← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 90

Sashe 29

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Salmanu yace."Legos zamu tattara mu tafi akwai wata 'kungiyar 'yan ball ta 'yan kano mai taken kano Pillas inaso muje mu fara gudanar da harkokinmu na ball a can Khalid ka iya buga 'kwallo jikina na bani kana da abinci a harkar.

'Karamin tsaki yaja yace."Wallahi na dauka zaka ce akawai company da yake bukatar irinmu a legos din wace irin ball kuma Salmanu mu fuskanci abinda yake gabanmu ina ganin tunda aikin ya'ki samuwa anan me zai hana mu tafi da takardun mu can mu gwada mu gani."

Salmanu yace."Eh dama haka za'ayi Khalid ai ba zamu dogara da abu guda ba idan aikin ya'ki samuwa ba sai mu mayar da hankalinmu gurin harkar k'wallo ba ko ya kaga ni."

Khalid yace."Salmanu nifa a halin yanzu aikin da zai ri'ke ni nake nema bana so nayi ta zama da girmana wani na dawainiya dani 'Kwallo tana kawo kudi amma sai mutum yana da hanya a harkar sannan duniya zata san dashi har ya samu wani abu."

Salmanu yace."Khalid ka kasa gane maganata dama ai ba wai zamu zauna a guri daya bane idan munje zamu dinga buge-buge nufi na duk inda ta fad'i daidai ne."

Ajiyar zuciya ya sauke yace."To shikkenan Salmanu amma dai akwai guziri mai yawa a gurinka ko dan ni ba wasu kudi masu yawa gare ni ba.

Salmanu yace."Babu damuwa insha Allahu zan tambayi kanin mahaifina zai taimaka min sannan Mamana ma zata bani goyon baya kuma zata taimaka mana.

Yace."To shikkenan Allah yasa muje a sa'a." Salmanu ya amsa da ameeen tare da fadin"Khalid ya kamata ka kunna wayarka ka kira gidanku ka shedawa mahaifinka yasa maka albarka ka kuma nemi gafararsa.

Yace."Salmanu wallahi tuntuni nake wannan tunanin amma na rasa ta ina zan fara ina jin kunyar abinda na aikata.

Salmanu yace."Daurewa kawai za kayi ita qaddara ai ba'a guje mata zuwa yanzu dai nasan zuciyoyinsu sunyi sanyi sai ka tausasa harshe gurin neman afuwarsu mussaman ita wacce ka 'batawa."

Shuru yayi yana me sunkuyar da kansa, Salmanu yace.''Bari na shiga gida na dauko mana abinci." Bayan fitar Salmanu daga dakin Khalid ya janyo jakarsa ya bude a nutse ya dauko wayarsa ya kunna kai tsaye number auntyn nasa ya lalubo ya shiga gurin kira.

Lokacin muna hanyar dawowa gida ni da 'kawata Hauwwa kiran ya shigo waya ta gabadaya hankalina ya dauke gurin hirar da muke shi yasa ban duba mai kiran ba na daga tare da sa wayar a kunne na.

A sanyaye naji maganarsa...."Auntyna barka da rana." Gabana ya yanke ya fad'i wayar ta kusa su'bcewa daga hannuna.....shuru nayi masa yace."Ina fatan kin warware ko."? nayi shuru ban tanka masa ba yayi d'an murmushi da fad'in "Kiyi hakuri sharrin shed'an ne ki gafarce ni dan Allah."

Ajiyar zuciya na sauke na kashe wayar na ajiye gabadaya yanayi na ya sanja.

Hauwwa na driving ta kalleni da fad'in "Kawata ina fata dai lafiya." da sauri nace"Lafiya mai kika gani."?

Tana 'kokarin magana ya sake kira kamar kada na dauka sai kawai na yanke shawarar dagawa sabida kada ta zargi wani abu.

Zazzafar ajiyar zuciyarsa naji a cikin kunnena kafin yace."Ya maganar wacan 'katon mutumin mai k'aton tumbi." Yana nufin Alhaji Nura. Nace."Khalid kada ka sake kiran waya ta kaji ko ba kaji ba."?

Jin sanyayyar muryarta yasa shi sake sauke ajiyar zuciya ya lumshe idonsa yana sake gyara kwanciya 'kasa-'kasa yace."Aunty Sa'ida idan kin janye maganar Alhaji Nura zan dawo gida idan kuma baki janye ba to ina mai tabbatar miki da cewa sai dai kuyi hakuri dani domin zanyi nisa kuma ba zan dawo ba.''

Nace."Khalid ka tafi 'karshen duniya kaji ko ba abinda ya dame ni bane aurena da Alhaji Nura yana nan yanda ka sani ranar Juma'a mai zuwa daurin aure."

Ya fesar da wani zazzafan huci! ya mi'ke zaune gumi! na yanko masa yace."Okey ina fata dai kin sheda masa cewa saura na zai samu domin duk na kwashe roman sai da ya samu sud'i."

Da sauri na kashe wayar gabana na dukan uku-uku addua nake a zuciyata akan Allah yasa Hauwwa ba taji komai ba.

Kiran wayar ya sakeyi na dauka da sauri na kasheta gabadaya, Hauwwa tayi dariya da fad'in "Khalid kenan kice dai har yanzu bai hakura ba."

Cikin basarwa nace" Hauwwa rabu da shashasha dan Allah idan ya gaji zai hakura."

Tayi dariya da fad'in "Ni kam ina sha'awar yanda yake nuna miki so hakan yana burgeni wallahi."

Nace."Hauwwa ke kin fiye budurwar zuciya wallahi ina abun yake a gurin Khalid me ya iya a soyayya sam baya burge ni wallahi."

Ta kalleni tana so ta gazgata maganata nace."Kwarai kuwa Hauwwa soyayya sai babban mutum wanda yasan abinda yake amma irin wannan soyayya tasu Khalid ai shirme ce."

Tace."Ni kam a gani na Sa'ida soyayya duk soyayya ce babu babba babu yaro a cikin ta na tabbatar da cewa babu abinda Alhaji Nura zai nunawa Khalid d'an zamani ne sai dai ma ya nuna masa wani abun."

Nace."Hauwwa wai ko son yaron nan kike ne." ? tasa dariya da fad'in "Ai abun so ne yaro ingarma namiji mai 'kwazo ai wallahi ni idan na sameshi to bakina alaikum."

Na dinga kallonta ina mamakin maganarta ita kuma sai kyalkyala dariya take tana 'kara tabbatar min da gaskiyar maganarta...

*30&31*
Cikin wani irin yanayi na damuwa Salmanu ya shiga dakin ya same shi.....Ya ajiye fulas din abincin a gabansa da fadin"Abokina yane na ganka a cikin wani irin yanayi dubi yanda kake zabga gumi sai kace wanda yayi tsere." Ajiyar zuciya ya sauke ido jawur yace."Salmanu dole ne ma na bar garin kano domin mutukar ina zaune a cikinsa hankalina ba zai ta'ba kwanciya ba yanzu nan na kira aunty Sa'ida a waya ta farfad'a min maganar da take so akan wannan mutumin da zata aura Allah Salmanu yanda na tsani Alhaji Nura haka na tsani mutuwa ta idan ina ganinsa zan iya aikata mummunan abu akansa domin sosai nake kishin sa."

Salmanu yace."Dan Allah Khalid ka cire soyayya a cikin ranka kayi abinda yake gabanka wai shin me kake nema ne a gurin aunty Sa'ida bayan ka samu biyan bukatarka duk fa namijin da ya aureta a yanzu sauranka zai samu to meye na damuwa kuma ka cire soyayyarta a ranka ka fuskanci abinda yake gabanka.

"Salmanu bana jin zai ta'ba daina son aunty Sa'ida a cikin jini na yake ko yaya nayi motsi sai na jita a rai na ina yi mata so da kaunar da ban san iya adadinsa ba saboda haka ka daina wannan maganar bana tsammanin zan cire sonta a cikin raina.

Salmanu yace." To ai aure za tayi bai kamata ka cigaba da bibiyarta ba dan Allah tunda dai ka samu abunda kake so a tare da ita to ka rabu da ita ta zauna da mijinta lafiya.

Murmushin takaici yayi yace.''Idan ni ne na auri mace babu budurci wallahi a daran ranar zan saketa to ina fatan hakan ta kasance a kanta Alhaji Nura ya koro ta gida a daran ranar da aka daura musu aure."

A tsorace Salmanu yake kallonsa yace."Khalid wace irin muguwar zuciya gareka wai shin kai baka kaunar zaman lafiya ne kake irin wannan mugwayen kalaman akan 'yar uwarka gaskiya ba sonta kake ba domin duk wanda kake so ba zaka dinga yi masa mummunan fata irin wannan ba."

'Karamin tsaki yaja yace"Salmanu dan Allah maganar nan ta isa haka ni kadai ne nasan abinda yake cikin xuciyata sai kuma wanda ya hallice ni duk da na samu abinda nake so a tare da ita to ba zan daina bibiyar rayuwarta ba."

Salmanu ya dinga girgiza kansa yana mamakin karfin halin abokin nasa.

Yace."Kenan yanzu daka kira wayarta ba hakuri ka bata ba."

Yace."Ganin ina karyar da kaina gurin bata hakuri yasa ta samu damar fad'a min ba'kar magana wannan dalilin ne yasa ka shigo ka tarar dani a burkice Salmanu wai dan Allah dame Alhaji Nura fini da har zata dinga fifitashi a kaina."

Salmanu yace."Watakila kud'insa take so amma bayan haka babu macen da zata dubeka tace bata so Khalid kasan matan yanzu suna so su auri mai kudi ko dan su huta shiyasa kaji nace ka watsar da komai kazo muje mu nemi kudi ko dan mu huce takaici.

"Salmanu bana tsammanin aunty Sa'ida za tayi auran kudi kawai dai nine bata ra'ayi tunda tasha fad'a cewa ita ba zata auri yaro ba sai mai shekaru shin wai wane abu ne take nema da bukata a gurin Alhaji Nura wanda ni bani dashi na zauna nayi tunani sosai na kasa gane mai take hangowa a tattare da mutumin."

Salmanu yace."Son sa take shiyasa take ganin kowane namiji a bayansa yake saboda haka ni dai shawarar da zan baka shine ka tattara lamarinta ka watsa a kwandon shara ka fuskanci a binda yake gabanka.
Murmushin takaici kawai yayi yace."Salmanu duk abinda zan fada maka a yanzu ba zaka gamsu ba saboda kai baka ta'ba soyayya ba sabida haka zanyi kokarin ganin na dauki shawararka amma inaso na sheda maka cewa ba zan ta'ba iya cire son aunty Sa'ida daga zuciyata ba."

Salmanu yace."To Allah yayi maka magani abokina." ya amsa da ameeen yana goge fuskarsa da hankici Salmanu abincin ya zuba musu a plate cikin ikon Allah aka kawo wuta dama zafi ya ishesu sai kawai suka kunna fanka suka fara cin abincin suna tattauna yanda tafiyar tasu zata kasance.

Ina komawa gida na kunna waya ta saboda nasan Alhaji Nura zai iya kirana a cikin ko wane lokaci.....sai da nayi wanka tukkuna na zauna domin cin abinci Gwaggo tace."Sa'ida yau ma sai hakuri domin dai tun safe Rabi tasa kafa ta fita daga gidan nan bayan fitar mijinta.

Nace."Ba ayi abinci ba kenan."? Tace."Sauran taliyar ki na dauka na dafa gatanan a cikin fulas sai dai babu yaji dan nayi ta neman yaro ya siyo min barkono ban samu ba duk suna makaranta.

Nace."Gwaggo taliya da man gyada ina laifin da manja.'' Tace."To nima dai har yanzu ban ci ba dan na tsani taliya ina jiran yara su dawo daga makaranta a siyo min d'an wake a gidansu Mamu."
Chapter 29 · 0% Book details