Sashe 59
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da kaina na hada masa ruwan wanka yana ta sa min albarka na fito masa da jallabiya da gajeran wando na ajiye kusa dani.....Daure da towel ya fito sai yayi saurin dauke kansa a maimakon ni naji kunyar ganinsa a haka sai ya kasance shi yake jin kunyata, dan sai naga kamar a tsarge yake tsayawa yayi bakin kofar toilet din da fadin."Bani kayan nan." Da sauri na mike da kayan a hannuna na kai masa, kawai sai naga ya koma toilet din ya banko kofar. sakato nayi da baki ina mamaki!
Ina nan tsaye ya fito ya wuce ni ba tare da ya tanka ba, a sabule nabi bayansa falon sai na sameshi zaune a kasan kafet yana duba loptop. zama nayi a hankali nace."Ba zaka ci abinci ba."?
Hankalinsa nakan Loptp din yace."Bari na rage aiki tukkun." shuru nai kawai na zuba masa ido ina mamakin al'amarinsa.
Kusan rabin awa yana aiki a loptop din kafin ya rufe a nutse ya kalle ni da fad'in "Tashi muje dainng din ki bani abincin." Mikewa nayi ya biyo bayana.
Tsaf na shirya masa abincin na tura masa gabansa zama nayi ina kallonsa yana cin abincin yana amsa waya
Nace."Yaya Aminu kayi abu d'aya mana ka ajiye wayar kaci abinci sai hakan yafi.''
Ba tare da ya kalle ni ba ya cigaba da wayarsa.....Ji nayi raina ya 'baci sai kawai na miqe na bar masa gurin.
Koda ya kammala cin abincinsa zuwa yayi ya dauki loptop dinsa bece min uffan ba ya bude dakinsa ya shige! ni dai mamaki ne ya kusa kasheni a gurin da kyar na iya kai kaina daki na kwanta.
Haka rayuwar mu ta cigaba da tafiya tsayin wata guda da dawowarsa babu wata mu'amula ta aure data ta'ba shiga tsakanina dashi Kullum a dakinsa yake kwana a garkame! gabadaya ma ya daina yarda na ra'bi inda yake dan duk kokarin da nake masa idan ya dawo daga kasuwa sai ya dakatar dani yace naje na huta shima Allah ya bashi lafiya zai iya had'a ruwan wankansa.
Ganin wulakancin yayi yawa yasa na daina shiga dakinsa sai dai idan ya fito mu gaisa ya kama hanya ya fita.......Gashi kamar mara tunani kullum sai ya tura min kudi accont d'ina al'amarin dai sai kace hauka! kuka naci na koshi na yanke shawarar tun kararsa da magana domin dai ni na gaji ba auran kudi nayi ba halastaccan aure nayi irin wanda Allah yake so......Sai da ya fito falon sannan nima na fito daga dakina na sameshi a zaune yana abinda ya saba lissafi da amsa kiran waya cikin zuciyata nace."Ban ta'ba ganin sahoramin namiji irinka ba. Wayar hannunsa ya kashe ya kalle ni da fadin."Kina da wata bukata ne."? a nutse nace."Eh ina da ita." Ya zuba min ido da fadin."Ina sauraranki." Murya na rawa nace."Yaya Aminu wai me kake nufi ne."? Cikin wani irin kallo yace."Bangane ba."? Na d'aure fuska tamau! nace."Shin dutse ka ajiye a gidan ka kome? ko kana da lalura ne."? Tsira min ido yayi yana kallona na sake cin kunu da fadin."Tsayi wata d'aya da sati biyu nake cikin gidan nan naci na koshi naci nama nasha madara nasha nono na kwanta a Ac me kake tsammanin zai faru." ? Dariya yasa yana kallona, sai kawai hawaye suka 'kwace min. Nace."Wato saboda kai baka da damuwa ka maisheni mahaukaciya kana min dariya ko to wallahi na gaji ni zan samu mahaifiyarka na fad'a mata halin da ake ciki." Da sauran dariyar a fuskarsa yace." Ai ba sabon abu bane a gurinta idan kin fada mata tuna mata kikayi domin tafi kowa sanin matsalata." Hannu nasa na share hawaye da fadin."To me yasa kasan kana da matsala ka amince da aurena."? Jim yayi kafin yace."Kawai bana so na bijirewa umarnin mahaifina ne." Cikin takaici nace."To kawai daga yau ka kira kanka da mace tunda ka fita daga sawun maza wato har wani fad'a kake kana da lalura to zaman me kake a haka da ba zaka nemi magani ba."? Rai a d'an 'bace yace."Ke Sa'ida kada ki fad'a min maganar banza mana." Nace."Ai gaskiya ce." Hannu ya daga min da fad'in "To tunda dai kin damu yau zan jarraba na gani." Naji wani kuttun bakin ciki ya tokare min a ma'koshi nace."Wallahi tallahi kudin ka na banza ne tunda har ka sake ka mayar da kanka haka meye amfanin neman kud'in naka kana fama da lalura irin wannan." Shuru yayi min, na dinga masa surutai ina farfad'ar masa maganar da duk tazo bakina.....A fusace! yace."Ki tashi ki bani guri idan ba haka ba wallahi ranki zai 'baci! Mi'kewa nayi na bar gurin raina a mugun 'bace.!
[3/29, 8:12 AM] +234 706 435 8270: *SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*74&75*
Koda na koma dakin kasa hakuri nayi raina a bace na dauki wayata number Hauwwa na nema kiranta zanyi na fada mata abinda yake damuna domin hausawa na cewa Abokin kuka shi ake fadawa mutuwa na yarda da Hauwwa mutuniyar kirki ce kuma na tabbatar da cewa ba zata fadawa kowa sirri na ba...... Cikin barkwanci tace."Amarya Amaryar Alhaji Aminu young millionaire ya kike ya amarcin.''?
'Karamin tsaki naja ciki ciki nace."Hauwwa ki daina kira na da amarya domin dai har yanzu ban amsa wannan sunan ba."
Cike da mamaki! tace."Kawata bangane ba.'' Ajiyar zuciya na sauke nace."Hauwwa akwai gagarimar matsala kizo don Allah.
A sanyaye tace."Sa'ida matsala wace iri kuma? mai kika rasa a wannan gidan da har kike kiran matsala.''
Nace."Hauwwa sai dai kinzo sai mu tattauna maganar domin a waya ba zaki gamsu ba.
A sanyaye tace."Tom shikkenan idan na taso zan shigo Allah yasa mu dace." Na amsa da ameeen ya Allah."
Motsin shigowarsa dakin naji sai nayi saurin rufe idona gabadaya bana son kallon fuskarsa dan wani irin mugun haushinsa nake ji.
Zama yayi a kusa dani yana kiran sunana, shuru nayi ban amsa ba.
Yace."Nasan idonki biyu ki tashi inaso nayi magana dake." Sai da na mula tukkuna na tashi ina kauda kaina.
Cikin taushin murya yace."Ki juyo ki kalle ni ki kuma fahimci maganata."
A hankali na juyo muka hada ido sai na hango alamun damuwa a fuskarsa.
"Sa'ida nasan na zalince ki dana amince da auranki bayan nasan bani da wani karfi irin na mazantaka bani da wani kwanjin da zan biya miki bukatarki ta aure saboda wannan dalilin. Sa'ida tunda na taso na girma na kai munzali ban ta'ba jin sha'awar wata 'ya mace ba ban san meye dalili ba mahaifiyata sosai al'amarin ya dameta duk inda taji labarin wani mai magani sai taje ta bada sadaka ta kar'bo min bana mata gardama zan kar'ba nayi amfani dashi amma duk da haka bata sanja zani ba har yanzu jiya i yau bana jin wani sauyi a tare dani kiyi hakuri insha Allahu zan je asibiti domin a duba lafiya.
Nace." Yaya Aminu mai yasa kasan kana da irin wannan matsalar ka kar'bi aurena.''? Girgiza kansa yayi yace."Na fada miki dalili na bana so na bijirewa umarnin mahaifina ne."
Ajiyar zuciya na sauke na koma na kwanta da fadin."Allah ya sawwa'ke maka." Ameeen yace tare da mikewa tsaye hanyar fita ya kama na bishi da kallo ina jin wani katon abu ya tokare min a kirji a gaskiya banga dalilin da zai sanya na cigaba da zama dashi da wannan lalurar ba dole ne na nemawa kaina mafita.
Kimanin minti ashirin da fitarsa ya sake shigowa a shirye da shirin fita ya kalle ni a nutse yace."Ni zan fita." Ba tare dana kalleshi ba nace."To Allah ya bada sa'a." Ya amsa da "ameeen ya Allah."
Ya juya ya fita daga dakin.
Sai yamma Hauwwa tazo gidan nace."Amma dai kin biya wani gurin ko."? Tace." Wallahi naje asibitin Yurolaji dubiya kwana biyu talakawa sai wuya suke sha suna fitsarin jini dalilin shan kayan lemo na leda da sukayi."
Cike da mamaki nace."Wane irin kayan lemo kuma."? Tace." Kayan lemo dai irin wanda kika sani Vevi mix Tiara d'an tsami da dai sauransu.
Nace."Ikon Allah wannan shekaran kuma annobar data afku kenan."? Tace."Wallahi kuwa ai al'amarin ma da sauki tunda an fahimta da wuri mutane duk sun tsorata suna kokarin kare kansu da lafiyarsu.
Jiki a mace nace."Talaka dai ya shiga uku wato ganin azimi yazo yasa aka shigo da wannan muguntar." Tace."Shine manufarsu dama jama'a suyi ta sha suna mutuwa.
Nace."To Insha Allahu sai Allah ya kare al'ummarsa duk mai nufin talaka da sharri zai koma kansa
Dariya tayi tace."Na lura al'amarin ya firgita ki Sa'ida." Nace."Sosai kuwa fitsarin jini fa." Tace."Wallahi kuwa sai ma kinga yanda suke shan wahala sai karin jini ake musu idan abun yazo da karar kwana har mutuwa ake.
Girgiza kaina kurrum nayi ina jajanta al'amarin.
Ta kalle ni a nutse tace."To Sa'ida gani nazo kuma ni banga wata damuwa a tare dake ba na dai ga kinyi kyau kinyi qiba da haske alamun kina cikin kwanciyar hankali."
Kallonta nayi nace."Hauwwa a jikina ina jin nayi rama sabida damuwa amma kice nayi qiba."
Murmushi tayi tace."Kin san Allah ni banga wata rama da kikayi ba.'"
Nace."Okey mybe dan kin kwana biyu baki gan ni ba ne." Tace."To zata iya kasancewa hakane.
Shuru dakin yayi na minti biyu na kalleta da fadin." Hauwwa kin san me."? ta girgiza kanta tana kallona. Nace."Yau tsayin wata guda da kwanaki a gidan aurena babu wata mu'amular aure data shiga tsakanina da Yaya Aminu.
"Bangane ba."? Tafada tana kallona da mamaki a tare da ita.
Murmushin takaici nayi nace." Abinda dai yake faruwa kenan Hauwwa Yaya Aminu yaki yarda mu had'a shimfida hannuna wannan bai ta'ba rikewa ba, dazu na sameshi da maganar sabida inaso ya fada min a wane matsayi nake a gidansa, Budar bakinsa sai cewa yayi shi yana da lalura wai tun da yake bai ta'ba sha'awar wata a mace ba amma wai zai nemi magani.
Hauwwa zuba min ido kawai tayi tana kallona. sai kawai naji zuciyata ta karye hawaye na kokarin kufce min.