← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 90

Sashe 28

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallona ayi tare da fad'in "Ki tashi baki da wata matsala abinda yasa gabanki ya tsatstsage lokacin da mijin naki yazo ka kar'bar hakkinsa kinyi gaddama hakan shi ya janyo miki matsala shiyasa kullum muke fada cewa duk budurwar da mijinta yazo kar'bar hakkinsa a daran farko to yana da kyau ta bashi hadin kai kada tayi wani yunkuri domin ceton kanta dan ko tayi ba zai bari ba daga karshe ma ta janyowa kanta wata matsala amma dai ke gabanki normal yake bai kar'u ba zafi da rad'ad'i kuma zaki daina ji insha Allah yanzu zan rubuta miki magunguna idan kun fita sai ki siya."

Cikin kokarin danne damuwar dake taso min nace."Nagode Dr." safar hannunta ta cire ta watsa a dustbin kafin ta fita daga dakin.

Kati na ta miko min mai dauke da magungunan data rubuta min...na kama hanya zan fita ta dakatar dani. juyawa nayi ina kallonta a tausashe tace."Sa'ida kada kice naiyi miki katsalandan kamata yayi ace tare da mijin naki ku kazo asibiti.

Kaina na sunkuyar ina nazarin maganar da zan fad'a mata....."Wallahi tafiya ce ta kama shi a washe garin ranar daurin auran mu shine dalili."

Kallona naga ta nayi kamar bata yarda da maganata ba, nace."Dr nagode da kulawarki." hannu ta d'aga min da sauri na fita daga ofis din ina mamakin bin
diddigi irin na mutane....

*Littafin na kudi ne....kada ki siya ki fita dashi idan kika ganshi kada kiyi sharing.....'yar idan kika karanta min littafi baki biya ba ina bin ki bashi....Idan kina so ki biya kudin littafin ga yanda abin yake.......Vip gruop#600....normal gruop#300....account.. 0542382124...Binta umar gtbank...idan kati zaki turo #400 ne sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan numbers*
*07084653262*
*08089965176*
*BINTA UMAR ABBALE*

*28&29*
Tun a cikin adaidaita sahu Gwaggo ke tambayata nace ta kwantar da hankalinta babu matsala, ajiyar zuciya ta sauke tana godewa Allah....har kofar gida nace da direban ya kai mu sai cewa tayi ita ya sauke ta a bakin hanya domin tana so ta shiga gidan Uwale su gaisa.

Nace."Gwaggo me zakiji kiyi a gidan Uwale da rana gatse-gatse haka." d'an 'bata fuska tayi tace."Zanje ne mu tattauna al'amuran da suka shafe mu Sa'ida kin san abokin kuka shi ake fad'awa mutuwa."

Idanuwa na suka kawo ruwa nace."Wallahi Gwaggo kika kuskura kika fad'awa Uwale abinda yake faruwa kin kashe kanki domin dai ni nasan Uwale ba zata ta'ba barin maganar nan a cikin ranta ba sai ta fad'awa wani kinga daga haka shikkenan labarin abinda ya faru ya bazu a duniya ko ya sani."

Shuru tayi tana nazari tace."Sa'ida Uwale tana da amana kuma mun jima muna aminta nasan zata ri'ke min amanata.

Nace."Ni dai dan Allah dan Annabi kada kije gidan matar nan wallahi bata da kirki ko kad'an yanda take kawo miki gulmar mutane haka kema zata kai gulmarki gurin wasu.

Tace."To naji dan Allah maganar ta isa haka na fasa zuwa shikkenan ko."

Na kalli direban da fad'in "Shiga damu cikin layin ka ajiye mu a kofar gida.
Da sauri yace." To hajiya.

Koda muka shiga gidan shuru babu motsin kowa kofar gurin Ummatu a rufe da kwado Gwaggo tace."Sarkin yawo kenan wato har ta kulle kofa ta fita."

Nace."Kika sani ko wani uzirin ne ya fita da ita." tace."babu wani uziri ta tafi yawon malamai ne."

Ashe hakane Ummatu bayan fitarsu gwaggo daga gidan itama sai ta shirya a gurguje ta tafi gurin malamin da suke zuwa gurinsa yana musu duba tana kuka duk ta sheda masa abinda yake faruwa.

Malam Sammani ya jima yana zane-zane kafin ya dago kansa ya kalleta da fadin"Rabi yaron nan naki abinda ya aikata gaskiya ne ba sharri akayi masa ba kamar yanda kike zargi! kuma na duba na gani cewa lallai akwai ibtila'in da zai sameshi a cikin 'yan kwanakin nan amma kuma akwai wani tauraro da yake haska shi watakila nan gaba akwai wata daukaka da zai samu sannan maganar surukar ki sai dai kiyi hakuri domin 'kwan'kwaman! da suke kanta sunfi karfin ki itama sunfi 'karfin ta iyayen aljanu ne a jikinta dole kiyi hakuri da duk abinda za tayi miki sai dai akwai wani taimako da zanyi miki akanta zan gwada daure mata baki mu gani idan zai yuwu."

Ummatu ta sharce gumin goshinta hankali a tashe tace."Malam Sammani dan Allah ka taimaka min akan yaron nan hankalina ya tashi da jin abinda kace yayi nisa da gari bayan haka kuma ga ibtila'in da zai hadu dashi ka taimaka min kayi aikin da zai sanya ya dawo gida babu shiri.

Malam Sammani yayi zane-zane a karo na biyu ya duba yaga abinda Allah ya haska masa tabbas duk abinda ya gani a dubansa zai faru amma bari kawai ya sanja mata magana domun ya kar'bi kud'inta ya biya bukatarsa.

"Shikkenan Rabi za'ayi miki kokari akan bukatarki amma kema zaki bayar da sadaka mai auki.''

Tace." To kamar nawa ne abin sadakar."? yace."Dubu bakwai zaki bayar ya isa." jim tayi tana nazari kafin tace."Malam a yanzu dai wallahi bani da dubu bakwai bani da dalilinta amma ina da kayan kudi a gida insha Allahu gobe zanzo maka da kudin sai ka fara gudanar da aikin."

Yace."To babu damuwa insha Allahu zan ajiye aikin kowa na durfafi naki sabida ni kaina al'amarin ya firgita ni amma babu komai za dage da addua muyi masa kiranye ya dawo gida babu shiri itama surukar taki aiki mai kyau zanyi akanta.

Ummatu ta dinga zabga masa godiya kafin tayi masa sallama ta tafi gida .

*Shashashar Uwa kawai a maimakon ta gyara kuskuranta ta sake tafka wani*

Kafin ta shiga gida sai da ta tsaya gidan Lantana Dillaliyi tayi mata bayani kancewa idan tana son siyan katifar gado tazo ta gani.

Lantana ta kalleta da mamaki a tare da ita tace."Ke kuwa Rabi me yayi miki zafi zaki siyar da katifar gadon ki shin rashin ci ko rashin sha ne ya janyo haka."?

Ummatu a sanyaye tace."Ko d'aya Lantana wata 'yar matsala ce dani wallahi sabida haka nazo nayi miki tallah idan kina so kawai muje ki gani bana san doguwar magana."

Lantana ta yafa mahaifinta da fad'in "To shikkenan muje naga katifar." suka fito daga gidan a tare.

Muna zaune nida Gwaggo a tsakar gida muna hira gwaggo na gyara wake za tayi mana alala Ummatu da Lantana suka shigo.....Lantana cikin mutunci ta tsaya suka gaisa da Gwaggo ita kuwa Ummatu ko kallonmu ba tayi ba ta bude gurinta ta shiga Lantana tabi bayanta.

Gwaggo da bakinta baya shuru tace."Sa'ida mai Ummatu zata siyar ta kawo dillaliya gidan nan."?

Nace."Gwaggo dan Allah ki daina shiga abinda babu ruwan ki kiyi shuru da bakin ki shi yafi miki alkairi."

Shuru tayi bata sake cewa komai ba sai dai sa'i da lokaci takan daga kai ta kalli kofar Ummatun nasan jira take su fito.

"To shikkenan Lantana sai ki aiko yaro da akori kura ya daukar miki na siyar miki akan dubu ashirin da biyar din." Ummatu ce ke wannan maganar a lokacin da suke fitowa daga gurin nata.

Lantana tace."To shikkenan yanzu yanzu ina komawa gida zan turo a dauka tare da kudin naki." Ummatu tace."To ina saurare."

Lantana ta kalli Gwaggo da fad'in "Gwaggo Allah ya bamu alkairi ni na tafi." Gwaggo tace."To ki gai da gida." Lantana na fita Ummatu da sauri ta juya zata bar gurin.

"Rabi." Gwaggo ta dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Fuska a murtuke ta juyo tana amsawa Gwaggo tace."Me zaki siyar ne."? Da sauri na kalleta ina jin masifar takaicin abinda take ina ruwanta Ummatu ko kanta da kanta zata siyar ido ne nata.

"Gwaggo ba abinda ya shafeki bane'' Ummatu ta mayar mata da amsa daidai da tambayarta. Gwaggo taji ciwo sosai tace." Duk abinda zaki siyar kije kiyi ta siyarwa ni dai nasan ba za'a zagi Ibrahim ba ace ya gaza a gidansa wannan ai cin mutunci ne rana gatse-gatse kije ki dauko dillaliya ta shigo mana gida me aka gaza dayi miki a gidan."?

Itama cikin rashin tausasa harshe tace." Ai dama ni bance Ibrahim ya gaza a gidansa ba tunda daidai gwargwado yana kawo abinci amma kuma suttura sai shekara shekara sannan ni na dauko Lantana ne domin tazo ta siyi katifar gadona saboda inada bukatar kudi."
Tana gama maganarta ta kad'a kanta ta shige gurinta.

Gwaggo ta bude bakinta cike da mamaki tana kallona.

Nace"Ai dama baki in yasan abinda zai fada bai san abinda za'a mayar masa ba tun farko sai da nace kiyi shuru kika k'i ai gashinan kin janyowa kanki cin mutunci.'"

Tace."Sa'ida ni ba wannan ne ya dame ni ba saboda cin mutuncin Rabi kuma wane iri ne ban sani ba ko ba kiji abinda tace ba wai zata siyar da katifar gadonta to a 'ina Ibrahim zai dinga kwanciya."?

Nace."Gwaggo babu ruwanki katifa dai ta Ummatu ce baki isa ki hana ta siyarwa ba saboda haka kiyi shuru da bakinki shi yafi miki alkairi Kawu kuma insha Allahu ba zai rasa gurin kwanciya ba ni nayi alkawarin siya masa katifa yasa a dakinsa shikkenan magana ta mutu."

Girgiza kanta tayi da fad'in "Lallai Rabi tayi nisa ko da yake ai nasan idan ta kar'bi kudin katifar gurin malamai zata kai asararriya kawai."

Shuru nayi ban tanka mata ba saboda bana so maganar tayi tsayi da dai naji taki tayi shuru sai na mike na shige daki na kwanta ina jira ta gama mana alalan nasha magani bacci mai nauyi ne ya dauke ni.

Gwaggo kuwa har akazo ka dauki katifar ba ta daina surutai ba tamkar ma wacce ake ingizawa Lantana da Ummatu sun sha habaici amma sai akayi sa'a cikinsu babu wacce ta tanka mata Lantana ta tafi da katifa ita kuma Ummatu ta shige gurinta da kudinta a hannu

****
*BAYAN SATI DAYA*
Khalid ya dan samu nutsuwa a gidansu Salmanu sai dai baya sakewa sosai a unguwar gudun kada yaga idon sani kullum yana dakin Salmanu a kwance yana shawarwari da zuciyarsa.

Salmanu ya shigo dakin da fad'in "Khalid ka tashi ga shawara nazo mana da ita."

Zaune ya miqe yana kallonsa da fadin" Nima kwanciyar nan da nayi shawarwari nake da zuciyata.
Chapter 28 · 0% Book details