Sashe 35
Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dakin yayi shuru na minti biyu kafin tace."Sa'ida Alhaji Shamsu mutumin kirki ne kwarai duk hidimar kayan daki ya dauke ya hana Ibrahim siyan komai duk abinda kika gani a dakin ki to Alhaji Shamsu ne ya siya miki saboda haka ki rike shi da kyau kinji ko."
Nace."To Gwaggo insha Allahu.....Ta dauki goro ta gutsira tana taunawa tace."Oh! yau dai zanji muryar Khalid a kunnena wallahi ni kadai nasan halin damuwar da nake ciki akansa, gashi lokaci guda Allah ya amsa addua ta.
Nace."Gwaggo kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana kallona, nace."Khalid nayi masa dubara kancewa ya idan ya dawo gida zan aureshi koda zaiyi miki maganar to ki nuna masa hakane.
Shuru tayi tana kallona kafin tace."Sa'ida me yasa kike yaudareshi gobe fa za'a daura miki aure."
Nace."Gwaggo Khalid fa idan ba haka akayi masa ba ba zai dawo gida ba zai bar zuciyoyinku cikin damuwa shiyasa nayi masa haka.
Shuru tayi na minti biyu kafin tace."To Allah ya sanyaya masa zuciyarsa idan ya dawo ya iske abinda ba shikkenan ba.
Nace."Ameeen ya rabbi sai ki zaunar dashi ki rarrashe shi ki nuna masa cewa samu da rashi duk na Allah ne idan yayi hakuri sai Allah ya bashi wacce ta fini.
Tace."Zanyi iyakacin bakin kokarina Sa'ida Allah ya sanya masa dangana." na amsa da ameeen ina kokarin fita daga dakin.
*Littafin na kudi ne....Kada ki siya ki fita dashi...idan kika ganshi a gruops kada kiyi sharing......Idan kika karanta baki biya ba na biki bashi.....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake... Vip gruop#600 normal gruop#300...account.. 0542382124...Binta umar gtbank....Idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min magana ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*
*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*
*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*
*39&40*
Sai daf da magariba Khalid suka fito daga filin wasa, hannunsa rike da karamin towel yana goge zufar dake jikinsa ya nemi guri ya zauna yana mayar da numfashi, Salmanu ya zauna kusa dashi shima da k'aramin towel din a hannunsa yana goge fuskarsa, Oga Labaran ya karaso gurin fuskarsa yawalce da fara'a yace."Khalid a gaskiya kana burgeni da kwazon ka babu shakka nan gaba kad'an za kayi fice a duniya zata san da zamanka."
Khalid murmushi kawai yayi ya kar'bi goran ruwan faro dake hannunsa ya bude ya sha ya mikawa Salmanu sauran. Oga Labaran ya mika masa wayarsa da fad'in "Kana filin wasa aka kira wayar ka ka duba ka gani.''
Da sauri ya kar'bi wayar yana dubawa ganin sunan auntynsa yasa shi sakin murmushi ya mike da sauri ya bar gurin, Salmanu ya bishi da kallo yana girgiza kansa.
Number ta ya shiga kira cikin zumud'i da bukatar son yaji muryarta.
Lokacin da ya kira wayar tana sallah Gwaggo kuma ta idar da tana jan carbi, da sauri ta dauko wayar tana dawurwura domin bata san inda zata ta'ba ba.
Sai kawai tasa wayar a kunnanta ta dinga zabga sallama tana fad'in " Halo Khalid kana jina ko? Halo Khalid nice Gwaggon ka nake magana." Da karfi take maganar gashi wayar sai 'kara take yi kafin kiran ya katse! ta shiga duba fuskar wayar tana surutai da fad'in "To ko dai babu nethook ne." Saura kad'an dariya ta su'bcewa Sa'ida da sauri ta kori shed'an ta cigaba da sallarta.
Gwaggo ta cigaba da surutai da fad'in "Babu shakka yaron nan ne ya kira waya amma saboda abin nasara bashi da tabbas yayi mana rashin mutunci.
Tana rufe bakinta wani kiran ya sake shigowa, da sauri tasa wayar a kunnanta ba tare da ta ta'ba wani guri ba Fad'i take."Halo Khalid kayi min magana mana nice Gwaggonka."
Ummatu dake gurin ta a zaune ta dinga jin shouting din Gwaggo tana kiran sunan Khalid da saurin gaske ta fito ta tsaya a bakin kofar dakin tana fadin"Gwaggo Khalid din ne."?
Da sauri ta mika mata wayar da fad'in "Eh ina tsammanin shine kinga tun dazu yake kira inata magana babu amsa shine nace ko matsalar nethook ne."
Itama Ummatu sai da ta kusa dariya ta kar'bi wayar tana fad'in "Gwaggo ai baki d'aga wayar ba ba zaiji maganarki ba."
Tace."Ayya to ya ake yi."? Ummatu na kokarin magana Na idar da sallar wanda kuma yayi daidai da sake shigowar wani kiran.
Ta miko min wayar da sauri! Kar'ba nayi na d'aga tare da sawa a kunnena.
A dan sanyaye yace."Aunty barka da dare ina ta kiran waya baki daga ba." nace."Barka dai Khalid ina sallah ne.'' Yace."Okey to ina Gwaggo."? Nace."Gata a zaune ita da Ummatu.'' Kafin yayi magana na mikawa Gwaggo wayar yaji sautin muryarta a kunnansa.
Ajiyar zuciya mai sanyi ya sauke yace."Gwaggo ki gafarce ni akan abinda nai muku." Murya na rawa tace."Khalid mun yafe maka dan Allah ka dawo gida gabad'aya mun galabaita da rashin ka.''
Yace."Gwaggo insha Allahu sati mai zuwa zan zo gida amma hakan ba yana nufin na dawo kenan ba zan koma insha Allahu."
Tace."Khalid yanzu kana wane gari ne."? Yace.''Ina legos kuma na samu aiki Gwaggo kada ku damu akwai alamun nasara a inda nake.
Tace."Khalid daka hakura da Lego's din nan ka dawo gida ka cigaba da harkokin ka dan d'azu da Sa'ida ta kira wayarka wani 'katon mutum ya dauka yake fadin wai kana filin wasa Khalid kasan na tsani buga 'kwallon nan ko."
Yace."Gwaggo idan anan abinci na yake dole kiyi hakuri dan babu irin fafutukar da banyi ba akan na samu aiki abun yaci tura dole tasa na mayar da hankalina gurin buga kwallo.
Tace."To ka dawo gida kayi anan mana." Yace."Gwaggo zan duba maganarki." Tace."To shikkenan ga mahaifiyarka ma tana so tayi magana da kai."
Ummatu hannu na rawa ta kar'bi wayar tasa a kunnenta,
Gaisheta yayi ta amsa a sanyaye tana jin kewarsa tace."Khalid me yasa ka aikata wannan abu." A raunane yace." Ummatu rashin jin magana ne kin gargade ni akan na fita harkar aunty Sa'ida ni kuma na'ki bin umarninki shiyasa Allah ya jarrabe ni nima nayi nadama."
Hawaye ta share tace."Khalid ka dawo gida nima bana son zaman Lego's din nan."
Yace."Ummatu zan dawo gida amma kiyi min alkawarin amince min auran Auntyna."
Magana za tayi Gwaggo ta d'aga mata hannu, da yake wayar handsfree take duk muna jin maganarsa.
Gwaggo a hankali tace "Kice masa kin amince."
Ummatu ta dinga kallonta tana mamakin maganarta wace irin magana ce wannan bayan gobe daurin auranta
Yace."Ummatu kinyi shuru har yanzu baki bani amsa ba." a sanyaye tace."Khalid ka dawo na amince maka.
Hamdala yayi ga Allah cikin tsananin farin ciki yace."Nagode Umma Allah ya tabbatar mana da alkairi." a sanyaye ta amsa da ameeen tana mamakin al'amarin ko me yasa Gwaggon ta fadi haka.
Bayan sunyi sallama sai ta mikawa Sa'ida wayar da fadin"Gwaggo nifa wallahi duk jikina yayi sanyi da wannan maganar taki gobe i yanzu Sa'ida na dakinta ya za'ayi kuma a yaudari yaron nan yanzu idan ya zo ya tarar tayi aure mai zai biyo baya.
Gwaggo tace."Rabi komai mai sauki ne mutukar dai an samu ya dawo gida ai ni a ganina duk abinda zai biyo baya mai sauki ne ni zan zauna dashi na rarrashe shi ya hakura da kaddara matar mutum kabarin sa."
A sanyaye Ummatu tace."To shikkenan Allah ya kawo shi lafiya yasa kuma ya d'auki kaddara kamar yanda itama Sa'idan ta dauka." Gwaggo ta amsa da ameeen ya Allah. Ummatu sallama tayi mana ta nufi gurin ta tana dan jin sassauci a cikin zuciyarta.
Gwaggo bata kwanta bacci ba har sai da Kawu ya shigo ta sheda masa abunda yake faruwa. to shima da yake ya huce fushinsa akan d'an nasa sai yayi ta murna da farin ciki yana adduar Allah ya dawo dashi gidan lafiya.
****
To cikin ikon Allah da hukuncinsa a ka daura auran Sa'ida da Alhaji Nura daurin auran da ya samu hallatar mutane da dama ta 'bangaran Ango da kuma Alhaji Shamsu da Kawu Ibrahim anyi taro an gama lafiya amarya tayi ado sosai tai kyau k'awayenta na gurin aiki sunyi mata kara sun hallaci taron bikin sunyi mata gudumawa sosai mussaman Hauwwa dan itace ta dauki nauyin gyara mata jikinta da nau'in magungunan mata masu kyawun gaske mahaifiyarta ma tayi nata kokarin dan tun kafin bikin take gyara ta ita dai Sa'ida kallonsu kawai take fargabar abunda zai biyo baya kawai ke damunta tabbas tasan idan Alhaji Nura ya fuskanci ita din ba budurwa bace dole ya tuhumeta wannan dalilin yasa har aka gama taron bikin aka kaita dakinta ta kasa sakewa bini bini gabanta zai fad'i....Yanzu ma tana zaune ita kadai a dakinta bayan tafiyar Hauwwa sai tunanin yanda zata kaya take tasan Alhaji Nura yana sonta watakila idan ta fada masa abinda ta tanada ba zai kalubanceta ba.
Ya shigo dakin cikin manyan kaya kamshin turaransa ya game dakin ledojin hannunsa ya ajiye kan teble tun kafin ya zauna a kusa da ita ya cire babbar rigar jikinsa da murmushi a fuskarsa ya kira sunanta had'e dayi mata kirarin da ya saba. "Amarya bakya laifi ko da kin kashe d'an masu gida."
Mayafin dake rufe da fuskarta ta cire tana d'an mirmushi tace."Alhaji kenan." yace."Aa inaso ki kira ni da angon gimbiya Sa'ida."
'yar dariya tayi cikin jin nauyi ta kauda kanta yace."Alhamdulillahi nagode Allah daya nuna min wannan rana Sa'ida auran nan namu anyi kamar ba za'ayi ba sai gashi Alkwarin Allah ya cika."
Tace."Hakane Alhaji dama komai yana da lokacinsa ina rokon Allah ya tabbatar mana da alkairi."
Ya amsa da ameeen ya rabbi yanzu zaki tashi muje falo domin inaso na zauna daku keda 'Yar uwarki."
Nace."To shikkenan." kokarin mikewa nake ya rike hannuna muka mike a tare falon muka fito ya zaunar dani akan kujera da fadin."Bari na kira ta ko." kai kurrum na daga masa na bishi da kallo a lokacin da yake kokarin hawa sama.