko ya gani tunda dai wannan maganar ta sirri ce be kamata a fad'a ba amma duk kokari na akan hakan be samu ba gabadaya ma yanda na fahimce shi matsalar bata damunsa."
Ummu tayi shuru tana nazari kafin tace."Ko shiyasa ya'ki aure ne saboda yasan bashi da lafiya." Nace."To ina jin dai hakane manufarsa." tace."To ai shikkenan Allah yayi mana magani kuma naji dadi da baki rufe maganar ba kika fito kika fad'a domin a san matakin dauka saboda haka kada ki damu insha yau idan Alhaji ya dawo zan isar masa da maganar." Ajiyar zuciya na sauke da fadi."To shikkenan Umma Allah yayi mana magani." ta amsa da "Ameeen Ya Allah."
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*84&85*
Koda Alhaji Shamsu ya samu labarin abinda yake faruwa sai ya rasa bakin magana yayi shuru yana mamakin al'amarin da kyar ya iya d'aga kansa ya kalli inda nake zaune kaina a kasa yace."Sa'ida ina neman gafara a gurinki a bisa wannan al'amari da ya faru wallahi dana san yaron nan yana da matsala da ban tilasta ki auransa ba ni duk abinda yake faruwa ban sani ba bani da labari shi bai fada min ba kuma mahaifiyarsa ma haka saboda haka kiyi hakuri da wannan al'amari nasan anyi miki laifi amma mutukar al'amarin nan ya zama da akwai cutuwa a ciki to zan sanya Aminu ya sawwake miki sai kiyi auran da hankalin ki zai kwanta."
Umma Habiba ta sauke ajiyar zuciya a sanyaye tace."A'a Alhaji ba za'ayi gaggawar yanke hukuncin rabuwa ba kamata yayi shi Aminun ya nemi magani domin a duniya babu cutar da bata da magani amma kada kace zaka raba auran."
Yace."Habiba yaron nan ya bani mamaki mutuka wato ashe yasan yana da dauke da lalura irin wannan amma bai ta'ba zama tare dani munyi maganar ba to Habiba ta yaya za'ayi rayuwar aure babu wannan mu'amular akwai cutuwa a ciki dole a raba auran.
Murya na rawa nace."Aa Alhaji ka dai kira shi kayi masa magana ya mayar da hankalinsa gurin neman lafiyarsa nima bana so a kashe min aurena ina tausaya masa halin da yake ciki.