← Book details Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 90

Sashe 23

Ga Irinta Nan Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gwaggo ta shiga girgiza kanta tana share hawaye tace."Sa'ida nima na gazgata na kuma yarda da cewa Khalid ba son Allah da annabi yake miki ba domin idan son gaskiya yake miki to ba zai ta'ba cutar dake ba wallahi tallahi ban dauka irin wannan matakin zai dauka ba jiya na zaunar dashi nayi masa nasiha kamar ya d'auki maganata ashe ni ya mayar mahaukaciya ya shirya tozarta ni a idon duniya to ai shikkenan tunda bukatarsa ta biya zai shigo gidan ya same ni wallahi sai yaga 'bacin raina kuma dan dai bana so maganar ta fita waje ne amma da sai nace ki fad'awa mijin mahaifiyarki a bi miki Hakkin ki."

Murmushin takaici nayi ina kokarin mikewa nace."Gwaggo duk wani hukunci da za'a dauka akan Khalid ba zai ta'ba goge wannan mummunan tabon da yayi min ba Gwaggo yanzu idan naje gidan mijina mai zance masa idan ya kusance ni yaji ni a bud'e."

Kuka tasa tace."Sa'ida ki daina maganar auran wani mutum kuma ai dole A mayarwa da Alhaji Nura kud'insa kiyi hakuri ki auri Khalid asirin mu ya rufu idan kin auri Alhaji Nura ya same ki babu budurci ai mummunan zargi ne zai shiga tsakaninku dama kuma jama'ar gari na munana zaton su akan ki."

Murmushin takaici nayi nace."Gwaggo ke yanzu a tunanin ki idan har na auri Khalid auran zaiyi albarka."?

Shuru tayi tana kallona....nace."Khalid fa ba sona yake tsakani da Allah ba sha'awata yake yanzu ya samu biyan bukatarsa to me kuma yake nema? babu wani sauran buri a tare dashi dan ko na aure shi 'bacin rai za mu shiga saboda haka ki daina wannan maganar Khalid ya zalince ni kuma insha Allah sai ubangiji ya saka min."

Hannu tasa ta goge fuskarta a sanyaye tace." yanzu yana ina Khalid din."? Shuru nai mata na fara kokarin sauka daga gadon...ta rirri'ke kafad'una tana taimaka min na mi'ke tsaye daurin zanina ta gyara min kamar 'yar kaciya haka muka fita tsakar gida.....Ta zaunar dani a kujera 'yar tsuguno kamar wata maijego mai haihuwar fari da sauri ta koma dakin ta dauko fulas cike da ruwan zafi tana share hawaye ta surka ruwan a buta ta kai min bandaki da fad'in "Shiga kiyi tsarki kafin na d'ora miki wani ruwan ki gasa jikin ki Allah zai saka miki abinda akayi miki.

Daurewa nayi na mike tazo wai zata taimaka min nace." Ki barshi gwaggo.'' gefe ta matsa ni kuma na dafa bango na shiga bandakin ina rintse idona......koda na tsuguna domin wanke najasar dake jikina kuka ne ya 'kwace min yi nake ina tsarkake jikina tare da yin tasbihi a cikin zuciyata.

Daga bakin kofar bandakin ta tsaya tana miko min zanin atamfa da fad'in "Kar'bi ki daura wannan sai na shigo miki da ruwan zafi ki shiga ki gasa jikinki a ciki."

Tausayi ta bani ganin yanda duk ta damu da ni banta'ba tsammanin zata yarda da lamarin ba.

Tana can uwar dakin na fito daga bandakin ganin maidaidaicin baho da ruwa a ciki yasa kawai na tattare zani na na shiga ciki....sai bayan dana shiga cikin ruwan kuma na shiga tunanin wanda zai shigo...

Gwaggo tana share hawaye ta cire farin zanin gadonta daya 'baci ta dinga kiran sunan Allah a cikin zuciyarta tana addua akan Allah ya kauda idanun 'yan gaza gani a cikin al'amarin.......zanin gadon ta fito dashi ta ajiye bakin kofar shiga gurin Ummatu.

Na bita da kallo ina mamakin abinda take nufi da yin hakan.....Tace."Sa'ida dole na ajiye sheda iyayen yaron nan su dawo su ga abinda d'ansu ya aikata ba zan shaqi takaici ni kad'ai ba."

Girgixa kaina nayi nace."Gwaggo ki dauke zanin gadon nan dan Allah bana so kowa yasan maganar nan." Da sauri tace."Sa'ida ko kowa bai sani ba to ya zama lallai Rabi da Ibrahim su sani daga haka sai a rufe magana a gida Khalid kuwa ya nemi gurin kwanciya dan ba zai 'kara shigowa gidan nan ba.''

Shuru nayi tare da yin 'kasa da kaina ta juya ta shige dakin tana surutai had'e dayin tur da abinda Khalid din ya aikata.....naji dadin ruwan zafin sosai hakan yasa na karfafa jikina na zubar da ruwan bahon kana na janyo ruwa a rijiya na daura alwala na nufin dakin..

Tsaf ta gyara d'akin ta ta kunna turaran tsinke sai kamshi yake.....dadduma na shimfid'a nasa hijabi cikin karfin hali da yanayi na jin jiri da hajijiya na tayar da sallah.....Itama alwalar ta fita ta d'auro ta dawo dakin.

Koda na idar da sallar kwanciya nayi kan daddumar na rufe idona....har yanzu gabana radad'in zafi yake min inaji kamar an tsaga da reza!! jin hawaye na nema ya kufce min yasa da sauri na shiga nanata kalmar innalillahi wa'ina ilahi raji'una.

A take kuwa na samu sassauci a cikin zuciyata na dinga jin imani da tsoron Allah na ratsa ni zuciyata ta shiga fad'a min cewa wannan al'amari daya faru dake ki daukeshi a matsayin qaddarar da kike tafiya da ita haki'ka duk wani abu da zai same ki a duniya mai dad'i ko mara dad'i a rubuce yake a lauhil mahafuz Allah shine yake zartar da iko akan kowane bawan sa Ki roki Allah ya tsayar miki nan kuma kisa a zuciyarki cewa baki sa'bi Allah da gangan ba sai dai karfi da aka gwada miki....Tsakanin ki da Alhaji Nura kuma fatan alkairi ne."

Jin irin shawarwarin da zuciya take bani yasa naji wani irin kwari a jikina na mike zaune a ina kallonta da carbi a hannunta tayi zugum! tana kallon guri guda nace''Ba zaki koma gidan bikin bane."?

Girgixa min kai tayi tace."Ya za'ayi na kuma fita na barki ya dawo ya 'karasa ki yaro mara imani yasa miki k'arfi ya fatataka miki budurci na tsorata da jinin da nagani Sa'ida."

Kaina na sunkuyar k'asa ina tunanin artabun da muka sha ni dashi.... ko da wane ido zai kalli mutane? ko da yake ai mara kunya ne zai iya fittikewa akan 'karya domin ya kare kansa.

Haka muka kasance a zaune cikin jajantawa juna dan har sai da naso na fita dauriya domin sa'i da lokaci ina hankalce da ita tana sa hannu ta goge hawaye a fuskarta.

Sai yamma Ummatu ta shigo gidan.....bakin kofar dakin ta tsaya da fad'in "Gwaggo lafiya baki koma gidan bikin ba? jama'a sai cigiyarki suke."

Girgixa kanta tayi tace."Rabi tashin hankalin dana tarar a gidan nan ne ya hana ni komawa gidan bikin ina fata kinje kinga dakin amarya."?

Ummatu tace."Aikuwa ni na wakilce ki dan dani aka kai Suwaiba dakinta ba kiga gidanta ba yayi kyau kuma sosai Jummai tayi kokari dan tayi mata kayan daki masu kyau."

"Ba shakka." abinda tace kenan tayi shuru da bakinta...Ummatu tasha jinin jikinta ganin yanayin rashin walwalar dake tare damu sai kawai ta bar gurin tana ta'be bakinta.

Tazo shiga gurinta taga zanin gado a kud'indine kuma kamar an goge jini dashi....cike da mamaki ta dauka tana dubawa wannan zanin gadon ai na Gwaggo ne. sai kawai ta nufi dakin Gwaggon da zanin gadon a hannunta

"Gwaggo wannan ba zanin gwadon da kika siya kwanaki bane."? tafada tana nuna mata.

" Shine Rabi ki warwareshi sosai ki duba kiga meye a jiki."

Ummatu tace."Haba Gwaggo ai ba sai na warware ba gashinan ina ganin jini kaca kaca a jikinsa."

Murya na rawa tace."Jinin budurcin Sa'ida ne Khalid ya dawo gidan bayan fitar mu ya haike mata a cewarsa tunda shi bai samu nasarar auranta ba to sai da taje gidan mijinta a fanko."
Ummatu ta shiga watsa mana wani irin mugun kallo kafin tace............!
*SADAUKARWA NE GA IYAYE NA BIYU*

*FATIMA MUSA (MOMMY NIJAR)*
*TARE DA*
*USAINA ABDUL-MALIK ISA (KAITA)*
*(HAJIYA BABBAH)*

*_Ha'kika ina Alfahari daku da irin kaunar da kuke min.🥰🤝🏻💜_*

*22&23*
"Gwaggo wannan wace irin magana ce kikeyi? Ina khalid yake a gidan da har zai aikata wannan mummunan akin! Gwaggo shuru-shuru fa ba tsoro bane gudun magana ne ya za'ayi yarinya tayi fasiqancin ta sannan a laqabawa wanda baya nan Khalid tun karfe bakwai na safe ya fita daga gidan nan ballanatana ayi masa mummunan sharri irin wannan."

Gwaggo ta nuna kirjinta da fad'in "Rabi ni kike wa rashin kunya har kina fad'in shuru shuru ba tsoro bane to me kike nufi? kin san dai ba zan qi Khalid naso Sa'ida ba tunda duk daya suke a gurina abinda kuma yasa na yarda da al'amarin shine jiya da daddare na jima tare dashi ina tausar zuciyarsa akan auran Sa'ida da Alhaji Nura na dinga kawo masa misalai ina fahimtar dashi cewa shi aure rabo ne Allah ya kaddara cewar Sa'ida ba matar auransa bace dan haka sai ya hakura ya nemi wata.....Idan kikaji irin munanan kalaman da ya dinga yi sai kin riqe baki wannan dalilin yasa na yarda da abinda ya aikata."

A fusace! tace."Gwaggo idan duk jikina kunne ne ba zan yarda da wannan k'anzon kuregen ba, a ina Sa'ida taga wani budurci da har jininsa zai 'bata zanin gado kawai dama dai ta dawo gidan ne da niyyar ta d'ora masa sharri saboda ta tsaneshi."!

Cikin takaici da 'bacin rai nace."Ummatu idan nayi wa Khalid k'azafin zina meye ribata a duniya."

"Ke! saurara kada ki kuskura ki sake kiran yaro na da wannan sunan Khalid ba mazinaci bane."! a fusace tayi maganar tana kumfar baki.

Gwaggo ta zabaro! itama a fusace! tace." To menene shi idan ba mazinacin ba Rabi nace ki fad'a min menene shi Khalid ya cancanta a kirasa da wannan suna tunda har ya iya haikewa 'yar uwarsa."

Ummatu ta fashe da kuka da fad'in "Jama'a wannan wace irin masifa ce Gwaggo ashe akwai ranar da zaki goyi da bayan 'karya akan gaskiya kin fi kowa sanin halin Khalid ba zai aikata wannan mummunan aikin ba."

Gwaggo ta girgiza kanta cikin takaici da bakin ciki tace." 'Dan yau ne fa Rabi ba'a shedar mutum sanin abinda yake zuciya sai Allah amma ko shakka ba nayi Khalid shine yayi wa 'yar uwarsa fyad'e a tunaninsa idan hakan ta faru sai a janye maganar auran Alhaji Nura ayi dashi."
Chapter 23 · 0% Book details